Sashe 4
Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunana Aisha amman a gidanmu ana cemin (Humairah) nice ƴata biyu a wurin mahaifina malam yusuf wanda muke kira da (baba) da kuma mahaifiyata khadija da muke kira (anty). Yaya imran shine babban ɗa a wurin mahaifinmu da mahaifiyar mu kuma muna da tazarar shekaru sosai a tsakaninmu domin ya bani kusan shekaru goma sha biyar kafin Allah ya bawa anty wani cikin ta haifeni dagani se nafisa se kuma auta anisa. Muna zaune a unguwar ɗorayi amman a salin su baba ƴan ƙauyen tofa ne mahaifan su, su biyu suka haifa daga babana yusuf se ƙanin shi sulaiman wanda muke ce masa baffa karami mahaifiyata anty itama ƴar nan dawakin tofar ce domin auren zumunci ma akai mata ita da babana wanda ita ta kasance ɗiyar ƙanin babansu uwa ɗaya uba ɗaya. Anan tofa baba ya fara zama da anty cikin gidansu na gado wanda mahaifin su malam nuhu ya gina yakuma zauna cikinshi shida matarsa Aisha indo har Allah yayi musu rasuwa se mahaifina ya cigaba da zama agidan shida kaninshi. Anan anty ta haifi ya imran dayake itace babba cikin gidansu yasa ƙannenta ke ce mata anty wanda jin haka ya imran ya taso da faɗa mata hakan. Baba yana zuwa nan cikin kano sarin kayan gwari ( kayan miya ) yana kaiwa can tofa ya saidar ranar sati ya kuma dawowa ya siya anan Allah ya saka mai nasibi har baya kaiwa satin, yakan zo ma a kwanaki biyu ya siya yaje ya saidar. Shikuma kaninshi baffa yana aikin sana'ar gini ne ma'ana leburanci. Yawan zirga-zirgar datai yawane yasa(ayiya) mahaifiyar anty dayake mahaifin anty shima ya rasu mahaifiyarta ce kaɗai ta rage se kannenta guda huɗu da suke aure suma anan tofar, ta kira baba ta nemi shawarar shi akan yakamata ko haya ce ya kama anan cikin garin kanon ya tafi da iyalinshi sabida ya ragema kansa zaryar baba bai musawa ayiyah ba anan yazo cikin gari ya sami abokinshi. Malam muhammadu sarkin gida wanda suke aminci sosai dashi sarkin gida ɗan garin katstsina ne domin sana'ar gini ce shima ta kawoshi kano dalilin dayasa ake kiran shi da sarkin gida kenan sabida yana harkar ginin gidane yana kuma yin hanyar samawa mutane haya. To sun haɗu baba ne lokacin da yaje siyan kayan miya anan ƴan kaba shima kuma baban yaje sari daga gaisuwa kuma abun kamar wasa seya zame musu aminta. Shwarar sarkin gida ya nema akan yana son ya sama mai hayar ɗaki mai sauki domin ya dawo da iyalinshi kusa shima kuma yana son ya sami ɗan wajen daze na sayar da kayan miyan shi anan base ya dinga tafiya kauye ba. Cikin raha sarkin gida yace masa. Aikuwa agidan dani ke haya muna da sauran ɗaki ɗaya in kana so dubu goma sha biyar ne seka kama anan ɗorayi unguwar bello. Baba baiyi musu ba ya amince wa sarkin gida haka suka rankaya zuwa ɗorayi, cikin mutunci sarkin gida ya shigar da baba gidan dayake hayar ya nunawa baba ɗakin. Batare da ɓata lokaci ba baba ya amince har ya bada kuɗin ɗakin sedai ya nemi sarkin gida akan dan Allah yana son ya kuma samawa ƙaninshi shagon daze na kwana. Murmushi sarkin gida yayi tare da cewa baba ai babu wani abu akwai shago a kofar gidan dama babu kowa se kanin nashi yana kwana anan ɗin. Sosai baba yayma sarkin gida godiya kana ya tafi tofa suka cigaba da shirinsu na komowa kano. Sosai ƴan uwa da abokan arziki sukaita jajantawa anty na rabuwar su sabida an saba sabo baɗan kaɗan ba haka su anty suka rankayo zuwa cikin garin kano anan cikin unguwar ɗorayi. Abinda ze baka mamaki shine yadda matar sarkin gida wadda zata ɗan girmewa anty da tazara mai yawa ta tarɓi anty kamar kanwarta haka tai musu girki mai rai da lafiya kana ta taya anty kintsa kayanta. Sosai anty taji daɗin karamcin Inna matar malam muhammadu wanda taji ana ce masa baba shima kamar yadda ake cewa malam yusuf mijinta zaman anty da inna zamane na son barka babu wata matsala datake faruwa kamar zamane na ƴan uwan taka. Baba inya fita wajan kayan miyarsa da safe shima kuma baba sarkin gida haka yake fita harkar ginin shi da safe basa dawowa gida se dare sabida baba sarkin gida ma da sulaiman kanin baba suke tafiya aikin. Lokacin yaya imran yana da shekaru tara a duniya baba sarkin gida da kansa yakai yaya imran makarantar primary yana masa wasa. "Kaganka sa'an Umarina nima na kusa na ɗauko shi na haɗeku waje ɗaya ku xama abokai" Murmushi baba yayi tare da cewa. "Lah daman malam kana da yaro aini ban saniba wallahi ca nake Allah bai kawo ba danaga gidan babu kowa daga kai se inna" Dariya baba sarkin gida yayi kana yace. "Ai ina da yarona sunan shi umari amman cika daji nake ce masa sabida jarumine na baroshi agida can ƙauye wajan mahaifina, yana koyar farauta sabida jarumtar shi, wannan dalilin nema yasa ake ce masa cika daji domin inya shiga dawa seya ɗauko ɓauna ko dai wani abun na namun daji". Murmushi baba yayi kana ya dubi malam muhammadu. "Amman malam niko ina ganin meze hana ka ɗaukoshi daga ƙauyen kazo nan ka gina masa rayuwa da ingantaccen ilimin zamani dana arabi ina ganin hakan zefi kodan yadda zamanin nan namu ya lalace komai sekana da ilimi ake yi dakai". Cewar babanmu. "Eh! nima haka nakeso to amman fitina ta tsofi kasan mahaifana sun tsufa kuma ni kaɗai Allah ya basu se kanwata ramatu ita kuma tuni ta rasu tabar yarinyarta guda ɗaya tana nan ƴar shekaru biyu wannan dalilin yasa suka dauki son duniya suka ɗora wa umari shida nuratu, kuma mahaifina mafaraucine domin shiyake da sarautar sarkin farauta na garinmu anan katstsina to baya son ya rasu baida magaji hakan yasa ya rike Umar wajansa yake fita dashi farauta ilimin arabic bani da hofi akan umari sabida yayi sauka tuni na bokon nedai babu ni yanzu babban tashin hankalina nasan tsoho baze yarda nazo da umari kano ba tunda nima da ƙyar ya barni nazo ciranin nan sabida nida ramatu kaɗai suka haifa ramatu kuma ta rasu se ƴarta nuratu, nikuma umar kaɗai na haifa kaga bamu da yawa sosai shiyasa suka ɗauki son duniya suka ɗorawa umari da nuratu amman yaya kake ganin zan bullowa lamarin?". Cewar baba sarkin gida yana kallon babanmu. Nisawa malam yusufa yayi tare da kamo hannun aminin nashi. "Ina ganin ranar sati zamu tafi tare dakai can katstsinan naiwa tsoho bayani sosai yadda ze gamsu amman kafin nan muyi addu'a" Sosai baba sarkin gida ya gamsu da maganar babanmu hakan yasa suka ida cin abincin su na dare kana sukai ƴar hirarsu sannan sukai sallama suka wuce ɗakunan su. Haka zaman ya cigaba har Allah ya nuna mana ranar sati. Ranar asabar suka tafi can katstsina anan wata ƙaramar hukuma ta bakori cikin wani ɗan karamin ƙauye mai yalwar arziki, sosai tsoho mahaifin baba sarkin gida kamar yadda ake ce mai suka tarbi ɗan nasu shida abokin nashi. Haka nan iyatu matar tsoho mahaifiyar sarkin gida tai ta nan nan dasu nan da nan ta kawo musu damin fura nasu na fulanin ƙauyen tare da ɗumaman tuwo. Seda sukaci suka hantse sannan sukai sallah zaman hutu sukai har zuwa faɗuwar rana. Tsoho ya kuma dawowa ɗakin da aka sauke su nan suka ɗan taɓa hira da ɗan nasa. "Tsoho nikam ina umari?" Cewar baba sarkin gida yafaɗi hakan cikin son ganin ɗan nashi. Murmushi tsoho yay tare da washe bakinshi mai cike da goro. "Ai CIKA DAJI, yana can dauji ya tafi kaso ɓauna da barewa sabida gobe muke saka ran za,a bikin auren ɗan gidan dagacin dawa shine muke son kowa ya nuna jarumtar shi anan". Murmushi baba sarkin gida yay kana yace. "A,a kai masha Allah ubangiji ya taimaka, daman tsoho nazone akan kaɗan bani aron umari ina son ze tayani wani aikine acan kano amman ze dawo". Yafaɗawa tsoho hakanne sabida in yace masa tafiya ce ta din din bafa ze bari ba. Haɗe rai tsoho yay. "Kodai kazo ka tafimin dashi kamar yadda kai nesa dani kabar sana'armu ta gado ka koma can bariki kake zama baka da ƴan uwa duba nan ko ina dangin kane amman ka ware kai ɗaya". Babanmu ne ya mike ya fuskanci tsoho cike da lafazi mai taushi yake tausarshi har Allah yasa ya yarje musu akan zasu tafi da umari amman baxe jima ba. Sosai su baba sukai murna tare dayi masa godiya. Umari bai dawo ba se goshin almuru. Sosai babanmu yay mamakin girman umari inka dube shi bazaka ce ɗan shekaru goma sha biyu bane sabida ya girmewa imran da shekaru biyu namijine ingarma mai ƙirar ƙarfafan maza dogone sosai mai girman jiki farin bafulatani, tass mai mugun kyau na asali. Cikin rashin sabo yake gaisar da su baba sabida shi bai wani saba da mahaifansa ba sabida tun daga yaye iyatu ta ɗaukeshi. Haka nan baba yayta jansa da labari shiko baya wani sakin fuska daga um se um haka yake basu amsa. Washe gari su baba suka juyo hanyar kano da umari wanda sam shi tafiyar batai mai daɗi ba sedai yana marmarin yaga innarshi gefe ɗaya kuma yana kewar nuratu ɗiyar kanwar babanshi wadda suka kusan tashi tare sun shaku sosai ba kaɗan ba. Sun shigo kano lafiya a hanyar ƙauyukan kano sukai mugun gamo da babbar motar kaya ta haye saman tasu motar. Inda suka sami mugun hatsari umar ya karye a cinyarshi shi kuma babanmu idanunshi ɗaya ya tsiyaye shiko baba sarkin gida bai ko shura ba Allah ya amshi ran abinshi. Innalillahi wa'inna ilaihirra ju'un. Haka aka ɗebu zuwa babban asibitin murtala. Kafin a soma basu tai makon gaggawa baba sarkin gida kuma aka kaisa matuware. Seda sukai kwanaki uku sannan aka sami bakin babanmu ya bada lambar wayar sulaiman baffa karami aka kirashi sosai iyalan su suka shiga tashin hankali. Musamman inna datai katari da gawar mijinta da kuma kallon karayar tillon ɗanta a take anan ta faɗi wajan bata motsi. Da taimakon likitoci aka samu inna ta farfaɗo wanda garin gwaji aka gano tana ɗauke da cikin wata biyu. Haka aka sallamo babanmu