← Book details Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 42

Sashe 13

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*15&16*

Sosai ya jima yana miƙa godiyar shi ga Allah maɗaukakin sarki, daya mallaka masa sanyin idaniyar shi Aishatul humairah, macen dayake so yake ƙauna yakeda burin ya kasance da ita muddin rai.
Har aka soma kiran assalatu yana saman darduma seda aka soma tayar da sallah a masallacin cikin unguwar tasu sannan ya miƙe gaban akwatin kayan shi ya nufa ya ɗauki turaren shi na element ya fesa a sassan jikinshi kana ya fita da sauri yana mai zira slipers ɗinshi a ƙafafun shi.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya buɗe ƙofar gidansu ya fita zuwa masallaci.
Sahun jam'i'n sallah yabi har aka idar anan suka haÉ—u da imran dasu baba suka gaisa a mutunce kasancewar duk anan masallacin sukeyin sallah.
Hanyar gida ya kamo cikin sauri sabida yadda ake azababban sanyi tura kofar gidan yayi kana ya mayar ya rufe sannan ya kama hanyar ɗakin innah wadda yake da yaƙinin tana saman abin sallah a zaune tana lazumi.
Aikuwa hakance ta kasance sallama É—auke abakinshi ya shiga É—akin.
Zaune ya tarar da inna a saman darduma carbi ahannunta daga cikin uwar É—akin kwa Æ´an bikine da sukazo daga katsina suketa faman haÉ—e kayansu waje É—aya.
Agabanta ya zube gwiwarshi tare da sunkuyar da kanshi a ƙasa yanajin yadda innah ke kai kukanta wajan ALLAH maɗaukakin sarki akan ya shiga lamuran ɗan nata dama sauran musulmi baki ɗaya.
Sosai yakejin daÉ—in tarin addu'oin nata akan shi harta kammala a tare suka shafa.
Sannan ya soma gaisar da ita a kunyace kamar koda yaushe, itama a nata ɓarin amsa mai take a kunyace tare da alkunya irinta ɗan fari, tana tambayar shi ya kwanan humairah?
Sosa ƙeyarshi yayi batare daya ce mata komi ba ya gyara tsugunnon ya koma ya zauna a gabanta tare da tanƙwashe ƙafafunshi.
"Innah yanzu me kike ganin za,a shiryawa baƙin nan na karin kumallo? dana ce a sayo bread se a dafa tea, sannan a siyo ƙosai su haɗa dashi anjima zan saka salim ya samo musu tasin da zata kaisu tasha".
Yakai maganar a nutse kamar yadda maganar shi take a koda yaushe babu baragada.
Kallonshi tayi cike da ɗunbin tausayin shi acikin ranta, tana yabon ƙwazon ɗan nata haka nan tana jin tausayin shi matuƙa gaya sabida wahal halun da sukai mai yawa, bare yanzu da daɗin wasu suka ƙaru amman tunawa da Allah yasa taji sanyi a cikin zuciyarta.
"Yaro"!
TafaÉ—a a hankali sabida sunan datake gaya mai kenan.
"Na'am innah"!
Ya faÉ—a shima a nutse.
"Kaga tun jiya na saka mairamu takai markaɗan gero na kwano biyu, sannan ga wake can shima na siyo za,a markaɗo se ayi ƙosai, amman yadda kagani tunda kayi niyyar alkairi ga ƴan uwanka bazan hanaka ba, asiyo kayan shayin inyaso geron semuyi amfani dashi agida".
Takai maganar a nutse.
"Tom shikenan innah".
YafaÉ—a babu musu kamar yadda tun asali baya mata musu a dukkan umarninta.
Tashi daga gabanta yayi ya nufi É—akin shi har lokacin humairah tana bacci kamar babu gobe akwatin kayan shi ya buÉ—e tare da zaro kuÉ—i acikin wanda abokanshi suka haÉ—a mai na jiya na gudun mawa.
WaÉ—anda sun kai kimanin dubu huÉ—u a waÉ—anda ya É—ebo É—in sannan ya fita waje, shagon dake bakin layinsu ya nufa ya haÉ—o kayan shayi tare da manya manya biredi wanda iya na gida kawai ya siyo domin shi abokan shi sun haÉ—a mai nashi jiya.
Lokacin daya shigo gidan ya tarar da inna a tsakar gida tare da kanwarta suna ƙoƙarin haɗa wutar sanwa sedai yaga kamar suna magana ne akan shanyar zanin gadon da suka gani a shanye a tsakar gidan wanda shi sam yama manta dashi.
A kunya ce, ya ƙaraso gabansu yana gaisar da anty maimuna.
Cikin barkwan ci take amsa mai tana tsokanar shi.
"Kai, ka aje wannan zanin gadon anan waya gaya maka yanzu ana buÉ—ar kaine?"
Kunya kamar ta kashe shi haka ya sunkuyar da kanshi yasan za,a rina sabida yadda yasan anty maimuna da muguwar zolaya.
Itako inna kasa tai da kanta tana sakin murmushin farin ciki.
Ledar hannun shi ya aje gabansu da sauri ya nufi gaban zanin gadon ya tattare shi ya nufi É—akin dashi, kicin É—insu ya nufa ya É—ora ruwan tea, sannan ya dawo É—aki ya tube rigar jikinshi yay saura dagashi se gajeran wando da singlet, sabida yadda Allah yayi shi da mugun jin zafi, yasa duk uban sanyin da ake tsulawa bai hanashi zagewa ba.
Zama yayi a bakin gadon tare da ɗaukar wayarshi ƙarama yana duba saƙonni.
Har lokacin daya kimanci shayin ya tafasa aje wayar tashi yayi tare da fita ya sauke sannan ya wanke tea flaks É—in dayake sabo cikin kwalinsa ya zubo tean a ciki sannan ya kashe rishow É—in yayo É—aki da flaks É—in shayin.
Komawa kicin ɗin ya kumayi, still ruwan wanka ya ɗora musu a ƙaton tukunya a tsaye yake wajan har ya tafasa sannan ya juyo rabi a bahon wanka rabi kuma a flaks ɗin ruwan zafi wanda yafi na shayi girma.
Wanka ya shiga bayan ya kammala ya fito.
Mai ya shafa sama-sama tare da mitsika turaren arabian udt, shirya kanshi yayi cikin ɗanyar farar shadda sabuwa dall se maiƙo take, lokacin wajan bakwai na safiya sauri yay ya daura agogon farar sliver a hannun shi kana ya ɗauko hula da bakin sau ciki.
Agaban gadon ya tsaya tare da zama bayan ya tura takalman gefe guda.
A dai dai kunnenta ya kai bakin shi yanajin feeling ɗinta na fusgarshi baiyi gigin matsata sosai ba sabida gudun kada ya ɓata lamarin shi domun sauri yake ya fita ya gaida baƙi suyi bankwana sabida yana da text yau a school ƙarfe tara.
"Ammatana! Ammanata!!"
Yake faÉ—in sunan ta a hankali kamar maiyin raÉ—a.
Mitsika idanuna nai a hankali ina mai yatsine face É—ina.
Sabida baccin dayake kaina.
Kafin na waresu a kansa yawani ranƙwafo saman fuskata kamar zemin rumfa.
Da baya naja jikina na matsa nesa dashi sannan nace.
"Miye ne wai baka san sunana ba se wannan munafukin sunan wanda nakeji yana tarwatsamin zuciyata da tsanarka".
NafaÉ—a kaina tsaye.
Amai makon naga yaji haushi kamar kullum innai masa rashin kunya.
Senaga yay murmushi.
Ya miƙe tsaye tare da zube hannayen shi a aljihun shi.
"Allah yay miki albarka da wannan kyauta da kikai min a daran jiya ubangiji ya bani ikon riƙe ki amana Allah ya haɗa kammu,nasan bakida matsala ajikin ki tunda har harshen ki ya iya sarrafuwa wajan yimin rashin kunya, ga ruwa can a fulas ki ɗauka kiyi wanka ga tea nan da kaza kici naso na kasance dake a yau domin na baki kulawa sedai kash inada uziri a makaranta, wanda bazan shigo gida da wuri ba, kiyi kokarin gyara kanki sabida gudun jin zafi irin na jiya domin yau ma bazan ɗaga miki ƙafa ba".
Yafaɗa yana mai ƙoƙarin kama hanyar fita daga ɗakin.
"Inka dawo lafiya kenan? ina roƙon Allah akan yasa kai hatsarin mota kai mummunan nakasar da bazata barka kai wani abu ajikina ba mugu azzalumi kawai".
Amai makon naga ya dawo da baya ya É—auki mataki akaina senaga yay ficewar sa batare daya nuna ma yaji mai nace ba.
Komawa nai na daki bangon É—akin ina daga kwancen sabida takaici sau tari wannan halin shariyar nashi yana bani haushi ai abu yazama kamar kurma tun a gida inna guma masa takaici baya tankani kuma ko a fuska baze nunan ba, miskilin tsiya kenan.
Kuka nasaka mai cin rai kafin na tashi cikin ƙarfin hali na sauka daga gadon alwala nayo nazo na tayar da sallah ina kuka.
Har na idar kana Na koma gado na ƙara kwanciya sabida yadda ƙasana kemin zafi kamar an tsaga da reza.

Zuciyar shi babu abinda take se tafarfasa jinsa yake kamar ya mutu matarka ta sunna wadda ka amarce da ita a daran jiya itake maka wannan fata? seda ya tsaya ya dai daita nutsuwar shi sannan ya nufi É—akin inna.
Zaune suke suna karin kumallon safiya..........

*Littafina na kuÉ—ine naira É—ari 300 ta wannan asusun bankin 0078174806 starling bank, shedar biya ta nan 08142105218, Auren bare naira #500 ta accnt dake sama*
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*17&18*
Chapter 13 · 0% Book details