← Book details Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 42

Sashe 22

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

farin ciki wajan sakina sosai take shirin bikin a wannan lokacin xata nuna true colour ɗinta domin batajin xatai mai bautar ƴaƴan maƙiyarta daman dasu ta kama ƙafa wajansa domin iya bincikenta ya nuna bazata samu aurensa ba harse ta kama ƙafa da ƴaƴansa wanda ba kowane yay mata wannan yaƙin ba face masoyinta saurayinta NAZIR wanda ta lasa mai ZUMA A BAKI na zata bashi kanta matukar ya farauto mata soyayyar UMAR ( hmmmmmm ) Wannan ƙwaɗayin yasa nazir ya shiga ya fita domin ganin ya mallaka mata umar sabida shibaya sonta da aure zumarta kaɗai yake da muradi wadda tai mai alkawarin bashi ita duk da kasancewar ta ba mazinaciya ba. Da wannan damar suka haɗa plan dashi har takai ta sami yadda tai ta haɗu da humaira takuma haɗata da nazir a matsayin yayanta haka nan koda wasa sakina bata yarda takai humaira gidansu ba kullum tace mata zata zo setace ai gidan surukaine ashe ita da gadar zaren datake haɗa mata( wannan baya bukatar dogon shari domin abinda yake faruwa ne a wajan alumma cin amana yaudara da zamba cikin aminci, yakamata muna zaƙulosu cikin litattafanmu domin mufaɗakar da al'ummah ). Haka nan naxir shiya kaita abuja har ya san yadda yay ya haɗata da titin da umar kebi don xuwa gidansa bayan yasha wuya kafin kammala binciken komi. Haka lokacin bikin yazo ranar da akai ɗaurin aure da daddare ana gobe xasu bar kano nazir yazo kofar gidansu koda ya kirata a waya setace mai. "Nazir idan abunsha ya ƙare shin mai za'ai da kwalba? "Ban gane ba?" Yace. Tace "Ina nufin naci biredi na yada leda daman na ɗaukane domin kaimin aiki to kagaman karkai tunanin zan iya bawa wani namiji jikina inba Ƙatona ba domin shine da alhakin cin gun! ina fatan ka fahimta dan haka seka kwashe ƙazaman ƙafafunka kabarmin kofar gidanmu domin daga kai har Humairah kidahuma nagama da babinku sabida na sami muradina dukkanku ZUMA A BAKI na lasa muku amman ai nihin ZAƘIN yana wajan Umar". Ƙitt!!! Ta katse wayar tama cire sim card ɗin baki ɗaya. Dariya nazir yay irinta gogaggun ƴan barikin cikin sabon gari kana yace. "ZUMA A BAKI"! yay dariyar ƙeta. Sannan ya shiga motar yabar ƙofar gidan nasu. Haka sakina ta wanxu cikin nishaɗin cikar burinta washe gari suka wuce abuja da yayarta daman su biyune daga ita se hadiza yarta se babarsu, dan haka hadixan ita ta rakata abuja bayan ta kwana ɗaya ta juyo, shima umar a ranar da hadiza ta komo kano shikuma a ranar ya nufi abujan cikin ɗaukin so ta tare sosai ta nuna masa kulawa haka nan koda dare yay tai matukar nuna masa soyayya sedai bai kai first night ɗinsa da humaira ba sedai kuma ya sameta a cikakkar mace. Zamansu suke son barka sabida daman shi ɗaya yazo abujan su islam suna kano wajan inna se an komo hutu ze ɗaukosu dan haka suka sake shida sakina basa aikin komi gida se romancing sabida yana matukar son romance. Hankalinsa ya kwanta tuni yama mance da wata damuwar humaira acikin rayuwarsa. ******** Nikuwa daman gaba ɗaya na koma wata iri bani da wani tunani a yanzu sena ƴaƴana su anty duk sun fita daga sabgata nasara mema zanyi cikin haka na kammala idda ta dan haka umma ta roki matar kaninta akan ta saman aiki a makarantar datake a matsayin shugaba wadda ta kasance private da taimakon umma na soma fita ina koyar da ƴan aji ɗaya da kwalina na secondry inda ake biyana dubu bakwai. Alokacin nutsuwa ta kuma shigata cikin wannan lokacin naji labarin ya umar yay aure kuma yama zo har ya tafi bai zo gidanmu ba ƴaƴana ma dana gansu ƙin yarda sukai dani haka naci kukana babu mai lallashina wayata na dauka na kira layin sakina sedai akashe na nazir ma haka jefa wayar nai a matsai na saka kuka ina mai cewa inama nasan gidansu sakina danaje ta bani shawara. Tsayin kwanaki gashi na tafi shekara an saka bikin ya imran da maryam kanwar ya umar haka nan an saka bikin nafisa mai bina, a wannan lokacin na rame na fige su islam na gidan inna hutu amman kunyar inna ya hana naje na gansu domin ni a tunanina ya gaya mata yadda muka zauna. Seda ana ya gobe zasu tafi nasai omo da sabulai anisa ta rakani gidan a saka makon takuramin da anty tai akan naje na gansu a karo na biyu. Tunda na doso layin jikina ke rawa sanye yake da bakar t.shirt se bakin wando yay wani haske ya karo kyau matasan layin zaune gefensa suna masa fadanci yana raba musu kudi gidan inna an gyareshi har wani gate aka saka domin rabona da gidan tun daya saken anisa ce ta gaishe sa nikuwa wucewa nai na shiga gidan inna maryam tana zaune tanawa islam wanka shiga nai muka gaisa da inna sannan na fito wajan islam sabida kukanta ya dauki hankalina kusan a tare muka isa gareta nidashi ajiyar zuciya na sauke ina mai kallon maryam. "Maryam meke damun Aisha?" Nafaɗa ina kallon yadda ƴar keta kuka! "Wallahi anty humairah wanka ne bata so" Kokarin kai hannuna nake jikinta yay saurin ɗauke ƴarsa ya makawa maryam harara tabar wajan. A kokarina na kuma kamo islam saukar mari naji a kuncina. "Kada ki kuma saka wannan jakin hannun naki ajikin ƴata banza marar zuciya uban me ya kawoki gidanmu wallahi nakuma ganin wannan ramammiyar fuskar taki sena la'antaki". Yafaɗa yana mai tofan miyau a saman fuskata yaja yarsa suka bar wajan. A tsakar wajan na zube nama kasa kuka dan takaicin tozarcin dayamin a wannan kadamin bana hango so se dunbin ƙi gareni. Haka anisa tazo tajani mukai gida dan tsabar bala'i har zazzaɓi nai ranar tundaga wannan lokacin ban kuma saka ƴaƴana a idanuna ba haka zalika inyazo baya zuwa inda muke sedai aikensa haka zalika matarsa ma bamu taɓa ganinta ba kwanaki ma tai ɓari amman batazo nan ba kuma a gidan inna tai jinyar, haka lamarin nawa yay ta tafiya har zuwa wannan lokacin dayau ya kawosu gidanmu wanda shine zuwansa na biyu tin bayan rabuwarmu. Wannan shine tarihinmu dafatan makaranta labarina zasu fahimta. *DAWOWA LABARI* *GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*
Chapter 22 · 0% Book details