Sashe 14
Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sallama yay cikin nutsuwa tare da shiga cikin falon ya zauna a saman tabarmar dake shinfiÉ—e a gefe É—aya, Sosai suka gaisa shida Æ´an uwansu na katsina har wasu na tsokanar shi da cewa.
"Ango kasha ƙamshi".
Mayar da hankalin shi yayi wajan iyatu kakarshi yana jin yadda take faman janshi da wasa, cike da sakin jikin sabon dayay da ita yake mayar mata da martanin tsokanar tata.
"Hamma umaru barka da safiya yaya amarya?".
Cewar nuratu wadda take sanye da shuÉ—iyar atamfa wadda akaiwa É—inkin riga da skirt ta yafa mayafi a kafaÉ—arta gabanta É—auke da trollyn kayanta tana mai danna wayar hannunta.
Tsira mata idanun shi yay batare dayace mata komi ba, seda ya ɗauki ƴan daƙiƙu kafin ya furta mata.
"Lafiya ƙalau Nur! amman mai yasa bakiyi break fast ba?"
Sunkuyar da kanta tai ƙasa tanajin daɗin sunan daya gaya mata, kafin tace.
"Ayyah hammana naci abincin nan kam, amai zanyi kafin mukai can bana break da safiya haka".
Murmushi yayi mata yana mai cewa.
"A,a kaga baturiya seki É—auki bread É—in ki saka a ledar in kinji yunwa kyaci a mota".
Dariya kurum tai mai batare data ce mai komi ba.
Miƙewa yayi yana mai zaro kuɗi a aljihunsa ya miƙawa anty maimuna.
"To anty ga wannan ba yawa kwa rage na mota ni zan wuce makaranta ne amman akwai, abokina salim ze kawo mai tasin daze kaiku tasha".
Amai makon ta amsa seta É—aga jakarta ta É—auko damin kuÉ—i guda biyu kowanne ze kai dubu hamsin a daure.
"Ga wannan namu ne na dangi mahaifiyarka ni ina wakiltar ƴan uwana da basu zoba amman ga saƙonsu nan da nawa ba yawa, kasan anata aikin gona a ƙauye, gakuma na dangin mahaifinka da iyatu ta bani ɗazu na baka harda nasu harɗo duka suna aikin bazara ne, yasa basu zoba, sabida haka mu bazamu amshi ko kwabonka ba yadda kake hidimar mahaifiyarka da kanwarka ma ya ishemu Allah ya tsare mana kai umaru".
Tausayin ahalin nasane ya ɗarsar masa a basu da shiɗin basu kasa taimakon shiba, wani maƙwallaton abu mai nauyi ya haɗiye kafin yace.
"Nagode sosai amman suna fama da kansu ai basa bada kuÉ—i mai yawa haka ba".
"Kai kaci ubaka dan ubaka inda muna dashi bamu zamuyi maka auren ba, in kana dashi ai barema zakama bare naka, maye mahaifinka bai mana ba, shi kaɗai muka haifa amman ya share mana hawayen dubu, kai yanzu wani irin saƙone baka aika mana ta tasha? shi kansa arɗon bada irin kuɗin da kake bamu bane ya zuba amfani gonar bana ba?"
Cewar iyatu wadda take faman taunar goro tana zuba masa magana.
Murmushi ya sakar mata.
"Afuwan gimbiyar mata uwar gida sarautan mata na".
Gaba É—aya dariya Æ´an É—akin suka saka masa kowa yana faÉ—in albarkacin cikin bakinshi.
"Yaro bakai karin kumallo ba zaka fita? ina humairan ita kuma?"
Inna ta faÉ—i hakan tana mai kallon shi.
"Inna innaje school zanyi ita kuma akwai shayi a É—akin bacci take in ta tashi zata karya".
YafaÉ—i hakan cike da soyayyar mahaifiyarshi aranshi inba uwa ba waze maka haka?.
"Badai wata matsala ko? naga fuskarka shigowarka kamar a damuwa?".
Sosa kanshi yayi.
"Inna zancen text É—innan ce ta sakani damuwa sabida kinsan mun kusan soma exam's wadda kuma daga ita zamu shiga lavel 4 daga nan kuma se service wannan shine damuwata".
Yakai maganar wadda sam ba haka take ba kawai danya ɓoye laifin da humaira tai masane a fitowarsa.
"Kaita addu' insha Allahu, ubangiji ze dubeka Allah yay maka albarka".
"Amin"!
YafaÉ—a yana maijin sanyi aranshi, haka sukai sallama dasu iyatu yabar É—akin kai tsaye gidan su humaira yaje a kunyace suka gaisa da baba again sannan ya wuce É—akin anty.
Zaune take a saman tabarma tana haÉ—a kayan dake gabanta su anty uwani sunata shirin tafiya suma.
Gaisarsu yayi a kunyace kafin ya zaro kuÉ—i na daga cikin wanda Æ´an uwanshi suka haÉ—a mai.
"Anty ga wannan ki basu na mota ni zan wuce school".
Fafur suma ƙin amsa sukai, sema albishir ɗin kayan gara da anty tai masa wanda baba ya haɗa komi yanzu za,a miƙa kafin danginsu na katsina su wuce.
"Haba anty duk irin hidimar da baba yayi mana sekuma yay wata gara dan Allah a bari ina da kudin kuma inada kayan abinci".
Cikin nutsuwa anty ta dubeshi.
"Kai ma kasan baya yi maka hakan domin humaira bane yayi maka ne sabida yana tausayin ka nidai fatana dan Allah ka riƙemin ita da amana kasan har yau akwai kuruciya atare da ita".
Sosai kalamin anty suka bigi zuciyarshi tabbas yanawa humaira so mai tsafta sedai halin dattako irin na mahaifanta yasa yaji ya kara mata ninki fiye dana da.
"Insha Allahu anty bani da bakin gode muku face nai muku addu'ar gamawa lafiya kun É—auko Æ´a kun bani batare da kun duba niÉ—in waye a halin yanzu ba, kun biyamin sadakin aurenta kunzo kun haÉ—ani da kayan abinci, inama abba na yana darai da idanun shi sun nuna mai yadda amininshi ke lura da lamuran É—anshi".
YafaÉ—a idanunshi na sauya launi zuwa jajur!
Sosai anty take bashi baki tare dasu anty uwani harya mike ya fita daga É—akin.
"Niko anty ina yabon umar É—in nan gaskiya humaira tai dacen miji sedai muce Allah ya basu zaman lafiya".
Cewar anty zulfa kanwar anty.
"Hakane zulfa'u Umar yarone mai ƙwazo nagari baida matsala, sedai ƴar takuce take mai tsiya dan Allah in kunje can ɗin ku kara mata faɗa sosai"
Nan suka hau tattaunawa akan halin humaira har lokacin da akace su fito domin miƙa kayan gara.
Shikuma yana fita adai daita sahu ya samu direct BUK ya nufa yana duba agogon dake hannunshi, lokacin daya isa malamin nasu yazo dan haka bai tsaya bata lokaci ba ya wuce aji tare da mayar da hankali ga text É—in dake gabanshi domin baida matsalar karatu sabida yana da naci wajan duba manyan littattafai.
Haka ya wuni a makaranta baya da wani time cikakke sabida zafafan text ɗin da aketa faman yi masu wanda ko abinci baiciba sedai sallah kaɗai ke fitar dashi, daman babu wanda yasan zancen aurenshi bare ai masa Allah sanya alkairi domin imran ba dp ɗinsu guda ba, sukuma su salim daman abokai ne na unguwa da aka taso tun ƙuruciya tare bare su faɗa, duk da shiya soma buɗe musu ƙofar aure acikin abokan nashi.
Lokacin dasu anty uwani suka isa gidan inna har su iyatu sun fito da kayansu gaban motar da salim ya samo musu, ganin karamar mota da kayan abinci ta tsaya a kofar gidan yasa suka dakata seda inna ta hango su zulfa kannan anty sannan taÉ—an saki ranta.
Suka karaso suka gaisa a mutunce.
"Ai daman tafiyar wuri zamuyi yanzu haka kayanmu muke sakawa a mota in mun fita mu biya muyiwa su malam yusufa godiyar karamci".
Cewar iyatu wadda anty uwani ke gaisarwa.
"To madallah muma kayan abinci baban nasu ya bada a kawo musu ne yanzu".
Cewar anty uwani.
Sosai iyatu tahau godiya kafin su rankaya zuwa cikin gidan kayan abince madai daita baba ya haÉ—o hardasu daddawa kubewa da sauransu, godiya mai yawa su anty maimuna kannen inna sukai kana suka dauko kudin tukwici zasu basu.
Fafur sukaki amsa suna cewa.
"Ai anzama É—aya wallahi su bazasu amsa ba".
Rankayawa sukai É—akin humaira gaba É—ayansu har su iyatu.
Maganganun sune ya farkar dani a kunyace na tashi ina cije bakina ina gaisar dasu.
Babu abinda iyatu take face tsokanata.
Haka na sinne kaina a jikin anty zulfa ina murmushin dole.
"Amaryarmu ina kwana?"
Naji zazzaƙar muryar wata farar budurwa a cikin kunnena tana min murmushi.
Kadaran kada han na dubeta.
"Ina gajiya"
NafaÉ—a ina mai gyara kaina jikin anty zulfa ganin bata sami fuskaba yasa taja ta fita, ganin haka yasa su anty zulfa suka sakani na sako hijab É—ina muka fita waje har suka gama shigewa motocinsu muna tsaye har motar ta tashi wadda naji suna maganar sesun je sunwa babana godiya kafin su wuce.
Haka naji muryar iyatu a cikin motar tana cewa.
"Ke nuratu tashi ki koma gaban mota nan mun matsu".
Wannan ta É—azun nagani ta fito ta shiga gaba tana É—agawa salim hannu da murmushi har motar tabarmu
Wajan ya rage dagani se inna da maryam dasu anty muke awajan kafin muma mu wuce cikin gida......
ÆŠakin inna naje muka gaisa tana tambayata yana kwana?
A kunyace nake amsa mata kafin na tashi nai É—akina sabida su anty uwani suna ciki, abakin kofa na haÉ—u da maryam itama gaisawa mukai.
Na kama labule na zan shiga É—aki naji dirin muryarsu anisa nafisa da kuma sadiya, haka muka rankaya cikin É—akin dasu.............
*Littafina na kuÉ—ine naira É—ari 300 ta wannan asusun bankin 0078174806 starling bank seki turo sheda tanan 08142105218, AUREN BARE kuma naira 500 maiso ya nemi numbern sama*
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*19 & 20*