← Book details Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 42

Sashe 19

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ya umar kenan wanda ake cemai (aslam) babu wanda yazo daga kano sedai nuratu datazo daga cikin garin,katsina, wadda taita ɗaukar yaran tana musu hotuna, sosai tai musu sayayya ta bam mamaki ni daman ban shiga sabgarta ba, haka lamarin namu ya kasance raino ya zaman biyu konace ya zame mai domun shike wa islam komi shikuma aslam iyatu tai mai haka nan rainon su ya koma kanshi shida iyatu wadda ta dau son duniya ta ɗorawa aslam nikuwa daman basa gabana sema tsanar yaran data ubansu danakeji araina. Shekararmu biyu a katsina domin seda ya kammala komi nasa harma muka ɗora watanni sannan muka dawo kano lokacin islam nada shekaru biyu ba watanni domin tana tafiya kuma tana magana wadda da daddy ta budi baki aslam yana tsaiwa sosai yaran suka shiga ran kowa domin tsabar kyansu da wayonsu hakan yasa wasu ma kece masu ƴan biyu. Lokacin ya umar bayada sukunin zama sabida baban nuratu yana yawan kiransa a waya yana turashi wajan wani ɗan siyasa a nan cikin kano wanda ya kasance aminin sa akan ya sama masa aikin gwamnati domin takardunsa sunyi kyau baida matsala. Wajan wata ɗaya yana faman cuku-cuku domin har abuja yaje yay sati kafin a kirasu domin duba suna cikin amincin Allah sunan *Umar muhammad sarkin gida ya fito a jerin sunayen da federal government ta ɗauka a ma'aikata na aikin ƴan sanda sedai shi yana ɓangaren sashin bincikene na fararen kaya( DSS POLICE ) wanda zasuna bincikar masu manyan laifuka ( criminal case )* Sosai nai masa murna daya dawo yake gayan. "Daman ya umar abinda ka karanta kenan shiyasa senai maka laifi kaimin shuru, kokuma innai abu nace ma banyi ba seka karyatani" Dariya yay min. "Aisha wannan aikin na jima da burin yinshi domin bawa ƙasata taimako sedai na ɓoye nemansa ne sabida aikine mai haɗari, naso mun sami aiki tare da imran to Allah baiba domin ba sashin karatunmu guda ba, kuma ni kinga baban nuratune ya sama min to abin alfarma kaima ka samu da ƙyar yasa ban zaƙe da yawa ba". Awannan karon shuru nai mai sabida banson mu shirya. Sosai su baba dasu inna sukai mai addu'a akan aikin nashi kafin ranar litinin ta farkon wata ya tafi training wanda seda yay sati biyu sannan suka dawo yazo yay sati biyu gida kana posting letter nasu ya fita inda ya sami aiki a garin Abuja. Lokacin da muketa shirin tafiya abuja lokacin sakina tazomin da daddare mukai hirarmu daga nan tace min zata tafi. Tashi nai na rakata amai makon naga ta tafi senaga tanata jana da hira akan tana missing ɗina zanyi nisa da ita, hasken motane ya haskemu a kofar gidan inna kafin naga nazir ya fito daga motar cikin sarsarfa ya karaso gareni yana kuka. Kokarin riko hannuna yake na doke ina ja da baya. "Nazir ni matar aure ce akull ɗinka"na faɗa da karfin gaske amman nazir yaki daina kokarin kamoni harseda ya rikoni yana kokarin rungumeni Ya umar ya doso gidan. Cak numfashina ya dauke na waiga banga nazir ba kuma banga sakina ba se lafiyayyun marukan danaji a kuncina suna sauka. Gabas yamma kudu arewa babu su se ya umar dake faman huci akaina idanunshi na zubar ƙwalla. Jana yay mukai cikin gida ya watsani a ɗaki, ya rufo kofar. "Daman abinda kike nufi kenan dani? shiyasa kika ƙi ƴaƴanki kika ƙini sabida wancan ɗan iskan da aurena akanki kike kula wani ƙato? yafaɗa yana shakoni, wallahi humaira nai nadamar haɗa zuri'a dake kuma kije na sakeki saki ɗaya!!! Hakkina dana yarana baze taɓa barinki zaman lafiyaba kije xaki fahimci wake sonki tsakani da Allah humaira kincu ceni!!" Ya faɗa yana zubewa a wurin yana kuka Bana fahimtar komi haka na ɗauki mayafi na nai gidanmu. Gurfane nake gaban baba ina kuka anty tana zagina sosai mahaifana suka nuna bani da gaskiya washe gari koda baba ya kirashi ce mai yay baya nan domin ashe tunda asubahi ya hade kayansa dana yaransa sukai tasha yana kuka haka ya isa garin abuja.
Chapter 19 · 0% Book details