← Book details Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 25

Sashe 6

Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abangaran gidan Abdulmalik kuwa Ruhaima tana kitchen tanai wa inna abinci taji Abdulmalik yana ta kwalla mata kira da sauri ta ajiye ludayin hannun ta tafito wata uwar harara inna ta watsa mata duban sa tayi tace

"Sannu da zuwa malik "

" yauwa, ya kika bar inna a nan baki kaita daki ba kuma ina abincin ta "

" wlh malik sai da nayi nayi da inna ta shigo ciki taki ko abincin taki ci "

Salati inna tasaka ta hau matse ido sannan ta dora da

" yan nan kiji tsoran Allah yaushe kika ce in shigo dakin ku kai amma yarinyar nan kin iya sharri "

Abdulmalik kam rasa ma me ze cewa inna yayi can ya dubeta yace

" kiyi hakuri inna inshaallah zaa gyara yanzu taso ki dawo ciki "

"Allah ya sawake ba inda zanje wlh ai yanzu abinda zakai min ka burge ni shine kasaki wannan matar kawai shine ka cika dan halak"

Cikin sauri da kidima Ruhaima da Abdulmalik suka dago suka kalli inna

Areefa bata bar Hydar ya tafi ba sai bayan magariba tunda ga wannan ranar kullum sai ta fita sun hadu da Hydar ahaka ta hadu da wani Alhajin birni nan suka shiga soyayya kamar ba matar aure ba

Hafeez yana fita wajen aikin sa ya wuce nan ya shiga office din ogan nasu takarda ya dakko yabashi yana dubawa yaga taransfer akai masa zuwa kano be bata lokaci ba ya shirya ya nufi kano sanda ya isa gida Areefa bata nan mamaki ya shiga yi nan ya shiga neman layin ta akashe

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [9:28 Pm, 2017]

*®💦💦💦NASEEBA GAWO 💦💦💦*

*💦N I G*💦

*ZAMAN AURE* 🤦
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA 💐

*Alhmdulillahil Ala kulli Halin Allahumma ya mukallabul kulubi sabbit kalbi ala dinika*👏🏻👏🏻

*9*

~~~cikin dakewa da basarwa kamal ya dubi lubna yace

"ke, yaushe kika zo kin wani zubawa mutane ido "

Sunkuyar da kanta tayi can kuma ta dago ta dube shi tace

" jiya muka zo da mama, ina kwana yaya "

" lpy kin tashi lpy "

" lpy kalau, Aunty sakna antashi lpy "

" lpy kalau lubna sannu da aiki na barki da aiki ko, kiyi hakuri wlh yau natashi da zazzabi ne ".

" Ayya sannu aunty".

Tabe baki kamal yayi yaja kujera ya zauna, sakna ma zama tayi ta dau cup ta fara zuba masa ruwan tea plate din soyayyan kawai ya bude take sakna tafara yunkurin amai tashi tayi ta nufi toilet da sauri yana zaune ko motsawa beyi ba kallon lubna yayi yace

"oya lubna jeki taimaka mata "

Tashi tayi ta bi bayan ta shi kuwa mai da hankali yayi wajen cin abincin nan sa, a haka suka fito sai sannan ya mike ya rungume sakna a jikin sa ya shiga yi mata sannu dauke kanta tayi can ya dubi lubna yace

" lubna kawo mata tea tasha "

A hankali sakna ta dago ta dube shi tace

" Honey bee, bazan iya sha ba pls ka barni "

" Aa my dear kisha kadan sai muje asibiti ko "?

hannu yasa ya karbi cup din da lubna ta zubo ruwan tea da kansa ya shiga bata tana sha, kadan tasha ta dauke kanta, duban lubna ya kuma yi yace

" jeki dakko mata mayafinta "

" To yaya "

Kai tsaye daki ta nufa ta dakko mata mayafinta ta kawo da kansa ya karba ya yafa mata suka bar lubna a gida suka nufi asibiti suna isa suka shiga ganin likita cikin kankanin lokaci ya dubata take ya gano shigar ciki na sati shida da fararsa ya dubi kamal yace

"congratulation abokina matarka na da ciki na tsawan sati shida "

A razane kamal ya dago ya dubi likitan hade da watsawa sakna wani irin kallo jikin ta ne yai sanyi ta tsura masa ido

Labiba kuwa duban Hajiyar jameel tayi tai mata sannu da zuwa da sakin fuska taamsa ta sami guri ta zauna cikin kwantar da murya ta gaishe ta

"Hajiya ina kwana ya hanya "

" lpy kalau yar albarka kuna nan lpy de ko "

" lpy kalau Hajiya, bari akawo miki abinci "

" Aa yi zaman ki ina Dan marayan zaki, yana nan de ko "

" ba ya nan Hajiya ya fita tun dazu "

Hajiya najin haka ta mike dan tafiya tare da duban labiba yace

" to shikenan badamuwa zan neme shi a waya, sai anjima "

Tafiya tayi ita kuwa labiba dariya tayi ta dawo ta zauna jameel ne ya fito cikin shirin fita office duban labiba yayi
yace

" Everlasting sai naji kamar muryar Hajiya ko "?

A hankali ta dago ta dubeshi tace

Su kuwa su Ruhaima hakuri suka shiga bawa inna tai musu banza Abdulmalik ne ya dubi innar yace

" Dan Allah inna kiyi hakuri wlh ina son ta "

" Wani kallo ta yi masa hade da tabe baki tace

"shikenan Abdulmalik na barka da matar ka amma wlh bazaka kuma gani na a gidan ka dan bana son matarka juya kawai wacce bata haihuwa saboda mugun ta "

Tana gama fada tayi gaba da sauri Abdulmalik yabi bayan ta afusace ta juyo tace

" wlh mutukar baka dena bina ba zan tara maka jamaa "

Shiru yayi can kuma yanisa yace

Abangaran Hafeez kuwa zaman jiran areefa yai tayi bata dawo ba sai laasar lokacin har ya gaji da jiran ta ransa yagama baci tana shigowa gidan tayi tozali da motar sa cikinn ta ne ya murda daakewa tayi ta shiga parlorn yana kwance daga shi sai vest da gajeran wando wani banzan kallo yai mata yace

"Daga gidan uban wa kike kuma da izinin wa kika fita "

Banza tayi masa can ya hassala ya mike cikin fushi da bacin rai ya nufi kanta tsugunawa tayi ta shiga bashi hakuri dan tasan zuciyar Hafeez yanzu ya bige ta abanza da sauri ta ce

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [6:10Am,2017]

*®💦💦NASEEBA GAWO💦💦💦*

*💦N I G*💦

*ZAMAN AURE*
💦 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA 💐

*subahanallahi wabihamdihi subahanallahil azeem Rabbi yasir wala taasir Allahumma yasir alaina*👏🏻

*10*

~~~Hannu kamal ya mikawa likitan suka gaisa sannan ya dubi sakna yace ta taso su tafi jiki a sabule ta bi bayan sa a mata ta same shi ransa a mutukar bace bata kula shi ba Shima be ce mata kala ba ahaka Suka isa gida kowa da abinda yake sakawa ya na ajiye ta a gida ta fita daga motar ya figeta a guje ya bar gidan kai tsaye gurin aiki ya wuce anan ya hadu da abokin sa *shaba* yana ganin abokin nasa ya fiskanci yana da damuwa cikin barkwanci ya dube shi yace

*"Bobson* kamar kana tare da damuwa ko "

Tsaki yaja sannan ya dubi abokin nasa yace

" shaba akwai matsala fa wai yarinyar nan ciki gareta, haba da Allah nawa nake da zanfara haihuwa yanzu ina tsaka da jin dadin rayuwa ta kai imposible "

Dariya shaba ya ringa yiwa kamal har sai da yagaji da kansa sannan ya dubi abokin nasa yace

" abokina akwai shawara matso kaji "

Matsawa kamal yayi ya rada masa magana a kunne dariya yasaka suka tafa

Sakna kuwa tunda ta koma gida take kwance dan ma lubna ta nan ita ta taimaka mata da aikin gida ana yin magariba kamal ya dawo gida da wasu ledoji a hannun sa a a parlor ya tarar da lubna tana kallo nan tai masa sannu da zuwa ya amsa leda daya ya mika mata mai dauke da kaji aciki ya dora da

"ki juye a plate ki dau taki ki kawo wa sakna tata "

" To, yaya kamal, kaifa "?

" wannan ta ishemu "

dakinsa ya nufa tana ciki a kwance ta takure a Kan gado, Kan gadon ya nufa ya yaye bargon da ta rufa dashi yajata jikin sa yace

" My dear sannu da jiki ya kika wuni "?

Idonta a rufe take magana," Honey bee sannu da shigowa, yau da wuri haka, jiki Alhmdulillahil"

"Eh dole ce tasa na dawo da wuri saboda jikin naki, gsky kinashan wahala dear kina jina ko nazo da wata shawara ne wacce zata amfane mu ina son kibani hadin kai"

Shiru tayi tana juya zancan nasa aranta can ya nisa yace

Labiba kuwa duban jameel tayi tace

"Oh, tambaya ta kake jameel to da baka ganta wai meyasa kake son jan zancan da bashi da amfani bare maana "

" Allah ya huci zuciyar ki, miko min flaks din tea din na diba "

" Babu na shanye sai dai in wani zaka dafa "

Murmushi kawai yayi ya dau berif case dinsa ya fita da sauri ta biyo shi tasha gaban sa tace

" jameel kana jina ina magana kai min Shiru ko, saboda ka maidani yar iska ko "?

" Everlasting kiyi hakuri indawo ko ma meye ayi wlh nayi late fa "

Yana gama fada ya fita ya barta tana ta masifa wayar ta ta dauka ta shiga neman layin ashanty

Jameel yana fita gidan Hajiyar sa ya nufa tana zaune a parlor yai sallama ya shiga dagowa tayi ta zubawa dan nata ido kusa da ita yasamu ya zauna ya gaisheta kasa amsawa tayi can ta dubeshi tace

*Danmarayan zaki* anya kuwa kalau kake, yanzu daga Ina kake "

Shiru yayi saboda yadda yake jin sa wani iri zuciyar sa a takure hotan labiba kawai yake gani dagowa yayi yace

" Hajiya daga gida nake, dan Allah ki yi min addua narasa me yake damuna kwana 2 "

Mamaki ne yakamata da yace daga gida yake can ta nisa tace

Abdulmalik kuwa duban inna yayi yace

" inna kifadi duk abinda kike so zan miki amma kar ki rabani da mata ta dan Allah "

" Naji bazan rabaka da matar ka ba mai mata to amma ina son zan dawo gidan ka da zama, dan naga me ke faruwa ni fa ban yarda da matar ka ba asiri take maka baka sani ba "

" shikenan inna ki dawo amma sai
angyara miki dakin da zaki sauka "
Chapter 6 · 0% Book details