← Book details Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 25

Sashe 11

Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"to,uwar kinibibi daga yau nasa doka agidannan kai Abdulmalik inzaka bada kudin cefane ,to ni zaka dinga kawowa inyaso tazo ta karba a guna "

da sauri suka dago da kansu suka kalleta Abdulmalik ne yai karfin halin cewa,

*Hafeez*

~~~cikin kankanin lokaci Areefa tashirya tsaf,ta fito gidan ta rufe tai tafiyarta kai tsaye gidansu kawar ta tanufa ,nan sukai ta hira ,wayar tace ta hau ruri tana dubawa taga sunan Alhj namadi dariya tasaki suka tafa da kawartata dada gyara fuskar ta tayi suka fita a cikin mota suka sameshi

hafeez kuwa yana fita kai tsaye gidansu fauza ya wuce ,yana isa,yakirata awaya tafito,daukar ta yayi a mota suka fita,kai tsaye,wani babban hotel suka nufa ,isar su keda wuya ,suka ci karo da ,

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:29] ‪+234 814 620 5819‬: [5:57Am,2017]

*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦

💦N I G💦

*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA💐

*Alhmdulillahi lazi ahayana baada ma amatana wailehir nushur,Rabbi yasir wala taasir allahumma yasir alaina*👏🏻

*Wannan shafin🍆 nakine kawata JIDDATULLAH TIJJANI ,mai littafin ALMAJIRA,ina godiya bisa kwarin gwaiwar da nasamu daga gareki nagode sosai,hakan shi ya tabbatarwa da Naseeba ana tare ,dan haka kiyi komai da wanga page ba komai domin kuwa nakine ke kadai*🍆🤣🤣

💦
*Tsokaci game da littafin ZAMAN AURE, anya kuwa abinda naseeba ke rubutawa yana faruwa a gidajan auranmmu ko de shaci fadi ne kawai irin namu na marubuta ?fadi raayinki game da hakan*🙅🏻

*18*

~~~cikin daurewar fuska kamal ya ke dubansu sunkuyar da kai lubna tayi sakna kuwa kallon mamaki take masa cikin ranta take fadin

_"wai dama haka rayuwar aure take ,miji yacanja kamar bashine wanda ada kafin auran ku baya son duk wani abinda zai bata miki rai ,kullum burinsa ya faranta miki rai ba,amma gashi yau anwayi gari yazama kamar bakin kumurci ,wane irin ZAMAN AURE ,kenan sukeyi_

*Nasseeba kuwa cewa tayi da sakna,haka rayuwar auran take ,gaba dayanta hakuri ce domin kuwa ankirata da ibada,kenan ibada sai anyi hakuri*

maganarsa da yakewa lubna ne yadawo daita daga zancan zucin datake ,cikin dakewa yake fadin

"malama,tashi kishirya,minti 10,kawai nabaki zaki zo ki wani zauna,uban me kike cewa ,wlh lubna ki shiga ki maida hankalinki,kinji de nafada miki"

yana gama fada ya koma parlor ya zauna ,lubna kam baki ta turo tana kunkuni ahaka ta shiga toilet ta yi wanka,cikin kankanin lokaci tagama shirinta tsaf ,sakna na kwance tana kallonta kusa da ita tadawo ta zauna ahankali takira sunanta

"Aunty sakeena zantafi,nasan bainda zakuje ,kuma nafiskanci akwai matsala a *zaman auranku* saboda haka wlh sai nafadawa Hajiya da na koma kiyi hakuri"

saurin katse ta sakna tayi ta cikin raunin murya tace

"Haba lubna ,meakayi da har zakije kifadawa hajiya,to gaskiya banyardaba,kuma maganar tafiya da zamuyi tunda yafadi hakan,may be tafiyar zamuyi ,dan haka ni ban aikeki ba kuma kar ki soma "

dariya kawai lubna tayi,ta dau jakar kayanta ta mike dan tafiya,yunkurawa sakna tayi ta tashi tahadomata wasu materials sababbi da kayan kwalliya hade da kudi tabata ,godiya taimata ta nufi parlor ,yana zaune ya dora kafa daya kan daya ,yana ganin ta fito yaja dogon tsaki ya mike ,yafita binsa tayi a cikin mota tasameshi ,baya ta bude ta zauna, afusace ya juyo ya kalleta yace

"ke waye driver direbanki dazaki wani kame abaya ,dalla dawo gaba "

dariya ce taso kubcemata tayi kokari ta gumtseta gaban tadawo tazauna da sauri ya figi motar wani gigitaccan horn yashiga yi da gudu mai gadin yazo ya bude masa gate din ya fita,cikin kankanin lokaci suka isa gidan nasu ,begama yin parking ba lubna tafito daga motar kai tsaye dakin Hajiyar su tanufa tana zaune akan sallaya sai ganin lubna tayi ta zube ajikinta nan ta shiga tambayarta

"Auta wane irin sammako ne wannan kamar wata korarriya,ina sakeena ,da kamal din"?

baki ta turo gaba hade da narkewa ajikinta nan ta kwashe komai ta fada mata game da *zaman auran* kamal da sakna ranta ne yai masifar baci ,ana haka sai gashi ya shigo da kayan lubna da bata tsaya ta dauka ba wani kallo Hajiyar ta watsa masa take jikinsa yai sanyi jikinsa ne yabashi lubna tafadawa Hajiya tabbas yasan bazasu kwashe ta dadi ba,

*jameel*

~~"Dan marayan zaki anyawa kuwa babu abinda ke damun zuciyar ka nifa tunda ka auri yarinyar nan gaba daya kasanja ,meke faruwa da *zaman auranku*"?

murmushin karfin halin yayi ,dan bazai iya furta,mata komai ba yasha zuwa takanas dan yafada mata amma dayazo gabanta sai yakasa hoton labiba ne kawai a zuciyarsa ahankali ya dago da kansa yace

"Hajiyata,kar ki damu danki bashi da wata damuwa ,yanzumma dai labiba ce bata da lpy shine tace danwake zataci ,zuwa nayi kiyi mata kinji Hajiyata"

murmushi tayi dan ta fuskanci inda zancan nasa ya dosa tashi tayi ta shiga kitchen cikin kankanin lokaci sai gata da danwake a kula mai kyau,ta kawo masa yana kwance idonsa alumshe kamar me bacci ahankali takira sunan sa,

"Danmaraya,tashi ka kaimata kar tai ta jira,har yafitar mata a rai"

"to,Hajiyata sannu angode ,Allah yaja mun da ranki"

dariya tayi taamsa da "Ameen"

yatashi ya tafi,sanda ya karasa gidan tana parlor a zaune ,cikin rawar jiki yakarasa gabanta yaajiye mata kular agabanta kallonsa tayi awani yatsine tace

"jameel,sai yanzu ,to kadauke abinka banaci ,tun yaushe kafita"

cikin sauri yadago ya dubeta yarasa ma mezaice mata kawai sai ya ,

*Abdulmalik*

~~shiru inna tayi tana sauraran abinda Abdulmaliki zaice

"inna dan Allah kiyi hakuri,da abinda zance ,ni sai nake ganin kamar Ruhaima ita yakamata ana bawa kudin cefane ,amatsayinta na,mai girki......

batabari ya gama fada ba ta daka masa wata uwar tsawa tadaka masa tadora da

"yayi kyau,Abdulmalik,
yau ka tabbatar min da cewa matar ka gaba take da mahaifiyarka to nagode da irin wannan sakayyar to amma kasani ,kan takarasa tasaki kuka

hankalinsu ne yatashi Ruhaima ce ta dubi Abdulmalik tace

"Malik,ayi yadda inna keso ai ba wani abu duk daya ne ,dan Allah inna kiyi hakuri "

"Dallacan rufemin baki munafuka ,juya kawai baki da aiki sai lashewa dana kudi ki haihu ,kinki ki haihu saboda tsabar mugunta "

shiru sukayi karshe suka bata hakuri hade da bata kudin cefanan yafita daki Ruhaima ta koma tasaki kuka mai tsuma rai ,

da yamma tana kitchen ta kusa kammala girki kawai sai ga inna taja ta tsaya a kofar kitchen din ,cikin daga murya ta kira sunanta

"ke Ruhaima uban me kike dafawa ,ko san ranki kike dafawa "

"inna sannu da fitowa,amm dama tuwan shinkafa nake miki "

"to,sauke bashi zanci ba,alkubus nakeso"

shiru Ruhaima tayi tarasa ma mezatace can ta sauke girkin ta koma daki ,binta innar tayi har dakin ,

*Hafeez*

~~cikin kissa Areefa ta kalli Alhj namadi shi dinmma ita yake bi da asirtaccan kallonsa irin na yan duniya hade da kiran sunanta

"my love,daga nan sai ina muka nufa,?

dariya tayi hade da kashe masa ido sanan tace,

"Duk inda ranka yaimaka zabi,domin kuwa zabinka shine nawa"

jinjina kai yayi hade da lakacemata hanci yaja motar suka tafi kai tsaye guest house dinsa suka wuce,nan suka hole abinsu ,dazata tafi yadakko kudi masu tarin yawa yabata ta bude kofar gidanta ta shige

Abdulmalik kuwa karo sukai da tsohuwar budurwar sa mai suna Anisa,murmushi yasakar mata ya karasa gurinta nan suka gaisa tambayarta yashiga yi

"Anisa ,kwana da yawa kinya dani "

kallonsa tayi ta lumshe ido,take yagane nufinta

Fauza kam tana tsaye tana kallonsa ,yagama da Anisa,ya karasa inda take wani banzan kallo tasakar masa tai tafiyarta .

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:30] ‪+234 814 620 5819‬: [6:00Am,2017]

*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦

💦N I G💦

*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA💐

*Hasbunnallahu waniimal wakil laila hailla anta subahanaka inni kunti minal zalimin*😰👏🏻

*Innalillahi wainna ilehir rajuun allahumma ajirni fi musibati waakilfini khairan minha ,ina taya daukacin dangin ALHJ UBA GAWO alhini bisa rashi da mukayi na SHAMSUDDEN Y UBA, muna rokon Allah yajikansa da rahama yasa ya huta ,hakika misalta halin da muka shiga abin zaizama kamar bata yawun baki da wannan damar nake rokon Allah da ya bawa iyalan Alhj ISMAIL UBA GAWO hakurin ibtilain da yaafka mana na rashin yaron nan ,haka kazalika ina rokon Allah da yaji kan SHAMSUDEEN B UBA Allah yaimasa rahama yasa ya huta Allah karaya SHAMSUDEEN U UBA kabashi halin yaya shamsun da muka rasa AMEEN*😭👏🏻

*19*

~~~Ahankali kamal ya karaso yasami gefan mahaifiyarsa ya zauna lubna ce ta dago da kanta ta kalleshi harara ya auna mata da sauri ta dauke idonta cikin ladabi ya gaida mahaifiyar tasu taamsa ba yabo ba fallasa can tadubeshi da kulawa tace

"kamaludeen ,meke faruwa a gidan naka,gashi kuma naga kakawo auta da sassafe lpy de ko?

kansa yadada dukarwa kasa ya zubawa kafet ido,kamar maison samo amsa a nan,can yadago suka hada ido da mahaifiyar tasa ahankali yace

"Hajiya,dama sakna ce bata da lpy ga shi inason zuwa kwatano,shine nakeson na maidata gida,saboda yanayin jikin nata,amma bawata matsala da muke da ita"

ido tazubawa fuskar dannata dan son gano gskyr zancan nasa lubna kwa takafe shi da ido cikin saa ya dago ya kalleta da ido ya gargadeta hajiya ce takatse shi ta hanyar kiran sunansa

"kamaludeen,ni kullum bazan gaji da fada maka cewar kaji tsoran Allah ba kasani akwai mutuwa akwai hisabi,mutukar ka zalinci yar mutane tofa ,Allah baze barka ba,to ma me zaihana ka kawo min ita nan har kadawo"

shiru yayi dan yasan dole hajiya zata iya cewa haka cikin kwantar da murya yace

"Hajiya ai nariga nafadawa mamanta zankawo ta ,da sai nakawo miki ita "

"To shikenan badamuwa ai duk daya ne ,Allah yabata lpy "

"Ameen Hajiyarmu ,Abba fa yanan ne ?

"eh yana nan dazu de yafita taaziya amma yadawo,kashiga ka gaida Mama "

"To,ke lubna zo nan"

fita yayi tabi bayansa,sai da suka bar dakin Hajiyar sannan ya tsaya ya juyo ya zuba mata ido,hade da daure fuska yace

"ke ,wlh mutukar kikafadawa Hajiya zancan gidana wlh sai jikinki yafada miki ,kinji de nafada miki "

turo baki tayi gaba tana kunkuni kasa kasa,ganin yayo kanta ne yasa ta amsawa da

"Thom,naji"
Chapter 11 · 0% Book details