← Book details Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiru yayi ,kalaman inna suna zame masa kamar saukar garwashi ,sai da tagama tsaf sannan yatashi ,kai tsaye gidan su Ruhaima ya nufa,

tsayawa yayi akofar gidan yana jiran dan aike ,ita kam tana shiga,
tafada jikin mahaifiyar ta,hankali tashe uwar tashiga yimata magana,

"Subahanallah ,Ruhaima lpy meke faruwa,ina Abdulmalik din"?

shiru tayi ana haka sai ga mahaifinta ya shigo,guri yasamu ya zauna tare da gyaran murya yace,

"ke,Ruhaima tashi ki zauna bana son shashanci,yazaki zo kisamu agaba kina kuka,meye haka?

tashi tayi,tare da share hawayen fuskar ta tace,

"Abba,innar malik,batasona,tarabani da shi,ta korone,wai dole sai ya sakeni"

Ransu ne yaimasifar baci ,ana haka sai ga Abdumalik yayi sallama yashigo,

a tare suka daga kansu suka dubeshi ko wanne fuska ba walwala cikin fushi abba yadubeshi yace,

*Hafeez*

~~wata kyakyawar yarinya Hafeez yagani amma abin haushi kan yadago ya dago har ta bacewa ganinsa murmushi yasaki tare da shafa sumar kansa,wata jaka karama ya dauka ya koma dakin da suka kama yana shiga idonsa yagane masa,

Areefa kam tana kwance da wayar ta a hannunta ,bugu biyu Alhaji Namadi ya daga kiranta ,wata dariya yasaki tare da fadin,

"zumata,sanyin idaniyata masoyi yata,abar alfaharina yaakanyi ne?

murmushi tasaki mai sauti tare da kashe murya tace,

"sweet heart,kewar ka tahana ni sukuni ,nakasa runtsawa wlh ,yazaayine?

"ya kike so ayi mai zakin"?

"kana ina yanzu?

"Ni ina guest house,dina amma zaniya zuwa inda kike cikin kankanin lokaci ya kikeso ayi ?

shiru tayi tana nazari can tanisa tace masa,

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:41Am,2017]

*@💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦💦

*💦N I G*💦

*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA💐

*Allahumma salli ala muhammad wasallim,ya hayyu ya kayyumu birahamatika astagisu*👏🏻

💦
*wannan shafin sadaukarwa ne ga tsohon principal din sheik maihula secondary school Allah kaji kansa da rahama ,halinsa nagari yabishi ,ina mika sakon taaziya gareku daliban wannan makaranta musamman yan shekarar 2009 wato kiyaya*🎓

*25*

~~Dada rusunawa kamal yayi,yana sauraron Hajiyar tasa,

"kamalu kanajina ko,bazaka samu damar ganin sakeena ba,saboda bansan mezakace mata ,bana bukatar dada sata a damuwa kai kuma baka da burin da ya wuce,kabata ciwon kai,saboda haka shige ka tafi naka guri,ka karaci sakarcinka kai kadai"

"Dan Allah ,Hajiya
kiyi hakuri ,wlh bazan sata a damuwa ba,inshaallahu zankiyaye"

dariya tayi har sai da hakorin ta na maka ya bayyana tadora da,

"Kamalu kenan ,ai sai kayi amma nikam nagama magana,saboda haka tashi ka tafi gidanka ka kwanta"

shiru yayi kamar zeyi kuka,can ya mike kamar wanda aka tsirawa allura,abakin kofa yaci karo da saif,dubansa yayi da kulawa yace

"Yaya kamal,lafiya kuwa,meyasameka haka?"

dada hade rai yayi tare da dan yin gaba yaja dogon tsaki, sai kuma yaja yatsaya yace

"Abba fa "?

"Abba yana sama ,bedade da dawowa ba,dan yau ya dade a waje"

tsawa yadaka masa tare da sakar masa harara yace,

"kai de banza ne wlh kawai tambaya daya naima amma sai da kabani amsa goma,malam wuce da Allah"

murmushi kawai saif yayi,ya shige dakin Hajiya gurin sakna ,kamal kuwa kai tsaye part din abban su ya wuce dauke da sallama a bakinsa ,mama ce taamsa cikin nutsuwa ya kutsa kai ya shiga tare da samun gefan abban nasu ya zauna ,cikin kwantar da murya yace,

"Abba,barka da dare"

"yauwa kamalu,kana lpy,ya jikin matar taka"?

shiru yayi tare da shafa sumar kansa dan dama abinda yakawo shi kenan,can yanisa yace

"Abba bansan yadda jikin nata yake ba,Abba Hajiya tahana ni ganinta wai ciwon kai nake bata,dan girman Allah Abba kasa baki tabarni inga jikin nata"

shiru Abba yayi tare da zubawa dan nasa ido,can yanisa yace,

*Jameel*

~~ido,jameel ya zubawa labiba,tare da sauraron mezata ce,game da mai kiransa shiru tayi can ta nisa can tanisa tace,

"jameel,number ce,may be ma kiran bashi da amfani kawai bari akashe wayar ko?

"bani da wani zabi face zabin ki Everlasting,a kullum jameel mai bi ne a gareki"

wani shuumin murmushi tasaki tare da kashe ido,

abangaran Hajiyar jameel kuwa gajiya tayi da bugu,ga shi wayar sa ma ankashe,hakura tayi ta tafi,kai tsaye gidan yayar ta nufa,tana zuwa tasameta zaune a madai daicin parlornta,da sakin fuska ta tareta ,suka gaisa ,shiru Hajiyar jameel tayi ,dubanta Hajiya Dije,tayi tace,

"Bilkisu,fuskar ki ta nuna damuwar da take cikin zuciyar ki,ko meke damunki"

nannauyar ajiya zuciya tare da duban yayar ta tace,

"yaya,ina cike da damuwa matar Dan marayan zaki bata da kirki nadade da fuskanta akwai matsala a *zaman auransu* to gudun zargi naki gasgata hasashena amma yanzu nagama tabbatarwa ,yaya jameelu,fa yarasa aikinsa asanadin matarsa ,nide banyi saar sirika ba "

dubanta Hajiya Dije tayi,da tausayawa kana ta numfasa tace,

"subahanallah,abu be dadiba bilkisu,meyasa baki taba fadaminba,to amma ba komai mudage da addua ai baabinda yafi karfin Allah ,mukaiwa Allah kukanmmu inshaallahu zai mana magani"

nan de sukai ta tattaunawa karshe taimata sallama ta tafi tare da daura dammara kubutar da tilon dan nata,

kamar kullum jameel ne a kitchen yana soyawa labiba doya da kwai kawai sai ganin ,

*Abdulmalik*

~~Gaban Abdulmalik ne ya yanke ya fadi saboda,yadda abbban Ruhaima yake duban sa dada russunawa yayi yana sauraransa,
cikin masifar fada yake fadin,

"Abdulmalik,ina ganin in *zaman auran nan* zai kawo matsala tsakanin ka da mahaifiyarka to gwanda a hakura "

cikin sauri yadago da kansa ya dubi abbban Ruhaima,yace,

"dan Allah aimin afuwa,wlh inason Ruhaima kar arabani da ita dan Allah"

"Abdul malik kenan kanason Ruhaima ,to ai mahaifiyar ka bata sonta kaga kuwa akwai matsala ,ni ina ganin kaje kawai ka aikomin da takardar sakin Ruhaima hakan kamar shi zaizama masalaha"

a razane Abdulmalik ya dago ya dubi abbba,zaiyi magana ya dakatarda shi tahanyar daga masa hannu yadora da,

"tashi kaje ,kawai zan nemeka"

ido Abdulmalik yazubawa Ruhaima itama shi take kallo,atare wasu hawaye suka zubo daga idanunsa,sauri yayi yamike ya fita kai tsaye mota ya nufa yasaki kuka mai tsuma rai,

inna kuwa waya taiwa yayar Abdulmalik da tazo tana kiranta,bata jima ba ta zo tana shiga tasaki kuka ,cikin tsananin tashin hankali Rabia ta dubi inna tace,

"yasalam,innarmu,meyasameki,me akaimiki,ina matar gidan?

sai da inna ta share majina da gefan zaninta sannan ta dubi Rabiaa tace,

*Hafeez*

~~Yarinyar da yadakko ya nema yarasa ta kwashe masa wayoyinsa guda biyu masu masifar tsada,nan yashiga duba amma baita ba alamar ta fitowa yayi reception din ya shiga tambaya ko anganta duk maaikatan sai suce basu gantaba,gajiya yayi ya koma dakin ya dibi ragowar shirgin sa ya nufi gida ransa a mutukar bace,yana shiga gidan
yatarar da Areefa, bata nan,take ransa ya kuma baci kan doguwar kujera yasamu ya kwanta aljuhunsa yafara dubawa dan daukar wayarsa dan jin inda matar tasa ta fita batare da sanin sa ba, ji yayi wayam,hannu yasa yadafe kansa,tare da sakin dan siririn tsaki,ya maida kansa ya kwanta idonsa ya kada yai jazur saboda bacin rai,

Areefa,kam suna cikin waya da Alhj Namadi ta tabbatar masa da gatanan zuwa inda yake bata bata lokaci ba,ta shirya tsaf ta nufi guest house dinsa dan sheke ayarsu,sun dan jima atare sannan ya dakko ta yadawo daita gida ,kamar amafarki Hafeez yaji tsayuwar mota a kofar gidan nasa tashi yayi ya leka dan ganin waye a motar ,cikin bugun zuciya idonsa yagane masa abinda betaba tunani ba,take,yaji shi yanajiri yatafi luuu ya,

_ZAMAN AURE_🤔

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:45AM,2017]

*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦

*💦 N I G*💦

*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA💐

*wallahu galibun ala amrihi wala kinna aksarin nasi la yaalamun,subahanallahi wabihamdihi subahanallahil azim*👏🏻

💘💕💘
*wonderful day 2 a wonderful girl ,2 day, is a special day the day that borne a queen Happy birthety Fadila Bilal Abdullah whish u many yrs a head ,my dear daughter HIP HIP HURRY FADILATY BINTY*🎊🎂🍭
*Assadiq said Happy birthday fadilaty ukuty*😘👌🏻

*26*

~~shiru kamal yayi yana sauraran abinda abban nasa zaice,cikin nutsuwa abban yake fadin,

"kamalu,to ai hakuri zakai bisa hukuncin da mahaifiyar ka ta yanke,kabari matar taka tadada samun sauki tukunna kaji"

cikin shagwaba yadago yadubi abban nasa yace,

"Abba ,baka fahimceni ba,nifa bacewa nayi adawo da ita ba ,kawai abarni inga yanayin jikin nata ,dan Allah mama kisa baki"

murmushi mama tayi tare da duban mai gidan nata tace,

"Alhj dan Allah kasa baki kamal yasamu yaga matar sa ayi hakuri"

"Dakata du Allah ,Hajiya mama,ke kamalu tashi kaje gida,gobe kadawo"

Abba.....

kan yakarasa ya dakatar dashi ,ba yadda yaiya haka yatashi jiki ba kwari ya fito,kai tsaye gurin motar sa yanufa ya dade aciki kafin yaja ta ,mashaya yanufa,yana zuwa aka kawo masa ruwan da yasaba sha,ido yazubawa kwalabar kamar mai son gano wani abun aciki,a hankali ya furta

"No,imposible"

tashi yayi ,yafita kai tsaye gidansa ya nufa ,yanashiga yai parking din motar sa ,yanufi parlornsu a kan doguwar kujera ya kwanta tare da jan dogon tsaki,wayarsa ya dauka yashiga neman layin sakeena ,tana kwance tunanin kamal dinta fal ranta sai jin karar wayar ta tayi da sanyin jiki tasa hannu ta dauka tana dubawa taga *honey bee* a screen din wayar da sauri ta danna tare da kara wayar akunan ta ,

*Jameel*

~~cikin azabar jin zafi jameel yafasa kara,sakamakon mai da ya sheko masa akafa,da sauri labiba,tayunkuro ta nufo kitcheen din ganin jameel na yarfa hannu ne yasa ta tambayar sa,

"Jameel lafiyar ka,sai kace ba namiji ba kafasa uwar kara ,wlh kabamu tsoro"

cikin radadi da azaba jameel yadago ya dubi labiba yace,

"Haba Everlasting meyasa baki da tausayi konewa fa nayi da mai ,amma me makon ki tausayamin sai kina yimin mitar nabaki tsoro"

"oh! ashe konewa kayi ai bansaniba sai da bakinka ya furta hakan ,Allah ya kiyaye gaba,ni bani wacce kasoya ,wlh yunwa nakeji"

ido jameel yazubawa labiba ,saboda yadda take gwada masa rashin tausayi,hannu tasa ta dauki wacce yasoya,tafito,gas din yakashe yafito kai tsaye bedroom ya nufa ya kwanta,yai lamo yana tunanin hali irin na matar tasa,

abangaran Hajiyar sa kuwa tun da taisa gida ta dukufa da addua da sadaka dan samun kan dannata ahankali yafara samun nutsuwa a ransa ,yauma kamar kullum yana zaune a parlor labiba tafito cikin kwalliya ga cikin ta da ya tsufa da kyar take takawa dagowa jameel yayi ya kalleta tare da fadin

"ina zaki kenan da wannan katon cikin,kina son ki haihu a hanya ne"
Chapter 15 · 0% Book details