← Book details Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"oh! ke yanzu jira ma kike yi, kiyi wani arba'in,cab wasa ma kenan to ai kafin sannan nagama mutuwa"

dariya yabata,dajin furucin nasa,dada zuba mata ido yayi take yaji wani alamari na ziyartar gan gan jikinsa,cikin sauri yafara jan numfashi,ahankali ya kwantar da khalid a cikin dan gadonsa,gefanta yadawo yajata zuwa jikinsa,cikin zakuwa yafara shafa gadon bayanta,hannun sa yakai kan zip din rigarta zai zuge da sauri takama hannusa tarike gam ,dagowa yayi ya zuba mata idanunsa da suka rine suka zama jajaye cikin wata iriyar murya yace,

" me kuma haka? yanzu sakna bakijin tausayin mijinki ko? yaushe rabon da inji dumin jikinki, ko kina son inje innemi matan waje ne?"

yafada yana tsareta da ido,ahankali ta girgiza masa kai alamar aa,muryar ta na rawa tace,

"Honey bee,wlh tsoro nakeji kar inkuma samun ciki,kuma...

kan takarasa maganar yatoshe mata baki danasa nan yashiga tsotsa kamar wanda yasami alawa yayi nisa ,ya kuma shgala kawai saijin muryar umman Sakeena sukayi.

*_Jameel_*

~~Haka rayuwar labiba tai ta tafiya cikin kunci da bacin rai tare da tunanin tsohon mijinta Jameel,yau tun safe take shiri zata fita,Momy na kallanta tazuba mata ido,tagama shirinta tsaf tacaba kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar kyau,dad'a dubanta Momy tayi tace,

"ke kuma,ina zaki haka"?

"Momy zanje gidan Khadija ne fa"

baki ta tabe,tare da kawar da kai gefe tace,

"sai kindawo,kar kuma ki dade"

shiru Labiba tayi kamar batajita ba tasa kai tafita,

tana fita ta tsare adai daita sahu,ta
hau,tun fitowar ta wani Alhajin birni ya ganta bayan adai daitan yabi dan ganin yacimmata, kaitsaye gidan jameel ta nufa dauke da addua abakinta ,

cikin kankanin lokaci hidimar bikin jameel ta kankama, ankai lefe, nagani na fada,kamar mai shirin yin auran fari,biki yarage saura sati biyu,

tun yamma Jameel yake zumudin zuwa wajen Munira,yana tashi daga aiki yakoma gida yai wanka tare da caba ado,sanye yake da shadda multi colour,tai masa mutukar kyau,sai kamshi yake zubawa,wayarsa ce tahau ruri da sautin kida mai dadi,hannu yakai kan mudubi,wanda ke daure da agogo silver da zoban azurfa,ahankali yakara wayar a kunansa,yace,

"Hello bride 2be"

dariya tayi har sai da yajiyo sautin dariyar tata
ta muryar ta mai dadi tace,

"Hello Groom 2be "

"Au ramawa kikayi to shikenan nagode yaakayi"?

cikin shagwaba tare da karyar da murya tace,

" nifa ba ramawa nayi ba,kafasa zuwa ko"?

kwaikwayar muryar ta ta yayi yace,

"Banfasa ba,mekika tanadar wa angon naki"

"shine kake kwai kwayata ko,shikenan nafasa fada maka abinda zanfada"

dariya yayi tare da bata hakur,karshe sukai sallama yakashe wayar,mukullin motar sa ya dauka yanufi hanyar waje dan tafiya gurin sahibar tasa,

fitowarsa tayi dai dai da zuwan Labiba,da sauri ta sallami mai adaita ta,takaraso inda Jameel yake,haka Alhajin nan yana cikin mota yana kallonsu,

*_Abdumalik_*

~~cikin dakakkiyar murya Abdulmalik yacigaba da fadin,

"Dafarko inai miki barka da zuwa gidana ,sannan inai miki murnar samun nasarar auran gangar jikin Abdulmalik,nasan kinsan komai game da aurena da ke ko?bakya bukatar karin bayani saboda haka sai kisan yadda zaki tsara *_zaman auranki_*"

ita de tana zaune tayi shiru saboda d'unbun mamaki ,ahankali tasa hannunta dayasha zanan kunshi ,ta yaye mayafinta tare da dagowa ahankali ta kalleshi dan murmushi tayi tace,

"Hmm,Allah sarki ango,to ai Mariya ma bawani sonka take ba,kawai mun taimakawa tsohuwa ne,dan haka kar kadaga hankalinka akaina shi *_zaman aure_* ai kamar karatu ne,wanda yaiya allonsa ya wanke"

mamaki yashiga yi sosai dajin furucin nata,basarwa yayi ya nufi dakinsa yabarta,itama shirin kwanciya tayi ta kwanta,da safe inna ce tayo musu break fast,taajiye shi a dakinta,Abdulmalik kuwa,da sassafe yafito da shirin sa tsaf na fita,dakin inna ya nufa tana zaune da kayan abinci agaba,guri yasamu ya zauna suka gaisa,dubansa tayi tace,

"Aa Abulmalik yanaganka kai kade ina Mariyar "?

kamar bazai amsaba dan besan mezaicemata ba can yagyara zaman hularsa yace,

"Tana daki"

"kamar yaya tana daki,ba tare kuka kwana ba ne"?

jin tambayar tata yayi kamar saukar aradu,dan sunkuyar da kansa kasa yayi ,dan bashi da amsar da zai bata,anahaka sai ga Mariya ta fito,sanye take da riga da zani na atamfa ta tsiro daurin dankwali,inna tana ganinta ta hau washe baki,daure fuska Mariya tayi tasami gefan innar ta zauna ,kamar bazata gaisheta ba,can kuma tanisa tace,

"inna antashi lafiya"

jikin inna na rawa tare da washe hakoran da suka dafe da goro tace,

"lafiya lau yata,ya bakunta,dafatan de bawata matsala"

"lafiya lau,wace irin matsala kuma inna?,dagayin auran,Allah yaimana katangar karfe da matsala"

Ameen diyar albarka ai dama baafatan ta"

Abdulmalik de yana zaune mamaki yagama kashe shi,inna ce takatse masa tunanin dafadin,

"Mariya ga abun karyawa bisimillah "

"ya tsine fuska Mariya tayi,tare da duban inna tace,

" Inna gaskiya bazan iya ciba,saboda ni ba abincin kowa nake iya ciba"

shiru inna tayi ta zubawa Mariya ido amma sam bataga laifintaba,haushi ne yakama Abdul malik yatashi yafita batare da yayiwa innar tasa sallama ba,aransa yake fadin _kindakko ruwan dafa kanki_

*_Hafeez_*

~~da safe Hafeez yagama shirin sa tsaf,ahankali yabude kofar dakinsa,da Areefa yai tozali kwance kan kujera tanata sharar bacci wani murmushi ne yasubuce masa,ya shigeta yai tafiyar sa,kai tsaye gidan wan mahaifinsa ya wuce,yai saa kuwa yasameshi bayan sungaisa ne yadada gyara zama yace,

"Baffa dama wata muhimmiyar magana ce takawo ni gurinka"

"inajinka Hafeez,Allah de yasa lafiya"

"lafiya kalau,Baffa,ina son zankara aure ne,shine nakeso anema min auran yarinyar"

"To,ai babu matsala,Hafeez,
Maman taku tasan da maganar auran naka"?

"Eh Baffa tasani"

"mashaallah babu damuwa zanje ,sai kaimin kwatancan gidan su Matar"

"To,shikenan Baffa nagode Allah yakara girma"

nan yaimasa sallama yatafi tare dayimasa alheri,kai tsaye gidansu Ashanty ya wuce,

nan suka sha hirarsu,tare da fadamata zai aiko neman auranta,wata shu,umar dariya tayi irin tasu ta yan duniya,

Areefa kuwa sanda ta farka da sauri ta tashi ta nufi dakin Hafeez,abude taji dakin da sauri ta kunna kai ciki,abun mamaki baya ciki,da sauri ta nufo harabar gidan,gani tayi babu motar sa,wani mahaukacin ihu tasa,tare da zabarar mayafi tafita,

*_NASEEBA GAWO_*✍🏻
[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [7:55PM,2018]

*_®💦💦💦NASEEBA GAWO_*💦💦💦

*_💦N I G_*💦

*_ZAMAN AURE_*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*_NA_*

*_NAEEBA I UBA_*💐

*_Allahumma salli ala sayyadina muhammadin wasallim_*👏🏻

*_37_*

~Cikin sauri Kamal yacika Sakna tare da gyara mata zip din rigarta,cikin inda inda taamsa kiran da Umman ke mata,

"Naam Umma"

"zo kidaukarwa Kamaluddeen ,abinci Hajir har yanzu shiru bata dawo ba"

to,Umma gani nan"

kafe ta da ido kamal yayi,tare sakar mata murmushi,dauke kanta tayi ,tafita tana dariya,motsin da Khalid yayi ne yasa Kamal tashi daga inda yake yakarasa gaban gadon Babyn, yasa hannu ya dakko shi,tare da komawa bakin katifar yazauna kuka yafara yi tare da neman Nono,ahankali yasa masa lebansa a baki cikin sauri yakama yashiga tsotsa,ahaka sakna tashigo tasameshi, tare da ajiye tray din hannunta zama tayi a gefansa ,tazuba musu ido,can tanisa tace,

"Honey bee,baka tsoron yayima tunbud'i"

mikamata Babyn yayi ,tare da sa tissue yagoge bakinsa yace,

"Badamuwa ai ana tare ko Born boy, da Allah yi kibashi yasha banason jan rai"

ashagwabe takalleshi tace,

"Honey bee,wallahi yaron nan naka tsotsone dashi,ka duba fa kaga yadda nabi na rame nide..."

ido yazubawa bakinta harta kai aya,zata kuma dorawa kenan ya katseta ,

"Haba Sakeena yanzu dan kina shayar min da d'a shine zaki sani gaba kina mita,ok badamuwa,abinda nake ganin zai zamar mana masalaha shine,kifadi nawa zanbiyaki kishayar min dashi cikin kwanciyar hankali"

da sauri tadago da kanta ta kalleshi ,shima kallonta yacigaba dayi ,danjin amsar da zata bashi,

cikin kwanatar da murya tadubeshi tace,

"Afuwan Honey bee,wallahi bahaka nake nufi,amma innabata ma rai Allah ya huci zuciyarka"

"Ameen,zuba min abincin inci,sauri nake zanwuce gida,kuma kizama cikin shiri nan da ranar assabar zaki koma"

shiru tayi masa dan tafahimci yabirkice yanzu data kulashi zasu yi kaca kaca aranta tace,

_Zaman aure kenan sai hakuri_

abincin tazuba masa tare da tura masa gabansa,dauke kansa yayi cikin dakewa yace,

"Au abincin ma bazaki sami damar baniba,da kaina kikeso naci ko me?

hannu tasa tadauki cokalin tashiga bashi abaki ,ahaka har ya koshi,kudi yaajiye mata ,yamike zai tafi,ahankali takira sunan sa,

"Abu khalid"

dadine yakamashi yace,

"Sakeena,yaakayi"?

"pls kayi hakuri kaji,inshaallah bazan kuma ba"

"karki damu yawuce,ki kularmin da Born boy"

yanagama fadar haka yasa kai yafita,shiru Sakna tayi tana mamakin hali irin na kamal.

*_Jameel_*

~~Dauke kai Jameel yayi yasa hannu yabude motar sa,dasauri tasa hannu ta dakatar dashi, tare da kiran sunansa,

"Yaya Jameel"

haushi da mamaki ne suka kama Jameel cikin daure fuska yace,

"Yaakayi"?

shiru tayi saboda yadda yaimata kwarjini can tanisa tace,

"Dan girman Allah da mamzansa kayi hakuri kayafemin wallahi nayi nadama kadawo dani dakina inshaallah zaka sameni mai mutukar yima biyayya"

murmushi yayi mai cike da takaici ko na kinma rainawa kanki hankali yace,

"Labiba ai kinbar kari tun ran tubani,atakaice de ina mai tabbatar miki da kin makara dan ayanzu haka saura sati daya bikina da matar danake fatan yimin biyayya tare da *zaman aure* bisa gaskiya da amana,saboda haka kukara hakuri ga wannan kibawa Abba ko zai sami halatta ,sai anjima ko?

shigewarsa yayi cikin mota yai tafiyarsa yabarta tsaye da katin daurin auransa a hannu,kasa dubawa tayi saboda fargaba,sai da kyar tasauke idanunta kan iv din kamar amarfaki taga sunan jameel da wata ba ita ba,wata razananniyar kara tasaki take ta sulale kasa,cikin matsanancin sauri Alhjn nan yanufo gunta,tozali yayi daita numfashinta nasama da kasa wasu mata ya kira akidime suka taimaka masa aka sata a mota,har yazagaya zaishige motar ya hango jakarta komawa yayi yadauka kai tsayecasibiti yanufa daita,

Jameel kuwa bezame ko ina ba sai wajen su Munira nan suka zauna a sittroom din gidansu ,suka sha hirar su mai cike da so da kauna katin bikinsu ya mika mata,hannu tasa tare fuskar ta dariya tabashi saboda yadda take jin kunyarsa kallonta yayi yace,

cab,naga ta yadda zaai wannan *zaman auran*matar najin kunyar mijin"

dariya kawai takuma yi tare da karbar katikan da yakawo mata,sallama sukayi yatafi cike da begenta kai tsaye gurin Hajiyarsa yawuce nan yabata labarin zuwan Labiba murmushi tayi tace,

"Ai Danmarayan zaki arayuwa karka sake ka dau hakkin mutum,gashinan alhakinka yahana rayuwar ta sukuni,Allah de ya kyauta"

"Ameen Hajiyata"
nan suka cigaba da hirarsu gwanin shaawa .

*Abdulmalik*
Chapter 23 · 0% Book details