← Book details Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 25

Sashe 18

Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dariya usman yasa da yaji muryar jameel ,yadora da ,

"jameel kenan ni ne mana lafiya kuwa najika so silent akwai matsala ko "?

ajiyar zuciya jameel ya sauke sanan yadora da ,

"usman kana gari kenan "

"nadawo jameel ,yanzu haka ma ina hanyar zuwa gidanka inafatan kana gida"?

shuru jameel yayi kamar mai nazarin wani abu,a hankali ya bashi amsa tare da godewa Allah da dawowar usman ,zama yayi yacigaba da jirans karasowar sa,

*Abdulmalik*

~~cikin son jin damuwar abokin nasa mansir yake tambayar Abdulmalik shiru kawai yaimasa tare da cigaba da dafe kansa,ahankali yace,

"mansir asibiti zaka kaini,koma de meye mayi maganar daga baya"

"To amma abokina zanso.......

hannu yadaga masa alamar yai shiru ,yadora da,

"Dan Allah dan annabi mansir kabarni ka na neman dada bani ciwon kai ,nace zanfada maka koma mene ne ko"

sanin halin abokin nasa ne yasa mansir yin shiru ,yaja motar suka nufi asibiti basu jimaba suka karasa sundan dade kafin susami ganin likitan suna shiga Abdulmalik ya yanke jiki yafadi,da sauri likitan yataso ya nufo kansa hankalin mansir ba karamin tashi yaiba,

inna,kuwa bayan sungaisa da babar mariya ta dada gyara zama tace,

"wato Hajiya asabe, dama zuwa nayi nemawa Abdulmalk auran mariya,dan dada karfafa zumuncinmmu"

shiru Hajiya asabe tayi can tanisa ta dubi aminiyar tata tace,

"To,naji dadin batukinki Binta,to amma ina matar sa take,kinsan fa mariya bazata zauna da kishiya ba "

dariya momy tayi sannan ta dora da,

Ruhaima,kuwa innalillahi kawai take furtawa cikin tausayawa ummanta tafara yimata nasiha tare da kwantar mata da hankali murmushin karfin hali Ruhaima tayi ana haka sai ga mahaifinta ya shigo ganin yanayin da yar tasa take ciki ne yasa shi saurin zama tare da mai da dubansa ga umman ta,

*Hafeez*

~~Ashanty tana daga wayar Hafeez tai shiru ajiyar zuciya yasaki sannan ya dora da ,

"Hello my dear Ashanty,kina lpy"

"lpy ,yau ka tuna dani kenan,ai wlh Hafeezu,baka da mutunci"

"yi hakuri tawan ,kiyimin uzuri wlh abubuwa ne suka sha kaina amma de yanzu kina ina?

"Hmm,ina inda kasanni mana,har yanzu bancanja sheka ba tukunna"

"yauwa tawan kinajina yanzu ina gidana ko zaki zo kosameni"

dariya tayi sai datayi mai isarta sannan tace,

"Hafeez kenan bama kai kazo ba ni zanzo lallai kam"

"eh akwai dalilin dayasa nake son kizo ne pls"

shiru tayi can ta nisa tare da tauna cigam yace kas ,tace,

"ok badamuwa kajirani nana minti 30"

"yauwa tawan "

sukai sallama suka kashe wayar tashi yayi yanufi kitchen dan nemawa cikinsa abinci,

Areefa kuwa tana fita kai tsaye gidan su Hafeez ta nufa tana shiga tasaki kuka ,cikin tashin hankali mahaifiyar sa tashiga tambayar ta

"Areefa lafiya meyafaru,ina Hafeezun"

shiru tayi can tashare hawayenta ta dubi mahaifiyar tasa tace,

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:00AM,2017]

*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦

*💦N I G*💦

*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA💐

*Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillahi azim*👏🏻👏🏻

*Dedicated this page 2 my brother Nazeer yusif muazu ango 2 be may Allah bless ur marrige live in peace ,Happines love , and Honest ya Allah! i whish them 2 live 2gether Ameen*👏🏻💔

*30*

~~cikin sauri kamal ya labe abayan kofa sakna kuwa murmushi tasakarwa lubna tare da jan hannunta suka nufi parlor ,dubanta sakeena tayi tace

"kanwata, har kintashi , Hajiya fa ?"

" tun dazu, Hajiya,suna parlorn Abba ita da mama,tun dazu take ta murda kofar ki arufe"

shiru sakna tayi can ta dago ta kalleta tace,

"Ayya nakoma bacci ne,yanzu de yunwa nakeji wlh me Hajiya taimana,?

"tea da dankali da kwai ,amma ke,me kike son ci ?"

" wlh,lubna dama zansami kunu da nasha ,shi nakeson sha banason shan tea"

"Ai kuwa naga Suhaif yana shan kunu,bari inje inkarbo miki"

"yauwa kanwata nagode sosai"

dariya lubna tayi ,ta tashi tafita ,cikin sauri sakna ta tashi ta leka dakinta ,dariya tasaki saboda yadda kamal ya labe abayan kofa,cikin tsokana tace,

"kazo Hajiya tana kiranka "

dariya kawai yaimata tare da janta zuwa jikinsa yashiga kissing dinta da sauri tazame jikinta ta fito daga dakin kan doguwar kujera ta samu ta kwanta tare da sauke, numfashi,da sauri kamal yabar dakin ,batare da kowa yaganshi ba,kai tsaye dakin abban su ya nufa ,sallama yayi ,aka amsa ,sannan yasa kai ya shiga,kusa da abban yakarasa yazauna,tare da gaisheshi,sannan ya juya gurin su Hajiya da mama suma ya gaida su,ana haka sai ga yayansa shareef shima ya shigo,nan suka hadu sukaita hira can kamal yadago da kansa tare da narkar da fuska yadubi mahaifin nasa,yace,

"Abba, dan girman Allah yau zantafi da sakeena ,tunda tadan sami sauki"

Hajiya ce tai caraf tace,

"kamalu wani ne yafadamaka tasami sauki ko kuma shiga kayi kaganta"?

shiru yayi bece mata kala ba ,sai sosa kai da yakeyi,dubansa ta kuma yi akaro na biyu tace,

"To,bainda zaka tafi daita,ai baka san darajar ta ba,shiyasa kake cutar da ita a *zaman auranku* "

Abba ne ya dubi Hajiyar yace,

"Haba ,Hajiyar lubna,meyasa kike haka ne ,meye amfanin hanashi matarsa,akan wane dalili kikai haka,dama ido kawai na zuba miki,to tun da girma da arziki ki bashi matarsa su tafi"

shareef ne ya gyara zama tare da dubi abban nasu yace,

"wlh Abba kamal yana da matsala gaba daya besan hakkin
*zaman aure* ba,gwanda abar yarinyar nan ta huta ,inbaya ganinta kila yasan amfanin ta"

"Haba sharifi,yazaka fadi haka ,ai ita fitina kwantar daita ake ba dada tayar da ita ba,abashi matar sa kawai,kai kuma kamalu kaji tsoran Allah a *zaman auran* ku kaji"

cewar mama tafada tana kallon kamal abba ne ya katse zancan da duban kamal yace,

"kamalu tashi kaje ka dau matar ka kutafi gida,Allah yakara sauki ka kula da ita kaji ko"

"to ,Abba nagode Allah ya kara girma yaja kwana,mama atayani godiya,
Hajiya muntafi,yaya shareef sai ka fito"

banza Hajiya taimasa ta dauke kanta,
yana gama fadar haka ya fito kai tsaye dakin Hajiyar ya nufa ,sakna na zaune ita da lubna suna kallo,ya shigo hade rai yayi ya dubi sakna ya ce ,

"oya,sakeena hado kayanki zamu wuce"

da sauri ta dago da kanta tadubeshi,lubna ce tai caraf tace,

"yaya kamal Hajiya fa tace kar ka tafi daita kabari tadada samun sauki"

cikin fushi hade da murtike fuska ya nufi kan lubna,

*Jameel*

~~Jameel yadade zaune yana jiran karasowar usman can wayar sa ta hau ruri da sauri yasa hannu ya dauka yana dubawa yaga usman dinne dannawa yayi tare da kara wayar a kunnan sa ,

"usman ka karaso kenan"

"eh gani a kofar gida"

"ok"

kawai yace,yafita acikin mota ya tarar da shi ,jikin motar ya karasa tare da kwankwasa glass din ,cikin sauri usman yafito,murmushi suka sakarwa junansu,tare da rungume juna kai tsaye gidan suka nufa,a parlor suka yada zango jameel ya dubi usman yace,

"Abokina ka ganka kuwa,gaskiya ka kama kasa,meye labari ne"?

"jameel kenan wace kasa ,kawai de ina samin kulawa ne daga gurin madam,yanaji gidanka shiru ko madam bata nan ne"?

shiru jameel yayi can ya nisa yace,

"kai amma mutumina kayi saa gaskiya ,ai ni lamarin baacewa komai sai de addua kawai"

"banfahimci zancanka ba abokina meke faruwa"

shiru jameel yayi can yadubi usman ya kwashe komai game da yanayin *zaman auransu* yafada masa har aikin da yarasa a dalilin matar tasa ,usman ya tausaya masa sosai can yadago ya dubi abokin nasa yace,

"Amma banjin dadin zancan nan ba jameel to ,yanzu wane aikin kakeyi"?

"Haba usman ina maganar aiki ,bana komai fa yanzu ai kai de lamarin baa cewa komai kawai"

dubansa usman yayi yace,

"tohm shikenan abokina yanzu abinda nake ganin zaayi shine,

"kakawo takardunka inkaiwa yayana dan ya bude sabon kamfani dama ana ta daukar maaikata "

cikin farin ciki jameel ya mikawa usman takardunsa
yace,

"kasan kuwa neman aiki zantafi,kai amma naji dadi gaskiya abokina"

"bakomai jameel ai ana tare,yanzu abinda zaayi shine gaskiya ka nemi mata ka aura,dan zaman ka haka ba zeyuba"

arazane jameel ya dubi usman yace,

"dan Allah usman mubar wannan maganar ni wallahi tsoran mata nakeji"

"haba jameel ai ba duka suka raro suka zama daya ba dan haka mubar maganar na dan Allah"

bayadda usman ya iya,kyale shi yayi karshe yai masa sallama ya tafi ,

labiba kam kawarta mero tana daga wayar tace,

"Kawata,kina ina akwai matsala,jameel ya sakeni dan Allah kizo"

"subahanallah ,kai amma abu be dadiba yanzu kina ina kawata"?

"Aa,ina gida mana kizo kifadamin yadda zanyi kinde san irin son danakewa jameel ko"?

"gaskiya ne ,sai dai bana gari labiba,amma na kusa dawowa,innadawo zanzo"

dan haushi labiba ko amsa bata bawa mero ba ta kashe wayar komawa tayi ta kwanta cikinta ta shafa ta lumshe ido,

*Abdulmalik*

~~Da sauri likitan ya nufi inda Abdulmalik suke ,daukar sa sukayi suka daura shi kan gado nan likitan ya shiga duba shi tare da yimasa gwajin jini take ya gano yadda jininsa yai masifar hawa mai da dubansa yayi ga mansur yace,

"Gaskiya jininsa ya hau sosai,kuma hakan zai iya haddasa masa mutuwar barin jiki domin yana da damuwa ,sosai "

cikin tashin hankali mansir yadubi likitan yace,

"Tabbas yana da damuwa sai dai bansan damuwar sa ba,dan befadaminba ,yanzu likita meye abunyi?

"eh to dole zamu bashi gado dan sai ankwantar dashi anabashi agajin gaggawa yanzu naimasa allurar bacci ,zaamaida shi dakin dayakamata ya kwanta"

"Tohm shikenan Dr nagode sosai"

haka kuwa akai aka bawa Abdulmalik gado ,yanata bacci mansir yana zaune yazuba masa ido can tafara motsi ahankali yana kiran Ruhaima ,

inna kuwa tana can bata san halin da danta yake cikiba,duban babar mariya tayi tace,

"Haba kawata ai yanzu haka ma daga gidan su matar tasa nake nakai mata takardar saki ,ai sunrabu ,bata da hali fa yarinyar nan wlh cutar yaron nan takeyi gashi ba haihuwa take ba,saboda haka nan kusa nakeson ayi komai agama"

"Aa to ai shikenan bakomai nabashi auran mariya bari yayan ta yazo zanfada masa"

"yauwa to madalla nagode ,bari intafi sai kinjini agaidamin da yar tawa"

tana gama dada tai gaba kai tsaye gida ta nufa tana zuwa tasa mukulli tashiga dakin Abdulmalik a rufe ,hankalinta be tashi ba sai da taga dare yayi bedawo ba nan ta shiga nemansa Rabia taiwa waya tana kuka ta fada mata,

Ruhaima kuwa hawaye kawai take abban tane ya tambayi ummanta yace,
Chapter 18 · 0% Book details