← Book details Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 25

Sashe 19

Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wai mekuma yafaru naganku kunyi cirko cirko"

takardar kawai umma ta mika masa yasa hannu ya karba tare da war ware takarda ya duba shiru yayi can yanisa yace,

"Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi kinji Ruhaima tashi ki koma ciki kar kisa damuwa aranki "

bata iya amsawa ba ta mike tanufi daki tana share hawaye,

*Hafeez*

~~indomie yadafa yafito kenan yaji bugun kofar ajiye plate din indomie din yayi yanufi kofar tamba yayi

"waye ne?

"inka bude kagani"

dariya yayi mai sauti da yaji muryar ashanty cikin sauri yabude tare da jan hannunta suka nufi ciki,dubansa tayi tace,

"Hafeezu kana cikin hankalinka kuwa matarka fa"

"karki damu daita mukarasa ciki"

atare suka jera suka nufi parlorn tana shiga tadau plate din indomie din tashiga ci ,cokali ya dakko yazo yasa suka shiga ci tare,can tadago ta dube shi tace,

"meye dalilin nemana har gidanka?

janta yayi zuwa jikinsa can ya dubeta,

Areefa,kuwa,karya da gaskiya tashiga fadawa ma haifiyar Hafeez ,ranta ne yabaci tashiga fada kamar yana gabanta wayar ta tadakko ta shiga neman layin Hafeez tana ta ringing be daga ba dubanta tayi tace,

"yanzu yana gida"?

"Eh yana gida"

"madalla tashi mutafi gidan naku zancan banza da wofi kai"

*NASEEBA I UBA*✍🏻
[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:13AM,2017]

*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦

*💦N I G💦*

*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA💐

*Allahumma la sahala illa majaaltahu sahala waanta tajaalul haznah iza shiitu sahala*👏🏻👏🏻

*32*

~~Dada tsurawa Hajiyar ido kamal yayi,dan sauraran abinda zai fito daga bakinta cikin nutsuwa Hajiyar tace masa,

"sai katashi kutafi ai,kuma wallahi tallahi kaji de narantse inka kuma kuntatawa sakeena banyafe maka ba,matarka yarinyar kirki amma katsaya kana shashancin banza da wofi"

sumar kansa yashafa tare da narke fuska yace,

"Hajiya dan Allah kidena fadin haka ,nifa baabinda nake mata kitambayeta ma kiji"

"matsalar kace kuma ai kamal, baabinda zan tambayeta ni kam,sakeena tashi kidakko mayafinki kutafi kinji Allah yakara lafiya"

"Ameen Hajiya Nagode Allah yakara girma "

"Ameen bakomai kede nafadamiki duk abinda yaimiki karki shiru da bakinki kiyimin waya kifadamin kinji"

murmushi kawai sakeena tayi ,ta nufi daki tadakko mayafinta,lubna ce tai sallama ta shigo dakin tana ganin sakeena da mayafi tace,

"Hajiya wai dagaske Aunty Sakeena tafiya zatai,nide gaskiya karta tafi yanzu"

wani mugun kallo Kamal ya watsa mata tare da fadin,

"To,uwarmu bazata tafi yanzu ba,sai sanda kika sa mana lokaci,wallahi lubna kishiga hankalinki dani ,inbahaka ba wallahi wataran sai na lakada miki dukan tsiya ,shegiya mai siffar munafukai"

cikin fushi Hajiya tadaka masa tsawa tare da fadin,

"kamalu wallahi kafita a idona inrufe,yar tawa ce,mai siffar munafukai,to ka kasheta inkatashi yimata hukuncin kaji ko,tashi kabani guri,mai zafin ran tsiya"

tashi yayi yadau wayarsa da mukullin motar sa yafita ,sakeena taiwa Hajiya sallama tare da godiya ,lubna ce ta daukar mata akwatinta,tarakata dakin Maman su saif taimata sallama tare dayimata godiya itama,har bakin mota suka rakata ,kamal sai aunawa lubna harara yake ,yaja motarsa suka nufi gida,

tunda takoma ya gyara halayansa shiyake mata komai kan yafita,yanzu haka kwance take kan doguwar kujera ga cikinta da yakara girma sai juya kai take saboda yadda ta tashi jikinta badadi,shikam yana kitchen yana soya mata kwai sai jinta yayi tasaki kara da sauri yafito daga kitchen din daga shi sai vest da gajeran wando,yakaraso kusa da ita ya zauna,tare da janta jikinsa yashiga tambayar ta,

"matar kamal ,menene,meyasameki?

shagwabe fuska tayi tare da dada narkewa a jikinsa tace,

"Honey bee,wallahi kayiwa babyn ka magana tun danatashi yau sai naushi na yake,nide wallahi banso"

tanagama fadar hakan tasa masa kuka,shi sai yarasa ma mezaice mata saboda yadda tabashi dariya ,rigar ta ya yaye,tare da shafa cikin nata, yana kallon yadda babyn yake ta wutsil wutsil,wata karar tasaki,cikin dariya yace,

"Babyn kamal dan Allah kabari bakasan maman ka bataso ba,kukafa takeyi ,kazauna kawai kaji"

dariya yabata yadda ya dage yanaiwa dan cikinta magana can tadaga kansa daga cikin nata tadubeshi tace,

"Honeybee,may be fa babyn nan yunwa yakeji ,shiyasa yake ta motsi ko?"

dariya yayi saboda yadda tai maganar kamar ba ita ke kuka ba,yace,

"bari inkawo miki wainar ki kici, ko babyn kamal yazauna lafiya"

"Honey beey nifa baby girl zan haifa,gaskiya"

Da sauri ya jiyo yazuba mata dararan idanunsa ,masu bata tsoro wani lokacin tare da yadda ya hade rai,

*Jameel*

~~jameel yana kashe wayar sa yadada jan dogon tsaki ,kwanciya yayi kan doguwar kujera yashiga tunanin yadda zaisami macen arziki yaaura dan shikansa yasan zaman sa haka bashi da amfani yana mutukar bukatar mace,wayarsa ya dakko yashiga neman layin abokinsa usman bugu biyu ya dauka,

"Hello Abokina ,kana lafiya"

"lafiya kalau usman ya madam,da yarana na"

"Duk suna lafiya"

"kana ina ne yanzu,inason ganinka yanzu"

"ok badamuwa ina gida zaka iya zuwa"

"Tohm shikenan usman gani nan zuwa"

sallama sukayi ,mikewa jameel yayi ya nufi bedroom dinsa ya shirya tsaf yafito kai tsaye gidan usman ya nufa ,be dau dogon lokaci ba yakarasa gidan nasa ,kiransa ya kuma yi awaya ,tare da shaida masa gashi yakaraso,bejimaba yafito ,hannu suka bawa juna suka gaisa tare da karasawa ciki,a parlor suka zauna jameel ya gaisa da Huda matar usman tunda yashiga yai tozali da wata kyakyawar yarinya ido yazuba mata har sai da yarinyar ta tsargu daga kallon da yake mata dago da kanta tayi ,atare suka hada ido,murmushi yasakar mata,

labiba kam suna isa asibiti aka shiga daita labour room nan da nan likitoci suka rufu akanta take suka gano yadda jininta yai masifar hawa,nan suka shiga ceto rayuwar ta, data babyn ga azabar ciwo gabadaya tafita a hayyacinta sunan jameel kawai take iya kira ,cikin kankanin lokaci tafita hayyacinta kamar wasa tafara jijjiga,hankalin momy yai masifar tashi,da kyar akasamu ta dena jijigar cikin ikon Allah ta haihu amma babyn yarasu saboda wahalar da yasha,momy sai kuka takeyi wayar jameel tashiga kira tanata ringing yaki dagawa,labiba kam tanacan ankaita dakin duhu wato dakin daake kai masu jijjiga,kiran Abban jalila momy tayi bugu daya yadaga cikin kuka tashiga fadamasa gasu asibiti ,hankalinsa ne yaimasifar tashi wata nurse ce tafito cikin tashin hankali ta nufi momy,dada gigicewa momy tadada yi,tare da zubawa nurse din ido,danjin mekuma zatace mata,

*Abdulmalik*

~~cikin kankanin lokaci Rabia takaraso asibitin bata sha wahala ba wajen samun dakin da Abdulmalik yake,shigarta keda wuya tayi tozali da kanin nata kwance,mansir yanata fama dashi yaci abinci yaki ,

"Dan Allah mansir kabarni Ruhaima nake jira tazo tabani abincin"

shiru mansir yayi ganin Rabia tashigo da sauri takarasa gaban gadon da yake,tashiga yimasa sannu tare da kwantar masa da hankali,cikin muryar rarrashi tace,

"Abdul kaci abinci tukunna sai inkira maka Ruhaima "

shiru yayi tare da zuba mata jajayan idanunsa ,can ya miko hannu yakarbi ruwan tea yafara kurba,mansir ne yadubi Rabia yace,

"Aunty wai meye musabbabin ciwon Abdulmalik ne?

shiru tayi tare da kallon Abdulmalik din tace,

"Au befada maka ba?

da sauri Abdul malik yatare ta da fadin,

"Dan Allah kubar maganar nan haka innayi bacci kya fada masa"

yanagama fadar haka yashiga share hawaye,

yana gama shan tea din Yaya Rabia takira masa Ruhaima tana daga wa ta mika masa wayar dasauri yafara magana,

"Hello Ruhaima ! Ruhaima!"

shiru taimasa sai faman kuka takeyi cikin rawar murya yace,

"pls stop crying,say something to me"

cikin tsananin tashin hankali tashiga rera kuka tare da fadin

"Abdul malik dan Allah kabarni kadena kirana kana fama min raunikan da suke cikin zuciyata na shiga uku"

kuka tasa masa gaba daya kasa magana yayi saboda tsananin tashin hankali dif yaji takashe wayar kansa ya kife akan filo yasaki kuka kamar mace,take kansa yadada sarawa yasaki wata kara ya sulale,cikin tsananin tashin hankali Rabia da Mansir suka fita dan kiran likita,

inna kuwa tanacan tarabka uban tagumi tana tajiran Rabia ta kirata tafada mata inda Abdulmalik yake,tun tana sa ran jin wayar ta har ta hakura karshe ta yanke shawarar daukar mayafi tanufi gidanta ,

*Hafeez*

~~Hafeez yanacan sun lula duniyar shedanci shi da Ashanty ,acikin gidan auransa agadonsu na sunna waiyazu billahi *Naseeba tace* *wannan wane irin zaman aure kenan Allah katsare mu*

wayarsa tana parlor tanata faman ringing besaniba ,sai da suka gama shedancin su sannan tafito parlor hannu yasa yadauki wayar yana dubawa yai tozali da missed calls din maman sa dana yayar sa da sauri yabi kiran tanashiga maman tasu tadaga tare da fadin,

"sannu Hafeezu ,sai yanzu kaga damar daukar wayar yayi kyau to gamu akofar gidanka inkaga dama kazo ka bude mana"

hantar cikinsa ce tabada kulu lulu ya maida dubansa ga Ashanty wacce tafito daga ita sai towel,takarasa ta kwantar da kanta agadon bayansa zagayo daita yayi tare da zuba mata ido,

Areefa kam gabadaya hankalinta ne taji yai masifar tashi gabanta sai faman daduwa yake haka kawai tarasa dalilin faruwar hakan,

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [7:24AM,2017]

*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦

*💦N I G*💦

*ZAMAN AURE*

*NA*

NASEEBA I UBA💐

*lahaula wala kuwata illa billahil aliyul azim tawakaltu alal lah wala haula wala kuwata*
*subahanalla wabihamdihi subahanal azim*👏🏻👏🏻

*31*

~~Da gudu lubna ta nufi daki tare da banko kofa,tsaki kamal yaja tare da fadin ,

"mara kunyar karya meyasa kika gudu ai da sai ki tsaya,wlh da sai na karya miki kafa shegiya"

sakeena de tana zaune tana kallonsa mai da duban sa yayi ga matar tasa yakarasa kusa da ita ya zauna tare da kama hannuta yahada danasa yace,

"matar kamal muwuce gida ko?"

shiru tayi tare da narai narai da ido ,dorawa yayi da fadin ,

"karki damu sakeena ina nufin karkiji komai inshaallah zamu shinfida rayuwar aure mai cike da so da kauna, zan canja tsarin *zaman aurenmmu* kinji,haka kuma nadena duk wasu muna nan dabiu danakeyi tunda kince ba kyau ko"?

ahankali ta dago ta dubeshe zatai magana kenan sukajiyo muryar Hajiya da sauri kamal ya matsa daga kusa da sakeena ,karasowa Hajiya tayi ,tare da samun guri ta zauna ,ahankali kamal yadago da kansa ya kalleta dada hade rai tayi ,tace

"kamalu burinka yacika kafadawa Alhaji zakatafi da matarka ko,to yayi kyau katashi kaje gurin aikinka in kadawo kabiyu ka dauketa dan bazaka kaita gida ba, katafi kabarta ita kadai bazai yu ba"

da sauri yatari Hajiyar tasa da fadin,

"Hajiya ai bazanje aiki ba a gida zan zauna inkula da ita"
Chapter 19 · 0% Book details