← Book details Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 25

Sashe 3

Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" kafiya jan magana wlh jameel taya zan iya tsefe kai na kai zaka tsafan to, kagama girkin sai muyi tsifar "

" yes, ma"

Yanagama fada ya nufi hanyar dakin sa sai gashi ya fito daga shi sai vest da gajeran wando tana kwance murmushi ya sakar mata ya shiga kitchen indomie ya dora cikin kankanin lokaci ya kammala ya zubo musu a plate ya kawo da kyar ta sakko ta fara ci sai shagwaba take wai tagaji kwantar da murya yafara yi yace

"haba everlasting ki daure kici sai ayi tsifar sai muyi wanka in gasa miki jikinki da ruwan dumi "

" jameel, dawa zakai wankan kar kace dani cab Allah ya sawake to wa zai min wankin undies dina ko salon mu tsaya wanka na batawa kaina lokaci"

"Hmmm shikenan everlasting badamuwa sai in zauna kije ki dawo "

" better"

Tsefemata Kan yayi tashiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya mukulin motar yabata ta fita guri yasamu ya zauna ya dafe kansa yashiga tunanin irin bakar rayuwar da ya tsinci kansa ciki

Abangaran abdulmik kuwa gaba daya hankalin sa ya bawa inna dan jin wane irin sharadi zata furta duban sa tayi tace

"Abdulmik so nake a dinga kawo min amincin gidan ka tun daga na safe har na dare "

" inna abincin gidana kuma?

"baze samu bane, a hakura "

" aa inna, ina ganin de kamar dan aike ne zai zama matsala "

" oh! meye amfanin kudinka malik, ai tunda kana kana da kudi dan aike zaa samo, sai kasai masa babur kana biyan sa duk wata"

Shiru yayi yana jin jina kalaman innar tasa can ya nisa yace

"shikenan inna badamuwa inshaallah zaai yadda kika ce"

"yauwa saura kuma yar mulkin tayi son ranta dan bazata so hakan ba tafiso daga ita sai yanuwanta Hmmm naso ace kana da kanne, wlh da taga yadda *kannan miji* zasuyi ko da yake ai ko basu akwai *uwar miji* "

Shiru yayi mata takaraci surutun ta kudi ya ajiye mata a gabanta karshe yaimata sallama yatafi tana ta sama sa albarka wani shuumin murmushi inna tayi

Kai tsaye abdulmik gidan su ruhaima ya wuce lokacin tana tare da ummanta da kannan ta dasuka zagaye ta sai wasa da dariya suke ummanta ce ta dube ta tace

"ruhaima dafatan kuna nan lpy ko "?

" lpy kalau umma sai dai matsalar innar sa kawai"

"bakomai ruhaima ke de kicigaba da yaimata biyayya kamar yadda zaki min ban yarda ki saba mata "

" shikenan umma inshaallah zan kula "

Sallamar abdulmik ce ta katse musu zancan da suke yi da faraa umma ta tari abdulmik suka gaisa cikin mutun tawa sukai mata sallama suka tafi tun a hanya abdulmik yarasa yadda zaiyi ya fada mata bukatar inna ahaka har suka isa gida sai da suka zo bacci sun kwanta yajata jikin sa sannan yafada mata Shiru ruhaima tayi can ta janye daga jikin ta daga nasa tace

Abangaran hafeez kuwa sai da ya bari kiran areefa ya katse sannan ya tashi ya fita cikin motar sa ya shiga sannan ya kira ta bugu 2 ta dauka cikin shagwaba tafara magana

"Hello yallabai, katafi kabarni da kewa ni de gsky kadawo "

" sarka mai rikicin gan gan, to indawo me zan miki, me kike so daga gurin hafeez, fadan inji "

Dariya tayi sannan tace," sai kace ka manta areefa ko, to bari in tuna maka areefa bazata iya rayuwa batare da hafeez ba ayanzu haka ina kwance sai juyi nake nakasa bacci wlh "

" ayya muyi daya sweet hert nima nakasa baccin, amma abinda zaai yanzu ki rufe idon ki zan ta fada miki kalamai masu dadin sauraro da kwantar da hankali har kiyi bacci "

Dariya tayi, tayi yadda yace nan ya shiga jero mata kalamai masu dadi akarshe ya juya zancan zuwa na tada hankali da shaawa areefa rasa yadda zatayi tayi saboda yadda taji kewar mijin nata ta dawo mata sabuwa karshe yai mata sallama ya kashe wayar Shiru tayi karshe ta yanke shawarar kiran saurayin data yi a school

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[3/19, 10:27] ‪+234 814 620 5819‬: [5:54Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

*ZAMAN AURE*
💦 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦

*NA*

NASEEBA I UBA 💐

*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*📿👏🏻

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦

💦💦
*Wannan shafin nakine kawata fayeex usman hakika kin cancanci yabo bisa namijin kokarin da kikai wajen kawo mana novel dinki mai suna hanyar yaman mun waazantu kuma munnishadantu Allah ya kara basira kina yi munjin dadi sai munji ki a sabon novel dinki naseeba tace ana ana tare*🤝💦💦

*5*

~~~ganin maman su kamal ne ita da lubna kanwar sa ne ya sa sakna sakin murmushi ta karasa gurin su hade da rungume lubna dubansu tayi tai musu sannu da zuwa mama ce ta amsa da

"yauwa sakeena sannu kinji dafatan kuna nan lpy ko "

Tsuguna wa sakna tayi ta gaida mama cikin girma ma wa ta amsa da kulawa duban lubna sakna tayi tace

" gsky lubna nayi fushi sai yau ko kullum cikin zuba idon ganin ki nake sai yau kika biyo mama "

Dariya lubna tayi sannan ta dubi mama tace

" mama dan Allah ai kullum ina son zuwa ko wlh aunty sakna makaranta, amma kisha kuruminki kwana 2 zanmiki "

Cikin jin dadi sakna ta dubi lubna tace

" kai amma naji dadi sosai kice yau ina da babbar bakuwa, mama yasu aunty da su suhaif "

" kowa lpy kalau sakeena ya kamal din dafatan dai kuna lpy ba wata matsala ko "

Cikin ran sakna matsala ce fal hade da damuwa amma bazata iya bayyana sirrin su ga wani ba dan *mijin ta sirrin tane* afili ko sai tace wa mama

" Aa, mama ba wata matsala muna zaune lpy "

" To Alhmdulillah ayi ta hakuri kinji ita rayuwar auri da kike ganin ta hakuri ake yi da juna, amma hakan bazai sa in daya ya cutar da daya akasa daukan mataki ba duk abinda kamal yai miki ba dai dai ba nabaki dama ki fadamin kinji yata "

" Hmmm to, mama nagode Allah yakara girma "

Tashi tayi ta je ta kawo musu danbun nama da ruwa da lemo da kyar mama ta dan ci kadan tai musu sallama ta tafi sabulai sakna ta dakko ta bawa inna nan suka zauna ita da lubna sukai ta hira

Da yamma sukai girkin su tare har bayan magariba lubna bata ga kamal ya dawo ba duban sakna tayi tace

"Aunty wai yaya fa, dama baya dawo wa da wuri ne?

Shiru tayi saboda bata san amsar da zata bata ba can ta nisa tace

"eh to, yadanganta da yanayin uzurin sa a ranar lubna "

" Au wlh nazaci baya dawo wa da wuri ne infadawa Mama "

Dariya kawai tayi nan suka ci abinci suka taba hirar su hamma lubna tafara yi duban ta sakna tayi tace

" Bacci ko,? taso muje ki kwanta "

Tashi lubna tayi suka nufi bedroom ta kwanta duban ta sakna tayi tace

" Haba, lubna yazaki kwanta ba tare da kinyi alwala ba "

" kai Aunty wlh bacci nake ji dan Allah ki barni "

Da kyar sakna ta lallaba ta ta yi alwala sannan ta zo ta kwanta parlor ta koma ta sa plate din Quraani tanaji wayar ta ta dauka ta shiga neman layin kamal tana ta ringing be dauka ba ahaka bacci baro yai gaba da ita

Kamar kullum kamal be dawo ba sai wajen 12:30 na dare abige ya shigo yana ta surutai tozali yayi da sakna tana kwance a Kan kujera tana bacci kawai sai jin mutum tayi ya fado kanta wata kara tasaki wacce ta gigita lubna da ke kwance a daki hannu yasa ya toshe mata baki sai kuma ya shiga kwarara amai ba kakkautawa ahaka lubna ta.

Abangaran labiba kuwa tana fita kai tsaye gidan su ashanty ta nufa tana shiga tayi tozali da kawar tata suka rungume juna cikin so da kauna duban ta ashanty ta dubi labiba tace

"kai kawata kingan ki kuwa gsky kina balai jameel ya tsaya miki wlh "

" cab jameel ya tsaya min ko na tsaya wa kaina sai kace kin manta halin jameel Hmmm yanzu dai kawata aikin malam yayi kyau ko ince yana kyau dan sai yadda nayi dashi dan yanzu haka yana gida nabar shi da wanki da girki "

" kai kawata baki da kyau wlh mijin ki ne fa "

" ashanty kenan sai kace baki san halin
maza ba, ko mai mace tai musu su suka janyo saboda in suka sami dama sai su maida mace tamkartamkar baiwar da suka sa kudi suka siyo, to wlh ni labiba ban yarda wani da namiji ya dan dana min bacin rai ba "

" Da kyau kawata, to yanzu ki shiryo akwai wani sabon malami daaka bani labari zan raka ki wajen sa "

" Allah, Ashanty to zamuje gobe gobe nan "

Nan dai sukai ta kulla mugun nufin su akan bawan Allah karshe sukai sallama labiba ta tafi kai tsaye gurin salon ta wuce

Jameel kuwa tun bayan fitar labiba ya hada under wears dinsu ya wanke tas ya wanke toilet din bayan yagama tsaf ya nufi kitchen girki ya dora musu yana yi yana share gumi ahaka ya kammala ya zuba a kuloli, wanka yayi ya dora alwala har zai fita masallaci labiba ta shigo da mota tsayawa yayi ta shigo ya mai da gate din ya rufe ahannu yasa ya bude mata murfin motar ta fito jakar ta ta mika masa yadanyi jum kafe shi tayi da ido take jikin sa yafara rawa a hankali ya ce.

Abangaran gidan Abdul malik kuwa jan ruhaima yayi jikin sa yashafi fuskar ta yace

"my dear dan allah kiyi hakuri da abinda zance "

" ina jinka malik fadi abinda kake son fada ruhaima me biyayya ce agareka"

"to godiya nake dear, ammm, dan Allah zaa dinga kai wa inna abinci tun daga na safe har na dare dafatan zaki bani goyon baya wajen kyauta ta mata "

Shiru tayi kamar bazata amsa ba can kuma ta nisa tace
Chapter 3 · 0% Book details