Sashe 5
The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murda handle din kofan tayi ta shiga cikin dakin inda ta hango ta tana zaune bisa sofa dake dakin da alama tayi zurfi cikin tunanin da take yi, cike da kissa tayi wani murmushin munafurci sannan ta karasa inda take tasa hannunta a shoulder dinta wanda yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula, kara marairaice face nata tayi tace "Adda Fati kema kina tunanin abinda nakeyi ko," cikin rashin fahimtan abinda take nufi tace "mai kenan", dan cuno baki tayi gaba tace "come on Adda don't pretend kidena acting as if like bakisan abinda nake nufi ba, after all kin san komai", dan hade fuska tayi tace "nifa bana son shirme kiyi magana yadda zan gane kidena mun shiga da futa", marairaice face nata tayi sai tazama abin tausayi, tace "game da twins din nan nake magana nasan kema bawai kin yadda dasu bane musamman yadda inkika kula suke kama da little da ita kanta Islam din ma kamar yayi yawa ni dana gansu har na fara jin shakku," cike da zakuwa da son kin gasgata abinda yar uwar nata ke kokarin fada tace " shakku akan mai," itako ganin yadda Addan nata ta dan rude ne ta kuma kafeta da ido, yasa tayi saurin sadda kanta kasa tana wani culprit din smile a heart nata, "yi hakuri Adda naga kaman ranki ya baci ni bari ma naje nayi abinda aka aiko ni, dama Innani ne tace nazo na diba mata kayanta ita da sabin jikokin nata data samu daga gurin sirkinta, ban san ma mai tagani ajikinsu ba wanda yasa sukafi Islam mutunci agunta ko dan ma ba abin mamaki bane yadda naga wannan mahaifiiyar tasu ba abin mamaki bane in hakan ta faru," tana maganan ne cike dason tunzura yar uwar tata bata yi kuskuren data bari suka hada ido ba, sai de tana satan kallonta da kuma fahimtar irin yanayin data shiga wanda da alama hakan ta ya cinma ruwa, ta cigaba dayin aikin daya kawo ta yayin da take cusa mata zancen da tasan tabbas zasuyi tasiri a zuciyar duk macen data cika mace mai kishin mijinta da aurenta, wanda sai ka kai zuciyar ka nesa kafin ka kubutar da kanka daga halaka cikin stawa tace "ya isa wai mai kike nufi ne", murmushin nasara tayi a heart nata kafin ta karaso inda take hannunta dauke da basket da jakan kaya ta dire su agaban yar uwarta tace "abu biyu nake nufi anan, na farko mahaifiyarki ta fifita wassu bare akanki wanda bata san asalinsu ba, ta tafi ta barki alokacin da kike bukatanta, haka danki ya kaurace miki ya tafi gun 'ya'yan da baa san daga ina suke ba, abin dubawa anan shine mai zaisa little yin hakan?? aganina ba komai bane ke jansa sai jini, ina nufin jinin dasuka hada da yaran," ba shiri ta dago manyan idonta ta zubasu akan Zainab, da ta cigaba da zuba zance "ehh abinda nake nufi kenan yaran jinin Faruq ne shiyasa jikinsa ke rawa akansu, sanin kanki ne Faruq baya shiga harkan yayan mutane amma yaran nan ko ina aka kaisu yana bayansu sabida mahaifi daya garesu kuma shine mahifin Faruq k.......," hannu ta daga mata tace" ya isa Zainab bana son maganan banza, ni ba sa'ar ki bane da zakina fada mun duk zancen da kika ga dama hak mijina ba abokin wasan ki bane, da umma ta tafi gunsu ai ba kina tayi ba su sun fini bukatar taimakon ayanzu shiyasa, in Faruq yaso yaran to wannan ra'ayinsa ne", . murmushi Zainab tayi tace" Adda kenan shiyasa kullum ake cutarki sabida kin fiye tausayi da yawa, asibitin nan acike yake da masu aiki mai yasa ba'a umarcesu dasu kula dasu ba, ita umman Dr ne,?? kuma shi mijin naki mai ya hanashi zuwa ya duba ki in yana da gaskiya, ina tun kafin ayi suna dayazo bai kara zuwa ba, kuma ai yasan baki da lafiya naga tun cikin ki yana wata 5 ya dawo dake nan rugar, to shi waliyyi ne da zai zauna ba mace har na stawon wata hudu, shi yasan abinda yakeyi kuma ba komai bane sai barikanci anan yasa mu yaran nan," tasssssssss kakeji Fatima ta wanke Zainab da marin da sanda taga taurari, sannan ta nuna ta da manuniyar ta "this should be the last time da zaki kara fadin maganan banza akan mijina, if not i will make sure i break every single bone from your body", Zainab dataji marin tamkar saukar aradu ta ka ta gagara ko mastawa daga inda take, .she is suprise cos Addan ta bata taba ko da zungurin taba arayuwarta duk dako irin azaban rashin kunyan datake mata, ko wani bata so taga yana tabata amma yau ita ta mareta da hannunta, "Adda ni kika mara akan wassu kazaman bare da bakisan asalinsu ba, stintattun mage ni Zainab Adda akan na fada miki gaskiya shine kika mun haka akan mutumin da bakisan asalinsa ba shida kwasassun mutanan can," tana magana tana pointing door da index finger dinta stawa ta daka mata tace "get out Zainab ki bace mun daga gani na", stugunawa Zainab tayi ta dauki basket da jakan ta kama hanyan fita sanda ta isa bakin door din ta juyo, tace "wallahi zakiyi dana sanin hakan zakiyi mamakin abinda stintattun magen naki zasuyi," gafff tabude kofa ta fita zaman da ba shiri Fatima tayi dan tabbas zancen Zainab ya soki zuciyanta matuka, taji zafin zancen nata sosai ta kuma kara dagula mata brain, tabbas dabata kai heart nata nesa ba da tayi abinda tasan zatayi dana sani daga baya, tasan bazai taba cutar da ita ba amma ai abin da Zainab ta fada yana kan gaskiya, da wuri tayi kokarin kauda tunanin da ambaton sunan Allah wanda da haka ne ta yaki heart nata afari har ya hanata aikata abinda zatayi dana sani. bata staya ko ina ba sai dakin patient din inda tabar Innani da ta cika tayi famm dan haushi, tun dazun sai jiranta takeyi ga Faruq sun futa da chief bare ta aika shi ya kira ta, tana bude kofa ta fara zazzaga mata bala'i kamar an kunna fanfo " uban mai kika tsaya yi acan din 'kika barnin ina ta jira", shiru tamata kamar bata jita ba hasala Innani ta karayi tace "dan uban ki ba magana nake miki ba kinmun shiru", zumburo baki gaba tayi tace "to ni mai kike so ince miki" "eyyehhh lallale Zainab wuyanki yayi kauri ani kike zumbura baki, ki jira intashi sai naci ubanki dai dai gwargwado, kuma ki wuce ki koma gida ki hada abincin Abbanku da furansa, ki kuma hadawa Faruq kayansa ki bawa bashir driver ya kawo, ki kuma tabbatar kinyi abincin dare da wuri wallahi kika barmu da yunwa irin na jiya zanci ubanki cikin buta," bata ce komai ba tayi ficewarta tabar dakin takama hanyan barin hospital din daniyan komawa gida don yin abinda Innani tasata tana tafiya tana kissima irin abinda zatayiwa wayannan stintattun magen da tun safe ake cimata mutunci akansu tun da safe yau take ta faman shan wiya akansu yau hartana murna Innani zata dawo ta karbi aikinta sai kawai akace sai gobe, ashe duk mastiyatan nan ne suka hana su dawo wa kwafa tayi ta cigaba da tafiyanta har ta isa gida. lokaci yacigaba da tafiya yabar zuciyoyi cike da waswasi Innani bata nuna gajiya warta wajen kula da wayannan yaran ba, wanda ita tausayi ma suke bata haka har dare yayi kamar yadda Faruq ya nace haka ko akayi anan asibitin ya kwana. washe gari Innani da kanta tayi wa jariren wanka suda islam, akasa masu kaya sunyi matukarr kyau da daukan hankali, ta kuma basu madaransu Dr ne ya shigo dakin da marar lafiyan take inda yasamu Innani, chief da fatima harda Faruq adakin, bayan sallaman da yayi aka masa, iso akayi masa ya shigo suka gaisawa yamawa fatima ya jiki' tace " Alhamdulillah yayi sauki gashi har na fito ma", "little imam how are you?, yace" am pretty fine, Dr how about you ?," "am also fine ina Dad dinka, kunyi waya ne," "ehh munyi yace ma yana hanya ya kusa isowa rugar nan, zai zo yaga twins din mu ai nabashi labarin su," murmushi dr yayi ya shafa kan shi sannan ya karasa gaban gadon patient din ya dubata sannan ya juyo ya fuskan cesu with full of hope, Innani tace " ya jikin nata", yace "Alahamdulillah da sauki zata ma iya tashi nan da good 3 hours nan da wa uku kenan, sai de zata iya tashi a firgice duba da irin yanayin data shiga a fari," "tohhh yayi kyau Allah tashi kafadunta," ameen kowa ya amsa dashi inji chief karasawa yayi gurin babies din yace " mashaallah look at them they are so pretty just like egyptians, kamar larabawa Allah de ya saka da alkairi gaskiya ba karamin kokari kuka yi ba chief da kuka cece su Allah saka muku da jannatul firdausi," murmushi chief yayi yace "kuma ai kuna kokari sosai Dr, " "ai bamu kai kuba kudin na daban ne, Allah de ya saka muku da alkairi," ameen suka amsa kafin ya fita ya je don duba sauran patient, yabar kowa da abinda ke saka wa a heart nashi baya Fatima da abin duniya ya isheta, . ba abinda ya kara daga mata hankali sai ganin matar datayi ganin irin zillan kyan da Allah ya mata, ga wani kwarjini na musamman da daukan ido da takeyi, in tace bata storata ba tayi karya maganan zainab ne ya fara dawo mata karde ita ne dako ita ne data shiga uku, tasan karshen zamanta da mijinta ne yazo muddin ya kasan ce abinda take storo ne, tohh tagama aiki ajiyan zuciya tasauke, numfashinta har wani hardewa yakeyi, jin an dafa kafadarta tane yasa tayi saurin daga idonta taga Abbanta dake gefenta fuskarshi dauke da smile, yace "babu abinda zai faru sai alkairi," itama murmushin ta kakalo ta mishi bata ce komai ba. wata hadadiyar car ce mai numfashi da keta hazo, ta keto cikin wannan rugar, a back seat wani kyakkyawan halitta ne ke zaune yana sanye da Ralph Lauren brown suit da yayi masifar amsar jikinsa akalla zai kai 35years, sai de sam shekarun