← Book details The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 33

Sashe 17

The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NIGERIA [ RUGAR HARDO BELLO] Washe gari kamar kullum munyi asubanci dan shirin tafiya school mun shirya cikin atamfa yau mun fito a asalin hausawa sabanin dressing din da muka sabayi na larabawa k'asashen ketare, atamfaar ta amsa jikin mu riga ce doguwa fitted gown wanda yabi lafiyar kyakkyawan surar mu, colour combinatoin din ko ya amsa jikin mu. kamar kullum mun gaisa dasu ummi a waya muna shirin zuwa don mu gyada su Jaddi. yau na tashi da wani irin yanayi wadda ni kaina na gagara misaltawa kuma na tabbata yana da nasaba da mafarkin danayi yau ya mugun storata ni sosai, mafaraki nayi da wata mata na yin stafi tana kiran sunan wani wanda na gagara rikewa tana stakiyan wassu mutane masu jajayen kaya da baki gabanta da wani kurciya wanda ta daura masa wani laya, ta kuma wulla shi daniyan ya tashi ta cigaba da ambatan sunan tana cewa "kayi nesa da gida karka dawo kayi nisa ka shiga duniya," bayan da ta gama ne ta sake kurciyan ya tashi sama, a nawa bangaren kuma na fara binshi don na kama shi sai de yayi nisa, wani dutse na samu na wulla mishi cikin sa'a kuwa ya sameshi ya fara tangal tangal yana kokarin faduwa, da gudu na bishi don ganin inda zai fadi sai de kash kafun na isa na tashi daga baccin arazane sakamakon karan da alarm yayi. Hmmm dogon numfashi naja Islam ne ta dafa shoulder dina tace'' what is wrong with you Sis'' jijjiga mata head nawa nayi nace ba komai ''kin tabbata'' nodding head nawa na karayi for second time ''okay muje mu Jaddi tunda kin'ki fadamun abinda yake damun ki i guess kin samu wata Sister data fini ne'' murmushi nayi don na fahimci ranta ya baci hannunta na kama don ta juya mun baya come on Sis na isa ke kadai nakeda kema kinsan haka ''uhmm ni de let go of me dama naga this couple days kina shareni bakyason fada mun damuwarki kona tambaya sai kice ba komai '' wafce hannunta tayi da sauri nayi hugging nata am so sorry Sis Allah ba abinda kike tunani bane kawai bana so na dameki ne shiyasa, breaking hug din tayi ta juyo tayi facing dina holding both hands nawa tayi da nata very soft hand din direct eye contact mukayi da ita which means munyi 4 eyes da ita '' damuwarki nawa ne nida ke abu daya ne we are Sisters remember, munyi alkawarin duk rinsti duk wuya we will be together and we would always stay by each others side because we are Sisters and nothing would change that'' hmmm i remember Sis ba abinda zai rabamu Insha'Allah '' now tell me what is wrong with you'' hmmmm dogon numfashi naja nace is a long story in mun dawo i will narrate it to you ''kin tabbata'' na tabbata ''okay lets go'' a tare muka fito don zuwa gyada Jaddi wani abu na hango yana dan mosti a karkashin bishiyan dake stakar gidan har kaman zan wuce wani abu yace in koma, ahankali kamar barauniya na fara sanda ina karasa inda abun yake Islam ganin abinda nakeyi tace '' are you okay'' ita sam bata ga abinda nake gani ba ko ince bata kula ba ma, am not sure nayi maganan ayayin da nacigaba da tafiyan har na isa, mai zan gani!!!!!!! kurciya na gani Islam tace "goshh Noor you scared me i thought wani big abu ne ashe wannan karamin halittan ne look it's just a bird, lets go yanzu nasan bai wuce wa ni ne ya buge shi ya fado ba mu tafi ko muyi latti," okay lets go har na juya na kara dawowa na kurawa bird din Lulu eyes nawa ina son gano wani abu game dashi stugunawa nayi kusa dashi na kura masa eyes mai zan ganiiiiii ware Lulu eyes nawa nayi ina kamo hannun Islam shine wallahi Islam shine shine Islam da ta daburce da yanayin nawa tace ''shine what'' the bird from my dream kama kanta tayi tace ''ohh my God Mahnoor what are you saying i dont understand, fairstly which dream are you talking about'' wanda nayi yau da dare na ganshi aciki ''and so dan kin ganshi sai akace wannan shine how comes,?? how could it even be possible from dream to reality '' copping face nawa tayi tace "look at me come down and take a deep breath am very sure everything will be find," hannunta tasa a forehead dina tace "i see now ashe fever ke damunki shiyasa muje Jaddi ya miki tofi,nasan zakiji sauki," fashewa nayi da kuka na hau bbbubaga legs nawa a kasa ni wallahi lfy na kalau ba abinda ya sameni, "okay naji mu tafi lafiyanki kalau" wallahi nikam bazan tafi ba sai na duba bird din nagani,' "hummm tohh naji i gave you just 3min kigama mu tafi," okay da sauri na koma inda bird din yake na stugana akusa dashi bismillah nayi kafun na dauka na kura mata ido na yan sakan'ni, wani abu na gani a daure a kafansa hannu nasa daniyan tabawa Islam ta kama hannun ido ta kura masa na yan lokaci zaaroo ido waje tayi tace " Ohhh my God laya ne Noor ba.. bbbari naje na kira Jaddi don't you there touch it," kai kawai na gyada mata don ganin yadda ta rikice lokaci daya, in less than 2min sai gata sun dawo dasu Jaddi cikin sauri suka iso inda nake Innani ta jawo ni jikinta kamar wadda akace za'a kwace mata n, Chief kuwa stuguna wa yayi bakinsa dauke da bismillah ya dauki kurciyan wassu addu'a yayi kafun ya ware layan daga jikin kafanta ya war'ware wani dan paper ne aciki da wassu rubutu a wargaje abinda kake iya fahimta agun wani suna ne kawai wato "FAHREEN" shine abinda Jaddi ya ambata, cikin rudu na zare large eyeballs nawa bakina na rawa shshshshs.... shine Jaddi shine na mafarkina, ganin yadda na rikice yasa Innani fina rikicewa, Jaddi yace "ya isa Noorul Hudarh ki nustu kimun bayani shine wa " ba bata lokaci na zayyana masa mafarkin danayi jiya, gyada kanshi kawai yayi yace "Biri yayi kama da mutum" muje ciki da tohh muka amsa masa bai ajiye kurciyan ba muka taafi farlonsa mun kai akalla 5min baice damu kala ba hannunsa dauke da kurciyan, addu'a kawai yake tofe ta dashi acan ya umarci Innani data kawo mishi koskon wuta da ashana, ba musu ta kawo paper yasa acikin kwaskon ya kyasata ashana ya kona sa murus, sanda ya gama konewa kafun yayi yaja dogon numfashi yace" Alhamdulillah Nana, " Innani tace "na'am Sheik," "anjima in rana tayi sanyi kisa Jauro ya gyara dakin baki ina stammanin zamuyi manyan baki nan ba da jimawa ba," da tohh ta amsa masa kafun ya fuskanceni yace "ta'al" ba musu nazo inda yake ya zaunar dani agefensa " ki kaddara duk abinda kika ga ya faru dake acikin kwana biyun'nan kaddaranki ne haka ki rungumeshi hannu bibbiyu ki kuma yi addu'a Allah baki ikon cin jarabawanki," kaina akasa batare da na fahimci abinda yake fada nace Insha'Allahu zanyi yadda kace Jaddi, murmushi yayi ya shafa kaina yace " Hafidatiii inaso kisan bawa baya wuce kaddaransa duk abinda Allah ya jarrabi bawansa dashi to tabbas yana da tabbacin zai iya dauka, naki jarrabawan ya ban banta dana mutane amma kicigaba da addu'a Allah zai kawo miki shi da sauki ," wani irin nauyi nake jin zuciyata tayi bani kadai ba kowa dake farlon haka yajin Innani ne tayi karfin halin cewa "mai kake nufi ne Sheik," yaja dogon numfashi yace "abunda muka dade muna boyewa shi yake shirin bayyana lokaci yayi," wani irin dummm kirjin Innani ya bada hakan yana nufin ta kusa rabuwa da shalelenta kenan wannan shine abinda Innani ke mai maitawa aranta. atakaice wannan ranan munyi wunin kurame kowa da abinda ke damunsa jikin kowa yayi sanyi baya ni daban san mai Jaddi ke magana akai ba, zuciyata ta jagule na rasa madogara daya da madafa na rasa wa zai sanar dani abinda ke shirin afkuwa . EGYPT { CAIRO} 9:30 lokacin kowa ya hallara Meeting hall na family din Sultan Abdulmalik, a duk lokacin da zasuyi tattaunawa mai muhimmanci anan ake hallara sunyi mamakin jin cewa yau za'ayi tattaunawa kowa ya zuba ido yana jiran Sultan Muhd Habibullah ya samu isowa . Gurine mai girman gaske mai cike da kaayan alatu, kayan more rayuwa wanda suka karawa gurin wani kyau da daraja, zaka ranste gurin da ruwan gold akayi stabar wal'wali da daukan idon da yakeyi, yasha Royal furnitures masu daukan ido da jan hankalin mai kallonsu da karatu, sanarwan da akayi SULTAN da tawagarsa na zuwa ne yasa su nutsuwa suka dena kananun zance kamar de a classroom shiruuu suka yi tamkar babu wassu halitta agun, da sauri Security suka bude tankamemen kofan saiga Sultan Muhd Habibullah da Sultana Maryam suna shigowa, yana sanye da farar jallabiya as always da farar kimono mai ra'stin golden colour da hiramin sa. Sultana Maryam na sanye cikin white abaya mai ra'stin golden colour sai golden din fula ko ince turban akanta ya fidda asalin kyanta. suna shigowa kowa ya mike, sun cigaba da tafiya bisa wani hadadden white centre carpet har suka isa mazaunin su wanda yake dan su akayi, wani hadadden golden and white royal kujera ne mai daukan ido da hankali, . anan suka zauna sai ya zaman to suna sama da sauran mutanen, bayan sun gama zama ne sai ga Malik Sultan da Malikat Nubia sun shigo suma da nasu salon dressing din, jallabiya da abaya sai de colour combination din ya ban banta dana su Sultan nasu maroon and golden colour ne, suma gurin zamansu suka karisa wanda yake gefen nasu Sultana hatta mazauninsu ma maroon and golden ne, wani kak'kauran sanarwa aka farayi na cewa SULTAN SALAHUDDEEN DA SULTANA NAJDA sun samu isowa, Masha'allah ko makiyinsu ya gansu shine abinda zai fadi sunyi kyau iya kyau, abinka da kyawawa Sultan Salahuddeen yana sanye da farar jaallabiya da kimono white and golden, sai farin hirami wanda aka nade da wani belt da yasha ado da golden bead wanda suka fi kama da gold masu dauke da
Chapter 17 · 0% Book details