← Book details The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 33

Sashe 16

The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Sun cigaba da taafiya bisa shimfidaddiyar kwaltan daya ya kaisu har hadadden estate din wato SULTAN ABDULMALIK ROYAL ESTATE.
Ya kasance estate mai dumbin tarihi da dogon zamani.
ya ginu tun lokacin Sultan Abdulmalik lokacin dayayi murabus daga karagan Mulki ya daura dansa wato SULTAN MUHD HABIBULLAH,
inda ya baro Cairo ya dawo Egypt da zama shida iyalinsa ya bar dansa acan,
sai ya ksance duk wani dan ahalin ya dawo nan da zama ya zamanto FAMILY HOUSE nasu duk wani jinin Sultan Abdulmalik anan yake rayuwa shida iyalinsa.
guri ne mai matukar girma tamkar gari kowa da sashen shi suna rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da kaunar juna duk da na ciki na ciki baa rasa yan kustiri stome,
kamar yadda kuka san kowani Family da irin nasu mastalan bare gidan sarauta wanda shine matattaran mastaloli,
duk da haka in ka gansu sai sun baka shaawa yadda kansu yake a hade a zahiri,
a mastayinka na bako baka isa ka fahimci wani abu dake faruwa mara kyau a stakaninsu ba,
suna kokaarin hada kansu a idon duniya,
a kowani karshen wata sukan hadu donyin GET TOGHETHER hakan na kara musu hadin kai duk wani dan family yakan halatta wannan taron don ya zama dole ako ina yake a fadin duniya dole yazo,
sun sanu a fadin duniya sabida wassu baiwa da Allah ya musu Allah ya azirtasu da kudi,ilimin addini dana boko, uwa uba kyau da kwarjini Allah yamawa matansu da mazansu wannan baiwan,
kadan daga cikin abinda ya yasa suka sharah suka kuma sanu a fadin duniya kasncewarsu HALF CASS wato ruwa biyu na daya daga cikin abinda yasa su shaharah suka kuma yi suna sannan suka zama abun kwatance a fadin duniya,
iliminsu na both arabi da boko ya taimakesu wajen gudanar da mulkinsu a zamanan ce bisa tafarkin musulunci,
kyansu shi ke kara jan mutane garesu da arzikinsu daya sa musu kwarjini a idon mutane,
Allah ya musu baiwan shiga ran mutane suna da shiga rai duk yawancin su a murde suke baya ga haka suna da manya a familyn su wanda suke da manya makami a fannoni da dama,
suna da duk wani nau'in maikata kama daga land army ,navy, airforce,pilot, doctors, lawyers, prsecutors...., da sauransu yana daya daga cikin abinda ya karamusu karfi ya kuma tara musu dinbum makiya na ciki dana waje .
Basu staya ako ina ba sai bakin wani tamkamemen royal gate black and golden gate din na raga ne so kana iya hangen abinda ke ciki ita kanta gate din abun kallo ne daga hannun dama akwai wani computer wanda daga nan mutum yake neman izini ana kallon ka daga ciki wato security dake ciki na kallon ka daga nan sai sun tabbar da wayene kafun ake bude ma gate don shiga,
already sun san da zuwan Sultan shiyasa basu staya bincike ba gate din da kanta ta bude a wani slow motion hakan ya kara kayatar da abun,
danna cars din sukayi cikin wannan Estate din ko ina securitys ne gurin ya mugun staruwa staywa kwtan ta tashi ma bata lokaci ne,
sun cigaba da bin wannna shinfidaddiyar kwaltan wanda gefe da gefenta shinfidaddun flowers ne msu tashin kamshi da daukan hankali.
tako ina a shimfide yake da interlocks da flowers sun wuce gate har uku kafun suka isa wani tamkamemen Building Wanda na hango kmr castle,
wni water fall ne stakiya wanda yake kewaye da kwalta wanda dole sai kabi kafun kayi parking hakan kuwa sukayi kafun sukayi parking,
zugan securities suka musu kawanya as always sun shinfida royal centre carpet wanda yayi leading nasu zuwa main door din building din, cab din motan aka bude musu suka fito sukayi ciki,
wani tafkeken farlo ne mai kayan more rayuwa katon gaske ne mai dauke da kayan alatu da kyalekyali masu daukan sense,
.bayan wuce zafafan farlo uku da sukayi Wanda servant ke aikin bude musu kof,
ta ko Ina kwasar gaisuwan servant din keyi Wanda ko amsawa basa Yi ,
sanda suka zo bakin kofan farlon Wanda yake tamkar da zinare akayi golden colour ne kofan gashi dagirman gaske jikinshi ko anyi mishi ado da wassu duwastu Wanda Ina kyautata zaton lu'ulu'u ne da murjani harma da diamond
Suna bude kofan suka ja baya suka staya su Kuma suka karasa ciki kasancewar bako wani bawa ne ke da iKon shiga ba sai Wanda aka yardar masa.
basu staya a ko ina ba sai wani sashi a farlon wanda yake dauke da wassu zafafan furnitures masu shegen stada da daukan hankali da walwalin su,
zaka ranste da gold akayi yanda suke sheki da daukan eyes
daga sama ko wani narkeken chandelier ne Wanda akayi shi da danyen zinare wato white gold,
Tiles din farlon kuwa dauke yake da tambarin masarautan Wanda ya Kara kayatar da komai hatta silin din falon zaka ranste da glass akayi yanda yake walwali ga wassu duwastu Wanda ke walwali da kansu suna daukan ido
hango wassu kyawawan larabawa su hudu nayi suna sanye da kayan alfarma maza biyu mata biyu bakowa bane sai sarki mai murabus da dansa wato SULTAN MUHD HABIBULLAH da dansa ko ince babban dansa wanda yayi murabus ya bawa dansa SULTAN SALAHUDDEEN mulki wato MALIK SULTAN IBN HABIBULLAH
sai matansu SULTANA MARYAM wacce take uwargidan Sultan HABIBULLAH sai MALIKAT NUBIA mata Malik Sultan IBN Muhd Habibullah.
fuskan ko wani daya daga cikinsu dauke da murmushi wanda ya juya firkici da alajabi lokaci daya sanadin tOzali da sukayi da yarinyar dake tafe dasu wanda a iya saninsu yau ta cika shekara daya da rasuwa.
atunaninsu ma wannan shine dalilin zuwan su Sultan d Sultana,
sai de sunga akasin hakan kowa bakinshi dauke da tambayoyi da alajabi wanda ya bayyana karara duk da sun kula da hakan sai de basuyi kasa a guiwa ba wajen karasawa inda suke don su gaisa su kuma samusu albarka kafin su yi abinda ya kawosu,
don anasu lissafin yau zasu koma sabida yau tuesday ba friday ba da friday ne zasu kwana sabida saturday and sunday ba zaman palace.
kamar yadda suka saba gaisuwan su ta larabawa gaisawa suka yi sannan suka yi pecking both cheeks nasu haka matan ma sukayi kafun suka zauna.
ita de sai mannewa takeyi ajikin Sultana Najda har suka zauna Malik Sultan ne yayi kaarfin guiwan tambayansu wacece atare dasu,
murmushi Sultan Salahuddeen yayi kafun yace'' atakaaice muma bamu san wacece ba mun de dauketa a mastayin wani Ilhama da Allah ya mana alokacin da muke wani hali na rashin madogara sai shi wanda ya bamu Rinaa ya kuma karbi abunsa''
"ban gane mai kake nufi ba"
inji Sultan Habibullah sadda kanshi kasa yayi cikin girmamawa yace
"wannnan itace gaaskiyar Jaddi"
ba tare da bata lokaci ba ya kwashe duk labarin abinda ya faaru wanda Sultana Najda ta fada masa ya musu da kumaa wanda yayi bincike ya tabbatar ,
kabbara kawai suka hau yi gaba dayan su suna jinjina wannan lamari Sultan Habibullah yace
"wani shawara kuka yanke yanzu"
''bamu yanke shawaran komai ba Jaddi hukuncin ku muke jira dan "
jimmm yayi kadan kafun yace "hakika wannan alamarin yafi karfin tunanin dan adam ko shirinsa wannan wani lamari ne wanda Allah ya stara abunsa dama ance kana naka Allah na nashi ya bamu Safeera ya karbi abinshi mun masa godiya munce Alhamdulillah ya jarabce mu da kaunarta ya kuma dauketa,
don ya auna karfin imanin mu to Alhamdulillah akarshe ga abinda muka samu wato wannan itace sakamakon jarabawan mu duk da ban cire rai akan cewa itadin ma wata jarabawan bace da Allah yayi agaremu ,
na farko bamu san wcece ita ba??
bamu kuma san dagaa ina take ba??
sannan ita kanta bata san wacece ita ba??
bare mu roki alfarma wajen iyayenta su bamu ita don maye mana gurbin abin kaunar mu,"
hmmm dogon numfashi yaja ya cigaba da cewa
"tabbas wannan yahh jarabawace agare mu wanda muke fatan Allah bamu ikon cinta sai de ba yadda zaayi ta maye mana gurbin Safeera don duk bamu san daga ina take ba kuma bamu da karfin ikon da zamu rabata da iyyenta,
alokacin da ta dawo hanklinta ta kuma bukaci komawa mahaifanta bamu da ikon hanata hakan ,"
dummm shine abinda zuciyan Sultana Najda ke bayarwa tana storon jin abinda zai yanke dama shine abinda take gudu kamr ta fashe da kuka take ji shiru,
Sultan Habibullah yayi cos he is speechless right now ahankali Malikat NUBIA tace
"Abie,"
cikin siririyar muryanta maai zallan nustuwa Wanda kana ji ko baka ga Mai shi ba kasan ma'abocin hakuri ne, ga wani zaki dadin saauraro,
dago kanshi yayi ya fuskance ceta ya amsa mata da cewa
"mai ya faru yahh binti,"
zubo wa tayi kasa tayi kneeling ta sadda kanta tace
"ina rokon alfarma agareka dan Allah,"
cikin wani yanayi yace
"fadi Binti,"
"dan Allah Abie ka yarda mu dauki yarnan ta zamanto wani bangare na ahalinmu,"
tayi magana tana hada hannayenta 2
tana hawaye gwanin tausayi ,
"yau akallah shekara 20 bance komai ba bawai dan baani da abin fada ba aa sai dan kawai nasan ko na fada bazai yi amfani ba,
amma ayau gani gabanka ina rokon alfarma daka taimaki zuciyata don tana gab da fashewa,
tun rasuwar yata ban kara yin wani farin ciki ba sai yau ganin wanan yarinyar ya sana na stinci kaina cikin dumbin farin ciki tamkar yata haka nake ganinta,
ayanzu ba kowa nake gani ba face yata dana rasa na rokeka amastayinka na mahaifi agareni ba sirki ba ba kuma shugaba ba a mastayinka na uba nake rokon wannan alframan,"
hakika kowa a wannan gurin sanda ya karaya basu kadai ba hatta masu karatu na tabbar da hakanne,
kallo daya zaka mata ka hango abubuwa da dama atattare da ita da kanshi ya mikar da ita ya kuma zaunar da ita a gefen shi yasa hannu ya goge mata hawayenta yace
"kinyi gaskiya ni ubane a gareki tunda uwa Daya ta haifemu da mahiafinki kuma ahanuna kika taso,
tabbas nayi mamakin yadda kika jure har stawon shekara 20 mun,
miki laifi wanda har yau cikin tarin dana sani muke bamu kyau ta miki ba keda diyarki amma inde hakan zai sa kiji sanyi cikin zuciyarki tohh ki kaddara an gama daga rana mai kaman ta yau ta zama yar ahalin SULTAN ABDULMALIK,
yanzu ba anjima ba zaa mata komai na tabbatan ta yahh kuma jika a wannan ahalin mai albarka bamu kadai ba duniya zata shaida hakan."
fashewa tayi da kuka ta tace
"shukran yahh Abie,"
ta rungumeshi shafa kanta yayi yace
"ya isa wani nannauyan ajiyan zuciya suka sauke gaba daya na farin ciki ahankali ta taso ta karaso inda suke ta mika mata hannu ta ce
"Taal yahh hafiidatii,"
wiki wiki takeyi da idanu ta mika mata hannun ta mikar da ita tana bin fuskarta da kallo ba abinda take gani sai fuskar yarta shalelen ta abin kaunar ta rungumeta tayi stam ajikin ta tana jin wani yanayi na kaunar yarinyar na rasta mata bargo tana ji tamkar suna da wani alaka ta jini,
tare suka zauna a kujera daya inda Malik ke zaune suka saata a stakiya shi kanshi ta mazan kawai yakeyi don yaji abubuwa dadaama akan yarinyar a heart,
nashi wani sanyi yakeji aranshi yana ji tamkar ya biya wani nannauyan bashi da ake binshi da dadewa,
Sultana Maryam da bata ce komai ba tace "yanzu mai zamu sanarwa duniya akanta in suka tambaye mu game da mastayinta??
in mahaifanta suka gaanta mai zamu ce dasu??
ya zamu kare kanmu??
ya zamu mai data ta zamo namu gaba daya??
ta wani hanya??
cikin zumudi da gaggawa Malikat tace "ta hanyar aure,"
hankalin kowa ya dawo kanta dan son karin bayani
"mu aurar da ita a AMEER MAHBEER,"
shiruu falon ya dauka na yan sakanni kafun Sultan Habibullah yace "ka'idan familyn na magaji baya auran bare kuma baya aure haka kawai sai bayan anyi bincike wato istihara da kuma addu'oi,
amma zamu gwada zanyi hakan bani kadai ba inaso yau dukan mu muyi hakan zuwa gobe muga abinda Allah ya stara akan wannan diyar,"
kowa yayi naam da wannan zancen sai ayanzu hankalin Sultana Maryam ya kwanta tace "ni bazaa bani ita inji duminta bane,"
murmushi sukayi suka mikata gareta kamar wata jaririya "mashaallah"
shine abinda tace tana murmushi
"ahlan wa sahlan ya Hafidati,"
atakaice de ko ince agurguje sun kwashi mintuna suna nuna mata kauna kafun aka sanar dacewa gobe akwai Family meeting ana bukatar kowa ya hallara bayan gayyato SHEIK JABEER wanda ya kaasance babban malami na familyn,
shine limamin wannan familyn ya gada gun mahaifinsa atakaice sune Imam don ka'idar wannan family komai gada akeyi.
sun sanar dashi abinda suke bukata yace ba komai shima zaiyi istiharan suga abinda zai faru tun da dama shine ka'idan faamilyn
DA FATAN KUNA JIN DADIN WANNAN LABARI, KU CIGABA DA BIYONI DAN WARWARE MUKU TULIN KULLIN DAKE CIKINTA.
Comment da react da Kuma sharhi shi zai sa na tabbatar da Kuna biye dani.
Follow this link to join my WhatsApp group and
me with comment and react
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
by Queen Mahirah
Comment and share
THE TWO LIGHT
[RIKICIN GIDAN SARAUTA
BY;QUEEN MAHIRAH
?29 ?January, ?2024
09:28:53 PM
Follow this link to join my WhatsApp group and shower
me with comment and react
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
Chapter 16 · 0% Book details