Sashe 19
The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
EGYPHT {CAIRO} Barewa baza tayi gudu danta yayi rarrafe ba, tabbas wannan magana haka yake ko ba'a fada maka ba kayi tozali da wannan halittan kasan ta hada jini da Muhd Kahter wanda ake ma lakabi da NAMIJIN ZAKI, bama zaki ba a'a shi namijin zaki ne mai wastar da taro, tacigaba da tafiyanta acikin nutsauwa ba tare da sanin cewa yaja kanta attention takeyi ba, ako wani taku daya da takeyi yana tafiya da bugun zuciyan mahassada da makiya, tana isa inda su Sultan suke Sultana Najda da kanta ta mike ta kaita har gurin zamanta wanda yake a bangaren damansu kujeru biyu masu shegen kyau da daukan hankali, a daya daga ciki ta ajiyeta ta kuma gyara mata zamanta da kyau kafun ta koma gurin zamanta ta zauna, stitttt gun ya Chief of army staff ne yace "kuna jira sai ance ku bawa Zawjatul Ameer girma ne, ko sai ance muku ku gyada ta," ai kamar masu rige rigen shiga bandaki haka suka mike zan dan akan kafansu don bata girma kafun kowa ya koma ya zauna, Minister of information ne ya mike yace " maraba da zuwanki Zawjatul Ameer, a mai makon dunbun mutanen family Sultan Abdulmalik muna miki maraba da shigowa cikin ahalin mu amastayin sirka, Allah ya baku zaman lfy keda Ameer Mahbeer, ya kuma azirtaku da zuri'a dayyiba," dan sadda kanshi yayi kasa alaman ban girma kafun ya koma ya zauna Malik Sultan yace " akwai wani mai neman karin bayani " wani na yamike bayan neman izini yace " tabbas na gamsu ita yar Muhd Kahter ne, to amma ina shi mahaifin nata" " mahaifinta yana kasar SIN in kana da bukatar ganinshi sai yazo, " wani dammm kirjinshi ya bada cikin rawar murya yace" a..a..a.aaa ranka shi dade," wani cute smile ya sake dama yasan za'a rina kaf Kingdom nasu kowa storonsa yakeji matuka yana da zafi sosai, mutane dayawa na cewa halinsa ya dauko, yana kaunarsa sosai yana kuma alfahari dashi mastayin dansa kuma sirkinsa, Sultan Habibullah yace" wani sati ran juma'a duniya zata shaida daurin auren AMEER MAHBEER DA AMEERA MEHNOOR, ina fatan kowa ya halicci wannan biki mai albarka," Imam Jabir ne ya mike don rufe taro da addu'a aka rufe taro kowa ya kama gabansa. Suna dawowa cikin gida ba bata lokaci aka fara mawa Zaawjatul Ameer gyaran jiki, sai shirye shirye akeyi kowa yana cikin farin ciki baya Malikat Nubia wani irin kaunar ta ne yake yawo ako ina na jikinta, ko gyaran jikin da za'a mata ma tana gurin duk da amintacciyar Jakadiyar ta (minister of women affairs), Na Nan, gani take inta barta ita daya kamar za'a cutar mata da ita, ta bangaren Sultana Najda ma haka ne sai faman shiri takeyi abun ya hadu mata biyu farin cikin har yaso ya mata yawa, za'ayi bikin danta kwaalli daya data ke dasahi a duniya da halitta mafi soyuwa agareta ai sai kiran yan uwa da abokan arzike take tana sanar musu, har ta manta cewa an sanar a kafafen sada labaru da taimakon S.A.M wato special adviser on media and publicity { san kira}, zumudi yasa ta manta hakan Sultan Salahuddeen dake zaune ya zuba mata ido sai kallonta yakeyi harda taguminshi, shi yamanta rabon da yaganta cikin farin ciki irin haka, sai abun ya zama masa sabo, tabbas maganan Imam Jabir da hasa'shensa ya tabbata yarinyar alkairi ce agaresu, da sannu zasu gane hakan, tun kafun aje ko ina ma sun fara gani ko daga yanzu sun fara gane makiyansu daga dan zaman da akayi kawai, bai san ma ta zauna a gefensa ba sai jin lallausan hannunta yayi a face nashi tace " Amirul dawlati what is wrong" lallausan smile ya sake yace" ba komai," "okay dama na gama hada maka kayanka kasan anjima jirginka zai tashi ko ka koma Cairo," ido ya zuba mata yana kallonta sanda ta karasa zancen yace "in koma ko mu koma" zumburo baki tayi gaba tayi folding hannunta a chest nata in a chaildish tune tace " ba inda zanje ina nan har sai anyi auren" wani warm smile ya sake ya mike yace "tunda kece mijin ba ni zaki iya zama, ki shirya da wuri kar lokaci ya kure nima yanzu zanyi nawa shirin" bata ce dashi kala ba ya fara ragea kayan jikinshi don yin wanka, ganin bata taso don taya shi bane yasa shi juyowa ya ganta aikuwa kamar jira take ya juyo ta fasahe da kuka da iya karfinta har shisshike wa takeyi " Yah Allah" shine abinda ya fadi ya staya kasakai yana kallon ikon Rabbi ganin kukan nata ba mai karewa bane yasa ya je don yin rarrashi, "Ummu mahbeer yanzu dan nace mutafi shine kike zabga wannan kukan kamaar wadda aka ce miki Mahbeer ya mutu," kara volume din kukan nata tayi yace " ya isa ni karki tara mun jama'a ace yanka ki nake, ina de tafiyan nea bakya so to yi zaman ki, dama ni stokalanki ma nakeyi" aiko ta fara jero smile iri daban daban yace " cry cry baby kawai" ya mike don cigaba da shirin wanka akarshe de ita ta taya sa yadda ta saba, ta shirya shi stabb ta hada masa kayansa da kanta, Sultana Maryam na zaune sashin ta tana ta nata shirin sai ga Ameera Subaihat ta shigo ita da wata yarinya mai kama da ita kana ganinta kasan yarta ne, slaves na ganinta suka fara gyada ta sai de ko kula su batayi ba inda mahaifiyarta take ta karasa nan suka cika ta da kayan mosta baki suka basu guri don su tattauna, Sultana maryama na kishingide ajikin wani makeken throw pillow mai laushin gaske bisa wani hadaddden garduma irin na masu sarauta, dakin shakatawan tane ba kujeru adakin sai throw pillows da garduma anyi wa dakin kwalliya da gashin dawisu, wani dan table ne kajere a stakiyan dakin da wani tea flask karami kamar na gold da kananan kofuna na shan shayi sai wani makeken tire na kayan marmari, a dun gun dakin kuwa burner ne sai tashin kamshin turaren wuta yakeyi, zama tayi agefen mahaifiyarta tana ta cin magani ranta a bace sai hade gira takeyi ita da yarta, kallo daya Sultana Maryama tayi musu ta kauda kanta don tasan mai ke tafe dasu ta cigaba da danne dannen ta a waya, ganin ta sharesu ne yasata cewa "yanzu Ummi abinda kuka mun kun min adalci, kinsan yadda SABREEN ke kaunar Ameer Mahbeer shine za'a hada auransa da wata bare da ba'a san asalinta ba" ta kai akalla 5 min kafun ta dago kai ta kare mata kallo na dan wani sakanni ta kauda kai kamar baza tace komai ba stabar izza sai can tace "kicewa wannan sakaryar yarki marar tarbiyan ta tashi ta fice mun daga daki ko insa security su fidda ta" " haba ummi mai yasa kuke haka ne sai kace baku kuka haifeni ba Sabreen fa jikarki ce jinana ce ita" cike da bacin rai tace "Subaihat tun muna shiri da juna, ni nace ki auri ubanta ina saida mutun cin mu kikayi kika bijire mana kika auri ubanta, wa zai so hada jini da marar tarbiyan yarki din nan wacce bata san darajan manya ba har ta shigo ta zauna amma ta gagara gyada ni stabar rasahin tarbiya, kin dauka haka kawai ake auran dan sarki azama gimbiya ne, in kina tunanin wannan yar nakin zata zama gimbiya to ki canja lale anan family babu mai hada jini da mai rayuwar nasara, kin daura ta bisa turban turawa kin kai ta yin rayuwa cikin su duba shigan dake jikinta, body hop top da tight jeans imagine gimbiyar Egypt da wannan dressing din this can't be possible, ko sarauniya wannan sakaryar bata kai zama ba bare Sultana, ki tasahi ki fice mun tun kafun ki fusata ni ta fadi hakanne a stawace" sanin halin mahaifiyarta ne yasa ta kama hannun yarta suka fito bata staya ko ina ba sai part din Malikat Nubia tako yi sa'a tasameta ana ta gyara a amarya, ita ko sai zuba shagwaba takeyi don da kyar take yadda ahaka ma mutane kadan ne agun wanda ta yadda dasu ne, bako sallama bare neman izini ta shigo da masifanta " tohhh muna fuka algun guma, ashe ba yayana kadai kika shanye ba har mahaifiyata ma kin shanye, da bakin jininki marar albarka mai tarwasta farin cikin iyali, an wani damu mutane lokacin auroki wai hasken da zata hasakaka masarautar mu har wani suna ake kiran ki dashi wai uwar haske, to ina hasken yake kin haifo wa mutane mazina'ciya mai zina da auranta, kin kawo wata shegiya wai jikarki zata zama Sultana ko, to kunyi kadan ke da ita wallahi sai de in bani da rai sai de in na dena numfashi hakan zai faru" tunda ta fara magana Malikat Nubia bata ce komai hasalima ko kallonta bata yi ba ta bawa ajiyan ta a iska duk da ranta na suya don magan ganun da take fada mata marassa dadi agaban masu aiki, bata kula taba inda sabo ta saba da rashin mutun cin Subaihat tun suna yara haka take mata ganin bata kula ta sai de bata taba yin wannan kuskuren a Sultana Najda duk da kasancewarta surkar su ita kadai ta rena, ganin bata kula taba ne yasa ta karasawa inda Zawjatul Ameer da ta takure a guri daya tun dazun don storo, ko kokarin gaura mata mari takeyi taji an rike hannunta gammm ba kowa ya rike hannunta ba sai Sultan Salahuddeen kallo daya zaka masa ka hangi zallan bacin ran dake idonsa wulli yayi da hannunta ya zabga mata maruka hudu masu kyau, Tassss tassss tassss tassss kawai kake ji, wani mugun shot yayi da ita da kafansa kamar ya samu ball idonsa ya rufe ya manta cewa kanwaar mahaifinsa ne ita stabaar bacin rai, Sultana Najda ne ta rike shi tace "sabr sabr ya Amirul Dawlati, stawa ta dakawa slaves su fita babu shiri suka fara arcewa adari sai huci yakeyi itako tama suma yarta ne keta raskar kuka akanta "zaki mana shiruu ko sai na an miki dukan sakwara" inji Sultana Najda salatin da sukaji Malikat Nubia nayi ne ya dawo da hankalinsu, Zawjatul Ameer