← Book details The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 33

Sashe 4

The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chief Imam daya gama fahimtarta ne ya kira ta cikin muryanshi ta nutsuwa kamar haka
"Binti,"
firgitt ta dawo normal sense dinta tace
"naam Abba,"
da wuri ta saukar da kanta kasa, ganin irin kallon daya ke binta dashi yace "
"mai ya sameki,ko jikin naki ne,"
kai ta jijjiga mishi tace
" aa Abba lafiya na kalau"
"kin tabbata, "
tace" ehh Abba,"
kai ya gyada yace
" yayi kyau, munyi waya da mahaifin su Faruq yace gobe zai zo ya duba ku,"
kara saukar da kanta kasa tayi cike da kunya tace
"to Abba,"
sai wani bangare na zuciyarta na cigaba da stinkewa akai akai, Innani tace
"to yanzu Sheik ya za'ayi da yaran kaga mu yau zamu koma gida, kuma bai dace a rabasu da mahaifiyarsu ba, duk da ba shayar dasu zatayi ba, amma de suna bukatan dumin jikinta,"
gyada kai yayi yace
"to ya kike ganin zaayi yanzu",
"tohh nace ko zamu bari sai gobe sai kawai mu tafi gaba daya, tunda likitan yace zuwa gobe zata farfado,"
murmushi yayi yace
"duk yanda kika ce haka za'ayi uwargidan sheik,"
murmushin itama ta masa, shiko yana daya daga cikin abinda yasa yake kara sonta, sabida yanda take darajashi wanda yakai duk abinda ya fito daga hannunshi shi, shima nashi darajan na daban ne, ga tausayi shi kam yasan yayi saan mata,
Faruq ne ya kaste musu hanzari da cewa nikam
"yau anan zan kwana nida triplet dinaaa," ya fada in his childish voice Innani tace
"cununu da baki, ba inda zaka kwana gida zaka koma, gun Umaima ku kwana tare,"
{wato mama karama} make kafada yayi, yace
" nikam aa anan zan kwana ba gurin Umaima ba, ni agurin Ummi na zan kwana,"
" eyyehh,!!"
abinda Innani tace
"sai mu gani, tunda kaine dani bani ne da kai ba,"
"nikam aaa anan zan kwana, ai ni mijinki ne dole kiyi abinda nace"
Ummin shi ne ta fisgo shi, cikin jin haushin yanda yake musayar zance da mahaifiyarta tace
"baka da hankali ne, saar ka ce ita dazatayi magana kaki ji wakafi eyyeh,"
Innani ne ta mike da sauri ta karbi Faruq daga hannun Umminsa, tace "
Fatima kashe shi zakiyi ne, ina ruwankin dashi,"
cikin kuluwa tace
"haba umma kiji yanda yaron nan yake miki rashin kuny,"
dakuwa ta mata tace
"hungo naki Fatima nace hungo naki, ina ruwanki ake yayi wa rashin kunyan, kuma mai abun rashin kunya ni ba kakarsa bace, "
shiru tayi bata ce komai ba sai tafasa da zuciyanta keyi tana jin haushin yanda Faruq ke wasta magana a Innani duk yanda yaso, bata son hakan amma innani ta gagara gane wa, ba dama ta kwabe sa sai ta nuna bacin ranta,
ba abinda yakara bata haushi sai ganin yadda innani keta faman rarrashin sa da take yi,
itako har wani hawayen bakin ciki take yi, Abban tane ya kira ta ya nuna mata gefensa, wato tazo ta zauna ba musu taje ta zauna,
murmushi yayi yace "sabr ya Binti, dena zubar da kwalla akan danki, hakan ba kyau, ko bakya so yayi albarka ne,"
da wuri da jijjiga kanta ta goge hawayenta, murmushi ya kara yi yace
"Imam yaro ne,amma yana da fahimta, innani mahaifiyar ki ne kuma tana da fada, sannan tana kaunar Imam kuma bata son laifinsa ko kadan, ke kuma bakyason yanda yake yi mata wani abun ko,"
gyada mishi kai tayi yayi murmushi yace,
"tohh yanzu kinsan Imam nada fahimta, cikin nutsuwa zaki na daura shi akan hanya, ki nuna masa abinda yake ba dai bane, ba dole sai agaban innani zaki stawatar mishi ba aa daga baya sai ki kirashi ki mishi fada, akan abinda yake mata, sannan ki dena yin fushi dashi haka, dan zai iya jawo masa mastala arayuwar sa, in ya bata miki rai ki daure ki samasa albarka, ki kuma masa fatan shiriya, sannan kiyi kokarin daura sa akan hanya, ki kuma dena bata ran mahifiyarki akan Imam, in suna abu karki kula su ko ma kibar inda suke, inta bukaci kimasa fada to sai kiyi,"
"tohhh Abba inshallahu zan kiyaye",
" Allah miki Albarka, "
"amiiin Abba"
sallaman da akayi ne yasa hankalinsu ya koma kan wanda yayi sallaman tare da amsa masa,
wata yar matashiyar yarinya ne tashigo, hannunta dauke da basket wanda da alama na abinci ne sai wani jaka,
kallo daya zaka mata ka hango stananin kaman da suke da innani,
Faruq ne yaje da gudu ya mata oyoyo itama oyoyon tamishi kafin ya karbi jakan hannunta suka karaso har kasa ta stuguna,
cikin yaren fulatanci ta gaisar da Chief Imam ya amsa fuska dauke da faraa, ta juya bangaren innani ma ta gaishe ta, itama ta amsa sannan ta gyada ummin Imam, ta mata ya jiki, ta amasa mata gaisuwar duk cikin yaren fullanci,
Faruq yace" Umaima zo kiga triplet din mu"
murmushi tayi tace
"kaide little baa rabaka da shirme, triplet kuma a ina, ina muka samu yan uku,"
hannunta yaja yace
" zo kigani,"
haka yakaita har gaban gadon yaran dake kwance abin shaawa,
ware ido
tayi ta dafe kirji tace
" kai mai zan gani,"
ta juyo ta fuskanci su ummi tana neman karin bayani little yayi wufff yace
"mata stintar su muka yi nida jaddi na harda mamansu,"
waro ido tayi tace "
mun shiga uku stintarsu kuma, umma wai haka,"
tabe baki tayi tace
"bakiji abinda ya fada bane ko karya zai miki,"
"shine kuma aka wani hada su da islam kalen su shafa mata wani cutan waya sani ma ko aljanu, ne gaskiya bai dace ahadasu da islam ba,"
hannu tasa da niyan dauke islam innani ta daka mata wani stawa
"keeee karki kuskura baki da hankali ne waye sa'an ki anan, ke zaki nuna mana abinda ya dace muyi, wa kika fi,"
zumburo baki tayi gaba tace
"haba umma ni mai kuma nayi ai gaskiya na fada, kawai daga stinto yara sai ahada su da namu dube su fa kamar wassu yayan aljanu",
innani ne ta hau banbami da sababi shiko,
Chief Imam bai ce kala ba sai hasaso abubuwa da dama da yakeyi game da yartashi Zainab, wanda halinta ya ban ban ta dana yar uwarta,
kai kaf gidan ma ita halinta daban ne ita tana da bakin hali, bata son mutane bawai hayaniya ne bata so ba bare ace miskila ce aa ita nata bakin hali ne ayanda ya auna, tana kuma da hassada wanda har yar uwarta ma takanyiwa, tana kuma da girman kai da son ace tafi kowa, yana da labarin irin tabaran datakeyi arugarsu ko abota bada kowa takeyi ba sai mai kudi,
kuma yanzu ma yasan kyan yaran data gani ne yasa ta ce wa kamar aljanu,
haka koda aka haifi islam sanda tayi furucin daya girgiza shi, wai ita ma sai ta auri balarabe wanda yafi mijiin yayarta kyau ta haifi yayan da suka fi na yayarta kyau,
firgitt ya dawo normal sense nashi jin kukan jariran da alama sun tashi daga bacci,
kuka suke ba kakkautawa wanda suka ki yin shiru innani tace
"wannan bazaa akai su gun mahaifiyarsu ba kuwa, ko in sukaji dumin jikinta zasuyi shiru,"
ballawa Zainab harara tayi tace
"muna fuka mai bakin halin stiya sai ki dauki dayan muje ai,"
,Chief bai ce kala ba ya mike ya musu jagora har dakin da mtar ke kwance abun tausayi suka shiga,
wani dummm zuciyan Zainab yabayar ganin irin kyan matar wanda yasa ta mugun rena kanta,
tabbas duk inda zaa kwatanta kyau matar nan takai har tafi dan ko kyau da kanshi ya ganta sai ya bata guri,
stawan da innani ta mata ne ya dawo da ita hankalinta
"zaki bani yarinyar ne ko saina gaggaura miki mari,"
sum sum tamika mata dan duk rashin kunyar ta tana storon innani ta dake ta,
dan sai tayi kwanaki bata ware ba karban yar tayi ta kwantar da ita akirjin mahaifiyarta yanda tayi wa dayan,
kamar kibtawa da bismillah kuwa sukayi shiru basu kara cewa komai ba, suka yi shiru sai sauke ajiyan zuciya da sukeyi akai akai, cikin mintina kadan suka koma bacci balla mata harara innani tayi tace
"kije ki dauko mun jakan kayana da kayan sawan yaran, ki kuma kawo mun abinci,"
zumbura baki tayi tace nifa ban san inda kayansu yake ba, tana magan tana aunawa matar dake kwance harara wanda bata ma san tanayi ba,
innani ne tayi kanta tamkar zata gaggaura mata mari ko ince da niyan gaggaura mata mari ganin hakan yasa ta fita da gudu
tana fita ta hadu da Abban su wato Chief kallon daya bita dashi ne yasa ta hadiyan yawu tasan tabbas ransa ya baci matuka akan abinda tayi,
ita ta manta cewa yana dakin ma tayi wannan diban albarkan wani miyau mai zafi ta hadiya, dan tasan zataci stelen uwata dan Abba yamafi umman zafi sosai,
ai da sauri ta wuce kanta har wani hardewa yakeyi ta isa bakin kofan dakin saide abinda taji yar uwarta ta na fada ne yasa ta ja burki,
,wani murmushi tayi na nasara dan tabbas ta samu makamin da zata fatattki matarnan da yayanta daga gidansu, dan tasan muddin matar nan zata cigaba da zama agidansu tofa kashinta ya bushe,
yanzu ma tasan sai Abba yaci ubanta dole tasan yadda zatayi ta ingizasu wani murmushin ta karayi ta murda kofan dakin
QUEEN
MAHIRAH
IDRISS
THE TWO LIGHT
[RIKICIN GIDAN SARAUTA
By;Mahirah Idriss
?12/?7/?2023
10:01:45 AM

Follow this link to join my WhatsApp group shower
with comment and react
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
Chapter 4 · 0% Book details