← Book details The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 33

Sashe 3

The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

imam kafin ya kara cewa "ahaaa that remind me, Ummi kinsan mai ya faru kuwa yau da muka je farm da Jaddi," muryan chief imam sukaji abayansu yana cewa " tohhh sarkin hira kabar Ummin naka ta huta mana" da sauri little imam ya taso yazo inda Jaddin nasa yake ya kama hannunsa yace "Jaddi ina babies din Ummi tayi feeding,"nasu sai granny tayi musu wanka," Ummin little imam ne ta sauko daga kan gadon marassa lafiyan da take ta stuguna har kasa ta gaisar da chief imam, wanda yake mahaifi awajanta fuskarsa dauke da murmushi ya amsa gaisuwar yar tasa yana mata ya jiki, tace "da sauki Abba jiki Alhamdulillah," "haka ake so Allah kara sauki," karan bude toilet din da suka ji yasa suka mai da hankalinsu, wata kyakkyawar dattijuwa ce ta fito daga bathroom hannunta dauke da baby, wanda ke nade acikin towel na yara pink colour fuskarta dauke da murnushi, ta iso cikin dakin tasamu guri ta zauna tace "sannu da zuwa Sheik kun iso lafiya,?" murmushi chief imam yayi, cike da kaunar matar nashi yace "mun same ku lafiya ya mai jikin," murmushi tayi tace "jiki alhamdulillah," " to ALLAH kara sauki," little faruq dake gefe ne ya turo bakinsa gaba yayi kicin kicin da fuska, kamar zaiyi kuka yace "ni ni ba ruwa na da ke bazan kara kula ki ba, kuma ki bamu Islam din mu, tunda abin naki haka ne, " dattijuwar da Faruq ya kira da innani tace "kaji dan kesan uwa ani zakawa badala da iya shege," fashewa da kuka Faruq yayi ya rike hannun Jaddinsa yace "Jaddi kaganta ko tana zagi na," murmushi Chief Imam yayi yace "mai ya faru ne haka, kai da innanin ka mai ya hada ku haka," Faruq ne yayi magana cikin childish voice nashi yace "ba ita bane bata mun sannu da zuwa ba ko gishe ni bata yiba, ta fara gaisheka bayan kuma nine babba, kuma fa ni da zuwa na ita na fara tambaya," murmushi Chief Imam yayi dajin zallan yarinta agun Faruq yace "kai kai gaskiya innani bata kyauta ba, ya zata ki gaida mai gidanta to yanzu barta kayi hakuri ka yafe mata baza ta kara ba kabarta da halinta," murmushin jin dadi Faru yayi yace "tohh Jaddi na barta, kuma baza mu bata yan biyun mu bako," gyada masa kai yayi abinka da salihin bawan da bai fiye magana ba, sai ambaton Allah innani ne ta daga kai ta kalla Chief Imam fuska da alaman tambaya da neman karin bayani game da abinda little yace, kallo daya ya mata ya fahimci abinda ke ranta dama ance labarin zuciya atambayi fuska { niko Queen mahirah nace ada kenan yanzu labarin zuciya atambayi whatsapp status din mutum} batare da wani bata lokaci ba Chief Imam ya zayyana masu komai cikin nutsuwa datake halitta ce agareshi, Innani da mahaifiyar Faruq sun girgiza matuka da jin wannan labarin sun kuma tausaya wa wayannan bayin Allah wato matar da yayanta, batare da sun gama jajanta abun ba suka ji sallaman Dr, wanda basu amsa ba sanda suka suturta jikinsu maana suka sa mayafi sannan suka amsa masa sallaman , da yayi garesu, suka kuma bashi izinin shigowa shida wassu nurses guda biyu, hannunsu dauke da babies din shi kuma Dr hannunsa dauke da milk din da zaa basu, wayannan nurses din suka nufi gun Innani wanda ta kwantar da Islam datayi bacci batare da an sa mataa kaya ba, karban dayan tayi itama Ummin Faruq ta karbi daya kusan atare suka furta masha' allah ganin irin kyawun da Allah ya azirta wayannan yaran dashi, tamkar larabawan EGYPHT, Innani tace "ayyah bayin Allah dube su yanda suka yi ja, dagani sun sha wahala da'alama kuma basu saba da ita ba, da gani ma wannan basu yi arba'in ba, kaman sa'anun Islam nema," Ummin Faruq da tayi zurfi cikin kogin tunani ne tayi firgitt ta dawo normal sense dinta, jin abinda Innani tace "bari na hada masu ruwan wanka inna wanke su sai abasu madaran nasu su sha, " cewar Innani Ummin Faruq tace "to umma," mikewa tayi ta kwantar da baby dake hannunta ta shiga toilet ta hado ruwan dumi ta fito dashi, tazo ta dauki wanda ta jiye ta cire mata kayanta tas, ta nufi gurin ruwan da ita ta sata aciki ba shiri ta bude bakinta ta fara kuka enyehh enyehh, abinka da jariri kowa yasan al'adansu ne kukan wanka, haka ta wanketa tass, tasa ta cikin wani towel ta nade ta, mika wa Ummin Faruq ita, ta karbi na hannun nata itama tamata wankan, ita ko Ummin Faruq ta fara bata milk din ba musu ta karba ta fara sha, har abin tausayi, kamar wanda akamawa horon yunwa, ita kanta sanda idon ta ya cika da kwalla dan tausayin babyn, Faruq dake gefen Ummin nashi yace " kai Ummi ganta kaman zata cinye feeder, ga yanda take sha gaskiya she is so starving," daga bangaren Innani kuwa ta gama mata wankan tass itama ta fara bata milk din, hka itama ma kamar zatayi swallowing feeder, kana gani kasan ba karamin yunwa suke ji ba, na hannun mahaifiyar Faruq ne ta fara koshii, inda ta daura ta a shoulder dinta tayi ga'sta sannan ta saukar da ita, daga cikin kayan Islam aka duba musu kayan sawa over roll tasa mata wanda ya amshe ta, bayan lotion data shafa mata tasa mata diaper da perfume, ta taje mata yalwaceccen gashin kanta mai dan karen yawa da stansi hadi da laushe baki wuluk dashi, fula tasa mata gudun kar mura ya kamata dan sai hattishawa take ta yi, ba karamin kyau tayi ba haka itama na hannun Innani ta shiryata, sun yi kyau ba kadan ba, dukansu uku aka kwantar dasu aguri daya, sai suka zama abin shaawa tamkar yan uku, Faruq yace "woww ummi look at them kamar wassu triplet," Innani ta amshi zancen da cewa "mashaallah gansu kamar yayan larabawa, sai Islam din ma ta saje dasu kamar wata balarabiya ta zama itama, har wanin kama suke kamar uba daya ya haifesu," wanii dummmmm kirjin ummi ya bayar dajin maganan Innani daya zo mata tamkar saukar aradu ta ka, tabbas shine abinda take hange tun kallon farko data mawa babies din, yanayin kaman jinin da suke da mahaifin su Islam ya fito karara, dan baza kace suna kama na fuska b saide na jini da yana yin halitta irin su haskensu da gashi sai kuma wani tabo data gani wanda mahaifin su Islam na da shi haka Islam da Faruq din ma nada shi, ta taba tambayarsa tabon ta mai ne ne ya amsa mata da cewa gadon gidansu ne to mai hakan yake nufii shin wayannan yaran suwa ye ne???, daga ina suke??? mai ne ne hadinsu da mijinta???, karde abinda take gudu ne zai faru, dako haka ne tana gabb da rasa ranta Chief Imam dake gefe ne wanda yake kula d yananyinta tun dazu da irin kallon da takewa yaran, ya fahimci irin halin da ta shiga wanda shima anasa bangaren haka ne yace Bintiii.............!!!!!!!!!! END OF PAGE 1 MU HADU A PAGE 2 Queen Mahirah THE TWO LIGHT [ RIKICIN GIDAN SARAUTA ] BY; Mahirah Idriss ?06 ?December, ?2023 12:32:05 PM
Chapter 3 · 0% Book details