← Book details The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 33

Sashe 18

The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tambarin masarautan, hakan ya mugun kara fidda asalin kyansa, fuskansa na dauke da eye glasses siriri wanda mafi akasari Dr ne ke sawa, ya fidda siririn mikekken hancinsa kamar shi ya yi abinsa, fuskarsa zagaye da hadadden mans pride dinsa mai daukan hankali da walwali inka gansa kamar shi yayi kansa, daga gefensa Sultana Najda ne wanda ke sanye da wani hadadden white abaya mai golden V neck, da hadaddiyar turban dinta fari wanda yasha golden bead ya kara haskaka turban din, kafarta na sanye da high hill mai kama da sandal white ne ya fidda santala santalan fingers dinta, hannunta dauke da wani cute small purse dinta wanda yasha bead golden colour, suna bisa centre carpet wanda yayi leading nasu har gurin zamansu wanda yake kasa dana su Sultan Habibullah sai de yafi nasu staruwa da kyau, shima white and golden colour ne sai de yafi ko wannae kyau da staruwa, sanda suka zauna kafun kowa ya zauna, sun dau akalla 5 min kafin Imam Jabir ya bude taron da aaddu'a bisa umarnin da Sultan Habibullah ya bashi, kowa ya shafa addu'a sannan Minister of information {mai shela }, ya mike don sanar da abinda zaayi ya fara da fadan date time sannan ya gangaro the main point "ayau mun taru anan ne badan komai ba sai dan tabbatar da wani alamari kamar yadda kuka sani ance gani ya kori ji, to ayau zamu shaida fuskar AMIRA MEHNOOR BINT MUHD KAHTER IBN ABDALLAH amastayin ZAWJATUL AMEER," cikin kan'kanin lokaci gurin ya kaure da hayaniya da cece kuce kowa da abinda yake fadi ga masu alajabi nayi ,maasu farin ciki nayi, muna fukai da azzalumai zalin cinsu yaki boyuwa, Army commander { sarkin yaki }, ya buga wani stawa wanda yasa kowa shan ruwan jikin sa cikin zallan bacin rai yace " hattara agaban Sultan kuke ba kasuwa ba kowa ya maida hankalinsa ko jikin mutum ya gaya masa", stitttt kake ji akayi kowa ya hadiye zancensa aransa don sun san halin Army cammander baruwansa da matasyinka ko girmanka jibganka zai yi gashi kiransa ba irin na sauran mutane bane giant ne a murde yake ga stayi da fadi, bayan ya kammala karanta shedule din ne ya juya ya fuskanci su Sultan yace "SUHATAJ ya aiko sakon ban hakuri bai samu zuwa ba don suna cikin wani yar maastala, babbaan dan su satinsa 2 anrasa sa, suna cikin wani yanayi yasa baasu da karfin guiwan zuwa yanemi da amasa uzuri," gyada kai Sultan Habibullah yayi daga nan bai kara cewa komai ba sai alama da yayi wa Malik Sultan da yayi magana, cikin girmamawa ya fara magana da muryansa mai taushi da dadin sauraro Wanda zallan IZZA da MULKI Hadi d karfin IKO ya bayyana kararar aciki, "ba sai na kara mai mai tawa ba kunji abinda Minister of information ya fada, ga mai bukatan karin bayani ko jaa Bismillah" kamar dama jira yake ayi magana ya mike yace, "muna so muji taya hakan ta faru bayan kowa yasan yau shekara 20 da rasuwar Amira Zulaihat da yaranta" murmushi Malik Sultan yayi dama yasan zaa rinaa yau zasu sha tambayoyi sai de sun shiyawa hakan yace " FUAD IBN SAREE kayi tambaya mai kyau, kasan ance kana naka Allah na nashi mu munyi namu tohh yanzu lokacin mu ya tafi dama da sa'a tabaar hannun mu ta koma ga ALLAH {S.W.T}, ina fata na amsa maka tambayanka" " ehh " ya zauna ba wai dan yaso ba, ba kuma dan ya samu abinda yake so ba, wani ne ya kara mikewa bayan neman izini kamar yadda na farko yayi, yace " taya za'ayi mu yadda cewa ita jinin AMEER MUHD KAHTER ne" murmushi Malik Sultan ya kara yi a karo na biyu yace "kana ganinta zaka tabbatar da hakan sanan inaso kusan ba yaddar ku muke bukata ba ko amincewar ku ba zaka iya zama yanzu" wani ne ya kara tashi yace " naji ance ZAWJATUL AMEER mai hakan yake nufi???," " a garinku idan ance ZAWJATUL AMEER mai ake nufi???," ya waaurgo masa tambaya "ana nufin matar yarima " gyada kai yayi yace "masha'Allah tohh muma haka muke nufi " shima guiwa a sace ya koma ya zauna kowa yasha ruwan jikinshi tun fari daasuka ga MALIK SULTAN ne zai amsa tambayoyi sun san abun yafi karfinsu, sun fahinci ba yaddar su ake buka ta ba ko lokacin Mulkinsa shi magana daya yakeyi, ya kasance mutun mai zafi da guntun magana wadda da zaran ya fadeta ko ka gane ko baka gane ba kai ta shafa, ya kuma iya bada amsa dai dai da tambayanka, shi baya son reni. Minister of infomation ne yace "akwai wani mai ta, mai tambayan," shirun da yaji ne yasa ya fahimci babu, "akarshe zan gabatar muku da MEHNOOR BINT MUHD KAHTER ZAWJATUL AMEER " wangale kofan akayi wani haaske ne ya fito wanda ya haska idon kowa agun ya mamaye wannan dakin Taron Wanda ya Sanya storo da firkici a zuciyan munafukai ya Kuma tabbatar musu da abinda ake Fadi batare da sun ga Mai shigowa ba. sanye take da wani arnen fitted gown white colou r da wani kimono mai dogon hannu har kasa, daga baya yana jan kasa kun'kuminta a daure da wani belt golden colour haka ajikin komono anyi kwalliya da golden anyi wassu zane wanda yake representing royalty, kanta ko ba dankwali gashinta yaasha gyara anzuba shi har kugunta sai tashin kamshi yakeyi, tana sanye da crown golden colour kana gani basai an fada maka ba kasan gold da diamond Wanda akayi ado dashi ajiki, kafanta sanye da wani royal designer toms white kwalliyan jiki kuwa golden, hannunta sanye da white handa socks daya baayyanar da asalin zararran fingers dinta, Fuskanta ko makeup Babu Amma haka Bai hana zallan kyanta nunawa ba tana walwali da hasken tamkar wata Wanda yayi dare goma sha bakwai, hannun hagu da dama akwai wassu servant hannunsu dauke da burner wanda ke fidda wani kamshi mai wuyan fassarawa, wani hadadden golden and white centre carpet aka shinfida wanda yayi leading nata har mazauninta, wanda ayanzu aka ajiye kana ganin kujeran kasan anyi barin naira, wa'iyyahh zibillah starki ya tabbata ga ubangijin talikai, zallan white gold ne akayi wannan kujeran dashi Sai farin yadi da akayi amfani dashi don Kara taushi a kujeran Shima kanshi yadin yasha kwalliya da golden paint Wanda akayi wassu design Mai tafiya da hankali, masha'Allah Starki ya tabbata ga ubangijin talikai wanda yayi wannan kyakyawan halittan mai daukan hankalin mai kallo, hakika kowa yasha ruwan jikinshi wassu zai zabga gumi sukeyi , wassu kamar zuciyarsu zai fasahe, ko baa fada ba sun san wannan jinin ZULAIHAT ne, sannan 'yaa ga MUHD KAHTER kwaarjininta da daukan idonta da karfin izzarta yasa su tabbatar da hakan don ance barewa baza tayi gudu danta yayi rarrafe ba. END OF PAGE 15 BY;QUEEN MAHIRAH THE TWO LIGHT {RIKICIN GIDAN SARAUTA BY;QUEEN MAHIRAH ?05 ?February, ?2024 07:43:41 AM Follow this link to join my WhatsApp group and me with comment and react https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
Chapter 18 · 0% Book details