← Book details The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 33

Sashe 2

The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata hadaddiyar mota ce bugun bature mai numfashi da daukan ido da hankalin mai kallon ta, motace wanda sai wane da wane ke hawanta, gudu motar take tamkar zata bar duniyan, daga bayan motan kuwa wata mota ce ke binta cike da zarra da son cin mata, tamkar zasu bi takan wannan bakin mota mai numfashi da daukar hankalin, acikin motan kuwa wata kyakkywar farar mata ne tamkar balarabiya ke zabga gudu cikin tashin hankali, kallo daya zaka mata kasan ba'a cikin hankalinta take ba, gefenta ko wassu kyawawan twins ne wanda ke ta faman zabga kuka da alama yunwa sukeji sai de itakanta mahaifiyar tasu bata da ishesshen nutsuwar da zata iya shayar dasu ayanzu burinta su kubuta daga hannun wayannan azzaluman, cikin muryar kuka da stananin tashin hankali da firkici tace "yah Allah save us from those evil monsters, yah Allah Protect me and my children, ta cigaba da cewa Allah ka stare mu da dukkan starinka ka kare mu....," batare da tagama zancen dake bakinta taba motan monsters din data ambata tabigi motarta da karfin gaske cikin zallan rashin iman hakan yasa tayi loosing control nata suka gangara wani jeji parking nasu motan sukayi, wassu garada guda biyu ne suka fito daga cikin motan kana ganinsu kaga cikakkun yan daba ba ko digon imani a goshinsu, dayan ne ya leka yace "oga sun sheka fa ita da yayan nata," batare da wanda aka kira da ogan yace komai ba phone nashi ta hau ringing ya dauka, yasa a kunnen shi cikin muryanshi na rikakkun yan daba yace "Allah ja zamanin gimbiya komai ya kammala mun sheka su zuwa barza'u, yau zasu yi kwanan lahira" daga cikin wayan akayi maganan da baifi na 30 sec ba, shiko ya amsa da cewa" komi yana kan stari gimbiya," kitttt ya ajiye wayan yace "Labaa??," yes oga "muci star mubar nan kar asamu mastala, wannan yar jagaliyan ba mutunci ne da ita ba, ana samun mastala kadan aradu wannan rocket din baza ta bamu salalan mu ba," wanda aka kira da laba yace" ta isa oga mu sace mata iska kai," "wai awa din," "a ita gimbiyar mana," " laaba baka san waye bakar maciji bane, duk rashin imaninka ta dama ka ta shanye ka, to wannan da kake gani kaho ne kawai bai fito mata akai ba, shima dan taurin da kaan yayi ne, ko balai ya ganta canja hanya yakeyi," "kai ogaa ita wace irin halitta ne aljana ce ita," " Laaba" "naam oga," "to ko a aljanu sai anyi bincike mai zurfi kafin asamu irinta, muci star kar muyi biyu babu" wuffff suka shige motarsu suka bata wuta suka bar gurin, wannan bakar motar kuwa ta cigaba da gangarawa tana kutsawa cikin bishiyoyi bata staya ako ina ba sai wani tafkeken gona mai girma, mai dauke da mutane suna ta faman aiki ko ince kowa da aikinshi, wannan motan gadan gadan tayi kan wani bawan Allah dattijo daa akalla zai kai shekara 50 da yan dauri, yana sanye da fararen kaya kanshi sanye da fula da tasha rawani irin na manyan malamai, fari ne tas kallo daya zaka mishi kasan bafulatani ne gaba da baya goshin shi dauke da tabon sallah wanda ya karawa kyakkyawar face nashi annuri da hasken imani, hannunshi ko sarkafe dana wani yaro da akalla zai kai 9 years yaron yana sanye da farar jallabiyarsa da hirami shima fari hannunsa dauke da wayan wasansa yana nan kamar dan larabawa. ba ji ba gani wannan motar tayo kansu kamar zata take su, cikin ikon Allah ta hadu da wani duste daya sa ta staya chak, ta fara hayaki daya ke nuna motan na iya tarwatsewa in any second cikin tashin hankali mutanen da ke ta faman aikace akikace a gonan sukayo inda wannan dattijon yake shida yaron da hannunsu ke sarkafe dana juna har yanzun kowa da abinda ke fadi, shiko wannan dattijo hankalinsa na kan wannan motan dayake stammanin hadari yayi kuma ran wanda ke cikin motan yana hadari, cikin muryansa mai cike da nutsuwa imani da zallan tausayi da sanin darajan dan Adam, yace wa daya daga cikin samarin dake gurin, "ku fito da wanda ke cikin motan kar ya illata," cikin girmamawa saurayin ya dukar da kanshi yace " tohhh malam," shi da sauran samarin suka karasa jikin motan don bada agajin gaggawa a wanda ke cikinta, ko wani daya dagaa cikinsu bakinsa dauke da addu'an neman stari da kariya, basu sha wiya ba suka bude motan inda suka yi tozali da wannan matar da kanta ke kife jikin sterin motan da alama ta dade da suma, yaran ko har yanzu basu dena wannan kukan nasu ba, cikin sauri daya daga cikin samarin ya kawo mota akasa matar, wannan bawan Allahn da aka kira da malam ya amshi yaran ya shiga front seat na mai zaman banza shida wannan yaron, matar ko tana back seat, nan suka dauki hanya suka fara kusta hanya basu jima ba suka iso wani kayaceccen gari, dan dai dai abinshi mai karancin mutane da yalwar shukoki tako ina, baza ka kira wannan kauyen da ruga ba dan da alama sun fisu wayewa sai de yanayin kan kantar mutanen garin yatabbatar da cewa ruga ce, amma na zamani dauke yake da gine gine na zamani dai dai karfin talaka, hanya suka dauka direct basu tsaya ako ina ba sai wani madaidaicin hospital, abin shaawa dan dai dai kamar mutanen garin, parking sukayi a kofar hospital din ko ince aka bude musu gate din hospital din suka shiga ciki, inda aka tanadar dan parking sukayi parking motar tasu driver ne ya fita ya kira maikatan hospital din suka zo da gado biyu na yara da manya aka sa wayannan bayin Allah aciki, direct emergency room aka wuce da su aka fara basu agajin gaggawa, wani Dr ne yazo cikin girmamawa suka gaisa da wannan dattijon yakuma masu iso zuwa office din babban likitan hospital din ya basu mazauni da abinsha, baa wani dauki lokaci ba saiga babban Dr ya bude office din ya shigo da alama aiki ya kammala, fuska dauke da faraa ya karaso inda dattijon yake yace "Chief Imam yau kaine da kanka," murmushi dattijon yayi yace "likita bokan turai," " malamai kuma magadan annabawa ba," murmushi yayi yace "ya jikin mara lafiyan," "Alhamdulilah zamu ce mun samu nasaran dawo da numfashinta da izinin Allah, yanzu de mun mata alluran bacci dan tana da bukatan hutu, jininta ya hau ta firkita sosai, ni nayi mamaki ma da abin ya staya ahaka ko rauni daya babu ajikinta kuma nayi bincike babu abinda yasameta sai jinin da ya hau kawai," " Alhamdulillah " shine abinda chief Imam yace fuskanshi dauke da murmushin daya bayyana zallar kyanshi sanan yace "yaran fa," zama Dr ya gyara kafin yace "suma suna lafiya, sai de suna bukatar mahaifiyarsu ta shayar dasu suna kuma bukatan wanka" shiruuu Chief Imam yadanyi tukunna kafin ya sa hanunshi a aljuhun riganshi ya ciro wayarshi yayi dialing wani number baa jima ba akayi picking sallama yayi aka amsa mashi kafin yace "Binti ya jikin naki," ta amsa ma shi da "Alhamdulilla Abba da sauki " kafin yace" Allah kara sauki," ta amsa da "amin," yace "kun koma gida ne," tace" aa yanzu muke shiri ," yace "ku jirani ina zuwa yanzu," "tohh Allah kawoka lafiya," kittt ya kashe wayan, Dr ne yace" little Imam yau ba magana ne yana maganan ne cikin zolaya," yaron da aka kira da little imam yace "good morning uncle" morning Faruq, how are you ?," yace "am fine," " and how is your sister," cikin muryansa na yara yacigaba da amsa masa tambayarsa yace "she is pretty fine," "uncle can i ask you something" "why not my dear am listening," "uncle mai yasa babies din nan ke crying sun ji ciwo ne," "aa babban mutum basu ji ciwo ba yunwa sukeji, and they need fresh air," "toh mom nasu tayi feeding nasu mana akaisu gunta haka Khadijtul Islam ma take intana jin yunwa, sai tayi ta kuka ko Jaddi" yayi maganan ne inda oily eyes nashi acikin na Jaddin nasa, da alama karin bayani yake nema gyada masa kai yayi alaman ehh, "toh uncle kaji Jaddi nama yace ehh hurry up and take them to there mom," murmushi Dr yayi yace "there mom is unconcious she is sick," ido little Imam ya waare, yace "ohh i pitty them, toh yanzu mai zaa musu," "sai de abasu milk," inji Dr hannun Jaddin shi ya kama yace "pls Jaddi help them, they are in need of help," murmushi Chief Imam yayi ganin yadda Faruq ya marairaice face nashi, idonshi harda guntun kwalla ahankali cikin nutsuwar sa da yake halittansa ne ya mike staye ya kama hannun Faruq kafin yacewa "Dr akwai milk din ne," da sauri dr yace "ehh akwai," jijjiga kai Chief Imam yayi yace "akawo yaran dakin da Fadima take zata kula da yaran, ita da ummanta," murmushi dr yayi, aranshi yana jinjina karfin imani da tausayi irin na Chief Imam yana da tabbacin tsintar wayannan bayin Allahn yayi kuma ba sune na fari ba mutum ne shi mai son taaimako, "okayy" shine abinda Dr yace wa Chief Imam jagora Dr yamasa zuwa dakin da yake bukatan zuwa, ya kuma bude masa kofa. bai shiga ba sanda yayi sallama ya tabbatar an amsa masa sallaman da yayi, wata siririyar murya ce ta amsa sallaman tana mai masa maraba da zuwa, little Imam ne yayi saurin riga chief imam shiga fuskarsa dauke da fara'a, ya shiga da sauri yayi gurin matar da ta amsa sallaman, wacce baza tafi shekaraa 25 ba a duniy, fara ce kyakkyawa son kowa kin wanda yarasa, kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewa ita din jinin chief imam ne, mahaifiyar little Imam{Faruq}, da gudu ya karasa gurinta ya rungume ta,yace "oyoyo Ummi na" murmushi tayi ta shafa kanshi daya ke dauke da yalwaceccen bakin gashi mai stansti da yawa tamkar na yayan larabawa, breaking hug din nasu yayi yace "Ummi ina innani da khadijatul islama, ina suka je" murmushi tayi ta shafa gefen face nashi cike da kaunar gudan jinin nata kuma mai sunan mahaifinta abin kaunar ta, tace "suna bathroom, innani namawa Islam wanka," "okay," inji little
Chapter 2 · 0% Book details