← Book details The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 33

Sashe 21

The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NIGERIA { KANO} SUHATAJ MUHD HABIBULLAH Ni Queen Mahirah gani cikin waani masha'huriyar masarauta mai girman gaske wacce take tamkar gari. masarauta ce wacce ta staru iya staruwa tasha ginin zamani da shinfidaddun kwalta zaka ranste masarautar ba'a Nigeria take ba stabar yadda ta staru, tasha royal paint wanda ya kara fidda asalin kyanta, mutane nata kai kawo a masarautar wanda na fahinci slaves ne da dogarai kowa da aikin shi wato kowa da abinda yakeyi sai kai komo suke tayi, bayin na sanye da riga da zani blue colour sai dogarai nasu riga da wando shikuma red and green. wata shinfidaddiyar kwalta na hango wanda ta kaini har gaban wani wanda yayi mahaukacin staruwa, kusta kaina nayi ciki nashiga wowwwww shine abinda na fadi, wani hadadden farlo ne wanda ake kira da aljannan duniya mai daukan ido yasha golden and milk furnitures da hadadden chinese carpet da tiles, kato ne farlon gari guda don harda dining a farlon wanda kujerun sunkai goma ko fiyeda haka, kujeru suna da dama a farlon mutane na hango fararen gaske mata da maza sunaa zaune da alama tattauna wa sukeyi mai muhimmanci, karasawa nayi don jiyo wa readers mai ake tattaunawa. Wani farin dattijo ne zaune bisa wani royal sit yana sanye da farar jallabiya wacce tayi matukar amsar sa ta fiddo da asalin kyansa duk da akalla zai kai shekara 75 sai de samm ko ajikinsa hakan bai nuna ba stabar hutu, ba kowa bane face SUHATAJ ABDALLAH wato suhataj mai murabus wanda ya sauka daga karagar mulki ya barwa dansa, gefen damansa shima wani matashin dattijo ne wanda akalla ya kai 55 years har ila ya'u shima girma bata nuna ajikinsa ba, shima fari ne tass mai stananin kama da larabawa don idan ba kasani ba zaka ce balarabe ne sai de bafulatani ne amma ba usul ba, sabida kasancewar sa ruwa biyu wato half cass, wassu kujeru ne guda hudu wanda suke facing wanda Sarki mai murabus { Baba sarki} da kuma Suhataj Muhd Habibullah, daya daga cikin kujerun daya fi kowanne girma da staruwa wata dattijuwa ce ke zaune akai fara tas mai stananin kyau duk da ta stufa amma kyanta samm bai dashe ba zata kai 60 years koma fiye da haka amma sanyin A/C yasaa baka gane hakan ba kowa bane face GIMBIYA NASHWA { FULANI}, uwargidan Baba sarki, dga daman ta kuwa GIMBIYA FADILA ne wato uwargida a wajen Suhataj sai kuma KILISA ZUNNURA {KILISHI} amarya agun Baba sarki, bayan ita sai GIMBIYA SAUDAT itace amaryar Suhataj sai kuma na karshe kanwa agun Suhataj Habibullah wato SARAUNIYA SAREENA. Cikin muryansa mai dauke da nutsuwar da take halittan sa ne yace "tohh Alhamdulillah bayan bude taro da addu'a da akaayi zamu aiwatar da abunda ya kawo mu, wato tattaunawa game da mastalan da ta taso mana ayanzu ina nufin batan YARIMA ABDULFATAH { FAHREEN}, kai staye baza muce ya bata ba tunda shi ba yaro bane sai de muna kyautata zaton wani abu ne ya faru dashi wanda har yasa ya guje mu ya kaurace mana na stawon sati 2, wanda hakan ba karamin tashin hankali bane a garemu kasancewarsa magajin wannan Masarauta mai tarin albarka" dan dakatawa yayi na wani lokaci yaja dogon numfashi kasancewarsa ba mutum bane mai son dogon magana ya cigaba da cewa " ayanzu bamu da tacewa sai de muyi addu'a mu kuma cigaba da bincike har Allah ya dawo mana daashi cikin koshin lfy," Ameen shine abinda suka ce wannan jawabin ba kowa yayi shi ba sai Baba Sarki, basu wani dauki lokaci mai stayi ba suka rufe taron da addu'a kowa ya kama hanyan gabansa ma'ana kowa ya nufi side dinshi. QUEEN FADILA'S { CHAMBER} Gimbiya Fadila ne kishingide a wani hadadden royal bed mai shegen kyau da daukan ido, kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa duk da idonta a lumshe yake sai de hakan bai hana damuwar dake zuciyarta bayyana ba karara, akan kyak'kyawan face nata mai daukan hankali, wanda stayawa fasaltashi da fassara shi bata lokaci ne. cikin husky voice nashi yace "Faddi," ahankali ta bude lumsassun idonta dasukayi jaa ta sauke su a handsome face nashi kallon shi tayi na yan sakanni ta kauda kanta gefe, sauke nannauyan aajiyan zuciya yayi yace " pls Faddi kidena sa daamuwa aranki mana har haka just 2 weeks kiga yadda kika koma duk kin rame ga bp dinki daya ke ta faman hauhawa, do you think what you are doing is right kin manta cewa ba Abdulfatah bane kadai dan da kika haifa bayan shi kina da 3, childrens infact shi ba yaro bane he is 29 years he is matured enough to take care of him self," zuba mishi snake eyes dinta tayi sukayi 4 eyes tace " shekara 20 daya wuce wannan shine abinda ka fadamun kenan game da yar uwata at the end what happened???, i lost her na har abada so tell me mai ne ne amfanin yin hakurin mai ne ne amfaanin kashe kaina da hakuri, i can't bazan iya ba bazan iya juran rashin Abdulfatah ba wallahi you better bring me my son back, in ma exiling nashi kuka yi yadda kuka saba gwara kun yi gaggawan dawo mun da da'na " shiruu yayi na dan lokaci yana kallonta dogon numfashi yaja bai ce kala ba don yasan ko mai zai ce baza ta dauka ba yaga ta hau dokin zuciya, mikewa yayi baice kala ba ya fice daga dakin da kallo ta bishi harya fice wani kuka mai cin rai ta fashe dashi komai yana dawo mata sabo abinda ya faru shekara 20 da suka wuce......... QUEEN SAREENA'S { CHAMBER} da shigowaarta wata sangarcecciyar yarinya ce doguwa fara tas da ita ta iso inda take cike da san garci daga ita sai boomshot da vest ajikinta, kanta ko dan kwali babu sai wani turbune fuska takeyi tana hade rai da sauri ta karasa gurinta tace " my daughter what is wrong with you waani ne ya tabaki " kamar dama jira take tayi magana ta fashe mata da wani kuka wanda kana ji kasan na lalaci ne, itako ta riki ce ta kama ta suka zauna a daya daga cikin hadadden sofa dake farlon " tell me waya tabaki yanzu nayi maganin shi koma waye ne " tace " bahh prince bane nake ta kiranshi yaki yayi picking call din at the end kashe wayan ma yayi gaba daya" ajiyan zuciya tayi ta rungumota " is okayy swerry stop crying prince ba lfy ne shiyasa ya guji kowa, but will see what i can do akan rashin lafiyan, am very sure wani keson rabashi da gida but don't worry i will make sure i deal the hell out of that person koma waye shi , just to make you happy my love" " shiyasa nake kara sonki momcy yanzu bari naje muna da party yau and bazan dawo ba sai 10pm, so sai kisan yadda zakiyi da wannan old man din," tana maganan ne yayin da ta mike akan kafanta " murmushi tayi tace don't worry my baby Fanan just chill up and make sure you look hot and snazzy " " don't worry momcy i will, you know am a snazzy dresser " wani daki dake a cikin farlon ta wuce wanda da alama shine dakinta, Gimbiya Sareena ma dakinta ta wuce tana shiga wayanta ta dauka tayi dialing wani number cikin kan'kanin lokaci akayi picking gaisawa sukayi nadan mintina kafun tace " inaso nasan mai ya faru da prince Fahreen ya bar gida" daga cikin wayan akace "korarsa akayi an mishi kurciya shine abinda muka sani bayan haka bamu san inda yake ba ayanzu" " inaaso a dubo mun inda yake ayaau kuma ina son sanin waya masa hakan " shiruuu yayi na dan wani lokaci kafun yace "akwaai mastaala babba ina storon abinda aka dade ana boyewa yana dab da buduwa, abinda aka bunne yana dab da fitowa cikin rashin sani wanda yayi masa asiri ya hada sa da ruhinsa wato sinadarin rayuwarsa wato mahadinsa " " bannnnn ganehh mai kake nufi bahh " " ina nufin alkawarin da aka dade da dauka yana kokarin hada kansa dazaran hakan kuma ta faruuu tabbasss komai ya kareeeeeee " wani gumi ne yake wanketa tun daga stakar kanta har tafin kafanta bata ma san wayan ya sulale daga hannunta ba, shike nan nata ya kare duk shirin data dade tana yi na stawon 20 years ya tashi a aikin banza, duk shirin datayi na zama surkar Suhataj ya tashi a banza har ta stara yadda rayuwar ta zai tafi matsayin sirkar Suhataj, duk abanzaa kenan inaa bazai yiwu ba sai de ayi mutuwan kosko kowa ya rasaaa....... END OF PAGE 17 BY QUEEN MAHIRAH comment and share plssss THE TWO LIGHT {RIKICIN GIDAN SARAUTA BY;QUEEN MAHIRAH ?Saturday, ?10 ?February, ?2024 12:48:58 AM Follow this link to join my WhatsApp group and shower me with comment and react https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9 PAGE 18 MASARAUTAR SUHATAJ HABIBULLAH { KANO} QUEEN SAUDAT'S {CHAMBER} Zaune take dakin shakatawan ta tana a kishingide a jikin wani tum tum kaayan marmari ne agabanta a jibge bayi nata faman kai kaawo a dakin kowa da aaikinsa, sanarwan da aka faara yi ne yasa bayin suka futa daga dakin, Suhataj Habibullah ne da kanshi yazo ita kaanta tayi mamaki sai de ta boye hakan ganin cewa yau ba ranan girkinta bane duk da ko ba ranan girkinta bane yakan zo don jin ya lafiyarta, sai de baa irin wannan lokacin ba kawad da mamakin tayi tasa faraa a fuskaanta kamar koda yaushe sai yashe hakwara takeyi wanda ya kara mata kyau ya fidda open teeth dinta, mikewa tayi cikin ladabi ta mishi sannu da zuwa sanda ya zauna kafun ta zauna, kallo daya ta masa tasan yana cikin damuwa hannunsa ta kamo cikin salo na kissa da kisisi sina tana murzawa ahankali ta dau lokaci tana yin hakan sanda ta tabbatar ya nustu kafun tace "duk lokacin da mutum ya shiga wani yanayi yayi hamdala Sanan ya gode wa mahaliccinsa masa da yanayin daya stinta kansa, sai ya roki sauki daga mahaliccinsa ya roki Allah ya basa ikon cinye jarabawan, Allah baya taba hada mutum da abinda bazai iya dauka
Chapter 21 · 0% Book details