Sashe 29
The Two Lights Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amsawa suka yi ya shigo ya zauna fuskansa dauke da murmushi, yace "saannunku da bakunta da fatan ban takura muku ba," caraff Fareed yayi ya cafke zancen da cewa, "ko kadan wallahi Jaddi dama muma yanzu muke cewa zamu shiga muyi wa matar gidan godiya" Fudhal dake gefe sai aikin auna mishi harara yakeyi shiko yayi kirmisisi kamar ma baisan yanayi ba, murmushi Chief yayi cike da jin dadi don bai stamman ci haka daga garesu ba yace " ayyahh ai ai sai kunje ba itama zata zo ku da kuke da marar lafiya," "aaa ba'a yi haka ba ai mu ya kamata muje mu duba ta mu mata godiya don ba karamin taimakon mu tayi ba" murmushi Chief ya kara sakewa yace tohh muje" ya mike don musu jagora ya fito waje, Fudhal sai aunawa ishi harara yayi don ba karamin kular dashi yayi ba, murmushi ya sakea yace " kadan ma kagani dani kake wasa wataran ma sai na ka kayi wanke wanke agidan, nan anan zaka gane ni cikakken dan shishigi ne," wani wawan cafka ya kai masa ya kwace ya fice kamar zai kone dan bakin ciki, Fahreen ne ya mike wanda tamkar baya gurin tun dazu sai de yana jinsu stabar miskilanci ne ya hanashi magana, hannunshi Fudhal ya kama suka fito tare suka hango Fareed da Chief har sunyi nisa sai hira sukeyi kamar wanda sukayi shekara 30, da haduwa haka suka bi bayansu har suka iso cikin balcony na gidan directly part din su Mahnoor yayi dasu don da shi ake amfani" a falo sukayi sallama suka samu Innani sai bala'i take ta zazzagawa Barira kamar zata cinye ta danya tana ganinsu ta fara washe baki , " maraba lale sannunku da zuwa" shigowa sukayi suka syugana har kasa suka gaisheta ta, amsa da sunyi niyan zama a kasa ta hanasu suka zauna a sama kan kujera, " Masha'Allah yau larabawa muka samu a gidan namu ai badan kunyi hausa naji ba da bazan yadda ku ba larabawa bane, da har ina kokarin kankaro nawa guntun larabcin ashe ma kuna jin hausa" murmushi duka sukayi amma banda Fahreen da ya saadda kanshi kasa wani mugun bugu zuciyarsa keyi da bai san dalilin taba, Fareed yace " ayyahh kice da mun wahalar dake ai mu muna jin hausa dan acikinta ma muka taashi, dama ma mun shigo ne mu muki godiya Mama mu ga abinci mun gode Allah saka da alkairi ba karamin taimakon mu kikayi ba " murmushi Innani tayi cike da jin dadi tace "laaa ba komai ai bakonka annabinka, kuma Innani zaka ringa cemun haka jikanun nawa suke ce mun shikuma Jaddi suke kiransa dashi" " shike nan Innani kinga mun samu sabin kakanni dama mun bar namu a gida sai ku maye mana gurbinsu'" washe baki Innani tayi tace " aiko ina maraba daku dama kaga kuwa jikanun nawa murdaddu ne kamar sauran yan uwan naka dama dama ma acikinsu Mahnoor ce" mugun razane ya dago da snake eyes dinsa ya zuba mata su jin abinda ta fada, ta tabo inda ke masa ciwo ta fame masa ciwon da ya dade yana fama dashi na stawon shekara 20, jin ta ambaci wannan suna duk da yasan mamallakiyar sunan bata duniyan ayanzu sai de har gobe tana ransa baya kuma fatan cireta daga ransa har abada, Fareed yace " ayyah wai itama jikar kice" " ehh ai su shida ne amma biyu ne kawai suke kasar nan, sauran suna can kasar Iraq su da iyayen su amma in anyi hutun karshen shekara suna zuwa" "shikenan kinga yanzu mun zama tara gani ga Fudhal ga kuma Fahreen " "murmushi tayi tace masha'Allah kuma kamar jikanuna suma haka suke kamar larabawa " "aiko zanso ingansu insamu kanne ko sun fini" dan ware ido tayi tace "sun isa sufa shekaransu 20 nema kuma mata ne ka girme su nesa ba kusa ba " " shikenan kinga na samu kanne sai in hadasu da nawa kanwar duk dama bata kaisu ba ita shekarunta 19 ne, amma ai ba mastala ina zasu dauke ni a yayansu " "murmushi tayi tace da Mahnoor dai baka da mastala amma Khadijatul Islam sai ahankali, don halinsu daya da wannan ta nuna fudhal kullum fuska a hade kamar shanu ba fara'a sai de ayi ta danne dannen waya Noor ce de yar gari" kunshe dariyarsa yayi jin abinda ta fada akan Fudhal wanda ya kara hade fuska kamar gobara ta kama makera " ai ba damuwa Innani zan iya da ita tunda na iya zama da wayannan dodannin, kin san fa su sai ahankali shi wannan baya son magana ya nuna Fahreen, wataran sai ya wuni ya kwana bai kula kowa ba " gyada kai tayi tace "mishkili kenan yafi mahaukaci ban haushi" "shiko wannan ba abunda ya iya sai hancini da hade rai waishi kar a rena shi" ya fadi haka yana nuna Fudhal da yayi kicin kicin, da fuska yanaji yakeji kamar yayi gula a bakin Fareed, Innani tace " Allah mai halitta dukan ku de kamar jika nuna suma kusan haka halayyarsu yake kowa da nasahi salon tabaran da raashin mutunci, shi Sheik fetel halinsu yazo daya da wannan ta nuna Fahreen shiko wannan haalinsu daya da Islam, kaiko kamar kara aka staga stakaninka da Mahnoor, haka nan take sai stokala da neman magana kamar yar bera ta shiga nan ta shiga can, yanzu nema girma ya shigo lamarinta sai ka taba ta take kula ka, amma yanzu a zaman mun nan da anyi karar ta akalla zai kai so 3 ko 5, ita ko Islam ta iya jibgar ya'yan mutane wai ita bata son reni in raashin mutuncin ta ya mosta kamar ta ci babu, sai de ita bata shiga sabgar mutane shiyasa ba'a fiye kawo karanta ba, amma inka kuskura ka shiga nata sabgar zaka san Allah daya ne, don ta iya shuka stiya iri iri," gyada kai yayi yace" kai ashe jikanun naki manyan kaya ne" " wai ahaka ma shi babban yayan nasu baya baya barinsu, yana koda su abinka da soja na sojojin yake musu, zan iya ce maka su renon soja ne dan basun yake ajikin su in suka yi laifi" " ikon Allah shi kuma mai ne ne sunansa" " shi sunansa Umar Faruq wai anace dashi wai Majooo generel ne ko maiye abun nasu sai su turawa" wani karamin daria Fareed ya sake jin yadda ta wani kwaba turancin yace " kina mufin Major General " " san musu ne ma ni sai de su turawan ni baturiyta bace " dan murmushi ya sake yace "MG Umar faruq ba shine sunan nashi " gyada kai tayi tace " laa shakka fiiii haka ne tabbas haka nai suke fada masa" gyada kai yayi yace kamar nasanshi washe baki Innani tayi tace" ehh zaka iya saninshi ai ba abun mamaki bane duk da de ba'a nan kasar yake aiki ba acan Iraq din yake aiki" " ayyah ina jikanun naki " " ai sun tafi makaranta wai suna sarbis ko mai ne ne kadai tambayi Sheik shi ya sani " murmushi ya sake don stabb ya gane mai take nufi don bayau ya saba mu'amala da stofi irinsu ba, yasan mutane da yawa shiyasa ya iya mu'amalantar kowa sabida yana bin muum ayanda yake ne, " ai nasan sun kusa dawowa ma yanzu suna hanya don lokaci yayi" tsaye muke a bakin makaranata muna jiran Auwal yaazo don yau baiazo da wuri ba wani mai kwakwa da dabino Islam ta hango tace "pls muje insiya Sis inaso" bancae mata komai ba muka kama hanya muka je inda yake, muka masa sallama sai da mamakin mu bai amsa ba kallo daya ya mana ya kauda kansa Islam tace " malam sallama fa mukeyi ta fada haka a dakile " mai dibino yace " banga daman amsawa ba lashe money kawai haka kawai na amsa ku lashe mu dan jarin da nake adanawa, sanda fa na sai gonan gadon Innata na samu wannan jarin" hade fuska Islam tayi tace " to ni na tambaye ka ne yadda ka samu kudin jarinka, kuma uban mai muka maka dakake kiran mu lashe money" "ohh rashi kunya zaku mun dama kukan anyi muku tambari ai kan haka, ansanku da rashin kunya ako ina asarar ru kawai masu jan alhakin mutane" cikin stiwa da hasala nace lalle kura tayi sanyi tunda har dan zomo ke jan kunnenta Islam ta cafki maganan tace "ai bama sanyi tayi ba kasa tayi duba wannan karamin alhakin a mu yake wa maganam banza, " ohh tantiranci zaku nuna mun to ni da kuke gani kasungumin tantiri ne don har kwana nayi a kasan gada a lagos" mtswwwww muka hada baki wajen jan wani dogon stuka " kai naka stiyan kadan ne and so what ma dan ka kwana a kasan gada a lagos, wannan ma ai gayyar kazanta ne cewa zakayi kai kasungumin tantirin kazami ne ba tantiri ba" "baku sanni bane lashe money kawai irinku nawa suka llata min jarii, yan iska masun farin fuska sai kuyi ta far farawa mutane ido kuna rabasu da hakkin su" Islam tace "no wonder yanzu na gane ashe banda tantirancin kazantar naka har da na iskanci, to dan Allah kai ya akayi sense naka ya baka mu sa'annunka ne , kaga munyi kama da class dinka see you stupid idiot, da gani ko fatihar sallar nan ma dakyar inka iya kai da kasamu zamu siya abunka ai gaba ta kai ka" cike da shaka yace" ke de kika sani ehhhehh nafi karfinku kurwata ahir dinku karuwai kawai" ware ido nayi nace " kan bazawara mai tallen fura da nono mune karuwan, kazamin banza kai inba kaddara bama ka isa mu sayi abunka banza kawai mai yawo da germs ajiki, dube kafa yohh tohh ko karuwancin zanyi ai mai lasisi zanyi, wallahi nafin kar wulakan cecce irinka marar abunyi, kwarton banza mai kallon 'ya'yan mutane asararre kwasheshshe kawai" "ko made mai zaku ce wallahi kurwata tafi karfin ku sai de kuyi gaba, sai kuzo kuyi ta hana bayin Allah bacci kuna mawa mutane kwalele ku barinsu zakuyi su taba ba" Islam tace " da tun fari abinda ka fada kenan sai kace muna maka