← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya kaɗan sukai suka ƙarasa Ƙofar Gidan Mai Rumfar Kwano mata ne zazzaune ga masu awara nan da masu wainar Gero ga masu Nama driver yayi parking Suka fito Ƙafafun Momi duk sun kumbura sabida zama Hajiya Lubna wajan mai nama taje ta siyo Musu Ita kuma Momi wajan zama ta samu don ta gaji sosai.
Bayan Lubnah ta miƙawa Driver Ƙullin Nashi ta iso wajan Momi suka fara ci batare da tunanin Yin sallah ba.
Seda akai la'asar layi yazo kansu Lubnah ta dakatar da Momi ta fara shiga sannan daga baya ta Kira Momi.

Babban mutum ne zaune akan farin Buzu ya sha manyan kaya ɗakin sa babu wata alama da zata Nuna wa Mutane yana Tsubbu Irin sune masu ci da Buguzun Suna tsubbu ta ƙarƙashin ƙasa a fili Kuma suna Nuna wa jama'a su Na Allah ne.

Seda ya cewa Lubna ta rufe ƙofa sannan ya janyo kwanon sha ya zuba ruwa ya ɗora hannu akai ya tura gaban Momi.

Zaro idanu Momi tayi tare da cewa.
"Ranka ya daɗe wannan Ƴata ce Adawiyyah da Mijina a cikin Ruwa"
Dariya yayi tare da shafe saman Ruwan Hoton su Adaah ya baje.
Kafin yace.
"Kinzo da Buƙata Biyu ta farko a Juya kan Mijinki akan auren Ƴarki Na biyu Kuma a raba shi da Ɗan uwan shi kwata kwata"

Momi ta Gyara zamanta sosai Cike da mamaki tace.
"Ƙwarai Ranka ya daɗe, Ƙawata ta jima tana gayan yadda ka shahara a fannin aiki amman naƙi zuwa sai yau Allah yayi, wallahi yayan Mijina ne ya sakoni a gaba na samu ada na rabasu da Kisisina, To yanzu kuma kwatsam suka Bullo da Maganar haɗin gida da ɗan shi da yarinyata Kuma wallahi ba dan Allah suka shirya hakan ba sedon kwaɗayi da son cin dukiyar Mijina"

Ɗaga mata hannu yayi tare da ƙara janyo kwanan sha ya Ɗora Hannu.
Akai ya kuma tura mata gabanta.
Zare ido tayi ganin Hoton Mahir ÆŠan Hajiya Lubna na yawo akan Ruwan.
Ya kuma janye Ruwan ya maida kwanon sha É—in yace.
"Waye kika gani a ruwan?"
Da sauri tace.
"Yaron wajan Hajiya Lubnah ne Mahir"
Yayi dariya sannan yace mata.
"Kinga wannan yaron shine mafitarki da ƴarki Sabida haka zan baki maganin da zaki zubawa Mijinki a ruwa in ya sha zai baku damar Fito da zaɓinku Ina so bada ɗaukar Lokaci ba Ki zaɓa mata wannan yaro domin Shi aljanu suka Nunan a matsayin Hasken Ƴarki"

Cike da É—unbin mamaki Momi tace.
"Jiya ma sai da nayi maganar Mahir da Adaah take cewa ita Inda Abban ta ya bata zaɓi data Fito da wani saurayin ta shine nace mata Ga Mahir Nan Ɗan aminiyata ashe kaga na faɗa akan Gaɓa Ni wallahi da wancan auren ƙaddarar gwara Mahir Ɗari Bisa Ɗari"
Fuskar Hajiya Lubna ta Bayyana da tsantsar farin ciki bata zaci Komai zaizo da sauƙi haka ba.
Maganin daya bawa Momi Ta É—auka ta bata tasa ajaka, KuÉ—i masu kauri Momi ta Kuma dire masa ta fita tabar Lubna aciki domin suyi sallama.
Zuciya ɗaya Momi ta ƙarasa Mota.

Bayan fitar Momi Hajiya Lubnah ta Matsa gaban Malamin tare da cewa.
"Wallahi ban zaci abin zaizo da sauƙi ba, Ita ce ƙawar tawa dana so na kawo maka ita amman da yake tana da wata Irin Uwa Mai Kafiya ita ce ta hanata Bin malamai wanda Nina fahimci kamar mahaifiyar tata ta gano Wasu al'amurane ko zaka duban?"
Ya janyo ƙasa yayi abin da zaiyi sannan yace.
"Kawai macece mai ibada amman bayan nan babu komai, Kuma Ƙawar nan taki zata baki haɗin kai sosai akan haɗin auren ƴaƴanku sai dai banyi zaton wannan lamarin zai kunno ba da takan Mijin nata zamu fara bi, Sabida mutanan suna da ƙarfin Ibada aikin zaiyi wahalar shiga Jikinsu sai dai ita Yarinyar zamu tura mata nata aikin duk da tana da kafiya da taurin kai"

Hajiya lubna tace.
"Nima bata gaya min ba sai da taga abin yafi ƙarfinta kasan a hankali nake so mubi abin sabida bana son wata Ƙofa da zata nuna cewar da wata manufa Mahir zai Auri Ƴarta, Malam Mijinta Ƴarta kaɗai ya haifa kaga Idan ɗana ya auri yarinyar zamu sami dama sosai tinda Ni yanzu mai gidana ba kamar daba abin kawai fafa ce nake Musu dan bana son ƙawayena suga gazawa ta amman wallahi ranar da Maryam tace min Yayan Mijinta ya turo ɗansa Auren Ƴarta ban Rintsa ba Ni ina nan ina faman yadda zanyi na Ɓullo mata da Maganar su kuma suna can sun Min shigar sauri"
Dariya yayi tare da cewa.
"Aiko furucin data wa ƴarta na Auren ɗan naki aikin dana sa a gabane mai zafi ƙawarki ta fiki son duniya fa Lubna Amman zaku sami alheri sosai In Auren nan ya haɗu sabida naga dukiya sosai"
Shirya yadda zata kasance suka yi har ta Miƙe sukai sallama ta ɗauki Jakarta ta fita.

Jiki a sanyaye ta shiga motar Momi tai mata Murmushi.
"Wato Lubna naji daÉ—in maganganun Malam se naji kamar nayi tsuntsu naga wannan aure ya tabbata"
Lubnah tace "Kayya Maryam baki gani Mahaifin Mahir bai kai mahaifin Adaah ba?"
TsakiMomi tayi.
"Haba Lubna ta yaya zaki faɗi haka bayan Kuma kuna da shi daidai gwargwado ai dama ƙwarya tabi ƙwarya ne wallahi da Adaah ta auri wancan gwara Mahir ɗin sau dubu mayi tuwo na mai na nida ke"

A zuciyar Lubnah Murna take tana fatan haƙonta ya cimma ruwa batun yau take kwaɗayin ɗanta ya Auri Adaah ba sabida su Gaje arziƙin mahaifin Adaah ganinta ta Hanyar auren ne kaɗai zata Iya haɗa kafaɗa da Maryam wadda ta fita jin daɗi ta ko ina.
Momi keta jan Hajiya Lubna da Hira Amman ita Lubna gaba ɗaya bata tare da Nutsuwarta Idanunta ya rufe akan tunanin cikar Burinta tana Jin Kozata rasa Komi nata seta san yadda akai Mahir ya aure Adaah Domin da arziƙi a garin wasu gwara a nasu garin, Don ba tin yau Ni'imar Maryam take tsone mata idanu ba.

Basu ne suka shigo gari ba sai bayan Isha'i a ƙofar Gida suka sauke Momi wadda Hajiya Lubna take ƙara gargaɗinta akan tafa yi amfani da maganin nan kartayi wasa dashi.
Da shigar Momy Gida Room ta wuce tai wanka sannan ta zauna rama sallolin kanta babu tunanin komai ta kwanta a saman gado sai bacci.
Wajan taran dare wayarta dake yashe acan gefe ta soma ƙara ɗauka tai ganin Kiran Abbah Sama sama suka gaisa ya shiga tambayarta Abbakar yazo wajan Adaah rasa yadda zatai tayi seta Amsa masa da yazo kashe wayar yayi ita kuma ta Miƙe da hanzari ta nufi ɗakin Adaah sabida gajiya bata barta taga halin da ƴar tata ta wuni ba.........................

Bayan idar da sallar Isha'i Jidda ta fito daga cikin Gidansu Hannunta É—auke da Jug wanda ta ciko shi da Kunun aya Shi take son kaiwa sabida yau azumi tayi bata gama abincin dare ba.
Tana Ƙoƙarin saka ƙafa a soron Gidan shima yana Ƙoƙarin Shiga Yana kallonta ya ƙaraso Ita kuma ta dakata tana Juya masa Baya........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *008*

A hankali yayi tattaki zuwa gabanta ya jingina da jikin bango yana kallonta ya harɗe hannunshi a saman ƙirjinshi ita kuma sai kuka take babu ƙaƙƙautawa gaba ɗaya ta cika mishi kunne Rintse ido yake yana faman hura iska daga cikin bakin shi, bai san ta inda zai fara da Rigimarta ba, Kuma bai shirya rarrashin Rikincinta ba domin yana jin makaman yaƙin shi sunyi kaɗan wajan tunkarar Rigimar Jiddah.
Sai da tayi kukan mai isar ta sannan ta shiga mai da Numfashi kamar wadda tai wasan Æ´ar tsere a hankali ya Kusanci dab da ita Cikin Nutsuwa Muryarshi tayi Mugun sanyi yace.
"Wai mai aka yi maki ban san waya taɓa min ke ba shiyasa na barki kiyi kukan ko zuciyarki zatai sanyi seki faɗa mini damuwar ki?"
Wani kallo ta watsa mai da dukkan Girman idanunta waÉ—anda sukai jajir kafin tace.
"Ina fatan Allah yasa kunnuwa na ke min gizo daga abin da naji Baba yana faÉ—a maka, In kuma gaskiya suka ji ina fatan nice ba wata ba"
Cikin dake wa ya dube ta.
"To tinda kinji ai shikenan Kinga bakina ya huta da surutu maganin mai laɓe"
Juya wa yake Ƙoƙarin yayi Cike da Jarumta.
Da sauri tai tsalle ta Cakumo shi ta riƙe masa Riga gam tana Huci kamar ba ita ba.
"Wallahi baka isa ba sai ka faɗamin manufarka Dole ne kayi min ƙarin bayanin abin da Kunnuwa na suka ji"
Da kallo yabi hannunta dake Riƙe da rigar shi cije gefen baki yayi yana girgiza kai kallo ɗaya yayi mata tak tai saurin Sakin Rigar tashi yaja tsaki Mai ƙarfi cikin Fushi yace.
"Tin da kema kin soma zama mara kunya zan saita ki kwanan nan karki ga ina sakar miki ki nemi raina ni wallahi ranki zai yi mugun ɓaci, Maganar da kika ji Baba yana min kuma aure ne zasu mini na zumunci sauran ƙarin bayanin Kuma laɓen da kikai sai ya ƙarasa maki shi"
Da sauri ya fice daga gidan gaba É—aya ya barta a wajan.
Chapter 9 · 0% Book details