← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 23

Sashe 14

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya lubna mai zatai in ba dariya ba.
"Kai ƙawata baki da dama wallahi"
sallama sukai suka kashe wayar ranar Momi taji iska mai sanyi na shigarta domin tana jin ta gama da Kaso Hamsin cikin ɗari sauran yaƙin gabanta kuma na Abbah ne don tana jin sai dai duk abin da zeyi yayi amman bafa zata bar wannan aure ba muddin tana da numfashi! tinda har ta sami nasarar shawo kan Adaah sannan shima Mahir ya karɓi abin hannu biyu to fa tana jin sauran yaƙin gabanta ba komai bane.
**

Washe gari wajan ƙarfe goma na safiya Iyah na zaune a falonta gabanta kuma Alkur'ani ne mai girma ta karanta shi, ta shafa ta aje shi a gefe ɗaya, sannan ta juya ta kalli Abbas dake zaune a gefenta yana waya, bayan ya kammala tace masa.
"Abbas kira min Amadu Mijin maryam jiya nayi mafarki marar daɗi ina fatan Allah ya tsare Maryam daga sharrin dukkan abin ƙi"
Abbas ya shiga kiran Abban Adaah a waya wanda sai da wayar ta katse sannan Abbah ya kira.
Cikin girmamawa suka gaisa da Abbas sannan ya miƙawa Iyah.
Abbah ya shiga gaisar da iyah cikin mutunci da sanin ya kamata.
Iyah ta gyara murya kafin tace.
"Amadu yaya batun auren Rabi ne naji kwana biyu baka bugo munyi magana akai ba"
Daga wajan Abbah cikin farin ciki yace.
"Alhamdulillahi Iyah dama yaron namu ne ya nemi da a ƙara masa lokaci sabida ya gama shirye shiryensa, shiyasa ma maganar ta ɗan kwanta"
Cikin dattijantaka iya tace.
"Haba Amadu shifa irin wannan aikin alherin ba a jinkiri wajan aiwatar da shi sabida magauta wannan abu fa duk na cikin gida ne sabida haka, ni zan sa akira min ÆŠan uwan naka ai da lambarshi a wayar Abbas, se muyi maganar data kamata ayi a É—aura auren nan sabida ina gudun kar maganar ta lalace"
Abbah yayi murmushi cikin ƙarfin zuciya yace.
"Da ikon Allah maganar ba zata lalace ba iya"
Sallama sukai cikin mutunci kafin ta umarci Abbas daya kira mata lambar baba, wanda Lokacin yana kasuwa kiran ya shigo sama sama suka gaisa dan bai É—auki murya ba, sai da ta masa bayani sannan ya gane nan suka kuma gaisawa a mutunce sannan ta shiga yi masa maganar data sa ta kira shi a wayar.
Baba ya nisa kafin yace.
"Ni bana gida ne, ina wajan nema amman bari na sa a sako miki lambar wayar sadaukin sai ki masa waya kuyi maganar, kinsan yaranmu sai haƙuri shi yace yafi son yayi komai kamar yadda ake yi a yayin aure to kuma abin ka da marar ƙarfi fafutukar ake yi"
Cikin Nutsuwa Iyah tace.
"Haba haba malam kamar ba gida ba nifa yadda na É—aukaki wannan aure abin sai ya baka mamaki maza turon lambar mijin nawa muyi magana"
Baba ya sa dariya yana cewa.
"To to iya angode da karamci"
Ya kashe wayar tare da miƙawa wani yaro dake gefen shi yace ya turawa lambar data kirashi lambar wayar Sadauki.
Baba yana ta murmushin karamcin iyah wato albasa ce batai halin ruwa ba, inda tayo ruwan da batai yaji ba.
Minti kaÉ—an lambar ta shigo wayar Abbas shi kuma ya kira wa Iyah lambar wadda taita ringing ba a É—auka ba.
Da yake fita zai yi sai ya aje mata wayar yace koda za a kira seta É—auka suyi maganar.

Tai mashi fatan alheri ya fita.

******
An sallamo Jiddah daga asibiti sai dai har zuwa lokacin Ko waya Saadik bai sake yi mata ba, kuma dama bai faɗawa Innah suna asibitin ba bare suje dubiya, Gaba ɗaya ran ummah ya gama ɓaci mita take tana cewa ga baki ga hanci ai ko iyayensa ne sa zo dubiya bare shi.
Duk Jidda tabi ta damu ta ƙara komawa ƴar firit sabida Mitar umma da kuma damuwar rashin Jin Saadik.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma,9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *10*

Zaune yake a bakin rijiya hannun shi riƙe da kofin da Innah ta cika masa shi da koko gefen shi kuma ƙosai ne wanda yake dangwala da yaji yana ci yana korawa da kokon.
"Haba kokai fa nina fi son ka dinga cin abinci sosai koka yi ƙiba kaike nan sai tsayi babu kauri"
Saadik ya ƙunshe dariyar shi sabida gudun kada ya ƙware sai da ya kammala sannan ya ɗago idanun shi ya kalli innah tare da ce mata.
"Haba hajjaju kullum fa sai na fita filin ball na ɗan motsa sabida naga har tumbi ya fara zamarmin ni kuma bana son shi, ni banga rashin ƙibata ba"
Innah tayi murmushi.
"Sanda kana yaro kafi haka fa yanzu duk ka rame sai tsayi ma sha Allah, nidai Sadauki ka dinga zama kana cin abincin ka sosai"
Tashi yayi da kofin da plate ɗin Ƙosan daya kammale ya miƙa gaban kayan wanke wanke wanda Khadija ke zaune tana yi sannan ya ƙarasa wajan Innah ya mata sallama sabida shago zai fita addu'ar alkairi ta dinga yi masa har bakin ƙofa ta raka shi Ɗakin shi ya shiga ya ɗauki wayar shi da makullin shagon da Umar ya bashi ɗazu da Asubah da suka fita masallaci ya rufo ɗakin ya fita.

Yana fita suka haɗu da Baffa mahaifin Jidda shima da alamun fita zaiyi da ɗan sauri ya ƙarasa wurin Baffan suka gaisa ya ƙara masa ya mai jiki.

Saadik na durƙushe baffa yace.
"Malam Abubakar kafa yi haƙuri da halin mata naji duk abin da Saratu tayi maka a asibiti kuma nai mata faɗa ai wannan shashancine dama ina son ma na gana da mahaifinka gwara ko kuɗin auren ne ku kawo asan inda magana ta dosa in yaso ta na kammala karatun nata sai ayi biki ina ga abin da zamuyi kenan Amman kayi haƙuri don Allah"
Saadik ya shafa kai tare da cewa.
"Haba Baffa karka sa damuwa acikin ranka, Ni ban riƙe abun ba ina ga ita Ummah fahimta ce batai ba Allah dai ya shiga lamuranmu gaba ɗaya"
Baffa ya ansa da "Amin"
Saadik ya miƙe yayi hanyar fita daga lungun shi kuma Baffa ya ƙarasa wajan Babur ɗinshi da zai hau ya fita.

Sai da yaje shagon ya zauna sannan ya ga kira da sabuwar lamba a wayar shi, ya É—an shiga mamaki sai da ya sallami matasan da suka kawo masa wani Fayif sannan yabi kiran.

Cikin kamilalliyar muryarshi Yayi sallama, daga ɓarin Iyah ma ta Amsa cikin Nutsuwa.

"Dama naga kira ne É—azu"

Ya faÉ—a kafin yayi shuru yana sauraron abin da za'a faÉ—a.
"Eh nice nasa a kira min mijin da bai kawo min kayan faÉ—ar kishiya ba"
Yadda ta faÉ—i maganar yasa yayi murmushi mai sauti duk da bai fahimci abin da take nufi ba.
"Kakar Rabi ce in babu damuwa ko zaka zo muyi magana"

Ya shiga tunanin wace rabin wace kakar rabin maganar iya ta kuma katse masa tunanin shi.
"Rabi wadda zaka aura mana ƴar ƙanin mahaifin ka amadu"
Sai lokacin ya tina Iyah bata bari ya shiga dogon nazari ba ta ce masa.
"Hotoro zaka zo tsamiyar boka anan gidana yake inda hali ina neman ka yau, In kazo seka min waya Abbas ya ƙaraso dakai"

Jin muryarta da alamun girma ya kamata yasa ya ƙanƙantar dakai tare da cewa.
"In sha Allah zanzo idan anyi sallar la'asar"
Iyah tayi masa godiya ta kashe wayar.
Yaɗan nisa yana tunanin kiran data ke masa kafin ya watsar da abun ya shiga sallamar mutane bashi ya sami kanshi ba sai dab da magariba kawai bari yayi idan anyi magaribar ya je don yadda ya gaji ma bada ban ya mata alƙawari ba da baze iya zuwa ba.
A masallacin da yake kallon shagon shi yayi sallar magariba da yake yau basuyi awon ƙarafe da robobi ba jikin sa tsaf yake sabida haka titi ya ƙarasa ya tari Napep zuwa hotoron da yake akwai go slow saboda magariba ce ƴan kasuwa da ma'aikatan gwamnati na tashi daga aiki bai ƙarasa ba sai wajan sallar Isha'i koda ya sauka ma sai da yayi sallah sannan ya shiga layin da Abbas yayi masa kwatance a bakin layin ya dakata ya kira Abbas wanda ya ƙaraso suka shiga Gidan Iyah.

Cikin mutunci suka gaisa da Abbas sannan ya shigar da shi falon iyah tana zaune a ƙasan Carfet gabanta kuma kwanon tuwo ne da alamun ta kammala cine.
Saadik ya ƙarasa gabanta a nutse ya shiga gaishe da ita.
Iyah ta miƙe da sauri ta shiga wani lungu jim kaɗan sai gata da ƙaton tire wanda ta zubo masa Ruwa da lemo da Fulas ɗin Abinci a gefe.
Zata aje yayi saurin tashi ya karɓa ya aje Dattijuwa ce sai dai Jikinta irin na fulani ne a murje yake babu gigita bare rakwarkwaɓe wa a tare da ita.

Samun gurin zama tayi ta zauna cikin sakewa tace.
"Ango na ga kayan sanyi nan ka sha na sanku sarai da son sanyi ga tuwon amaryarka nan kaci nan gida ne karka ƙi ci dan Allah"
Ruwan ya É—auka ya sha kaÉ—an ya aje.
Tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cikin rashin sakewa.
Iyah ta gyara sosai ta fuskance shi tare da cewa.
"Wato zaka ji wani iri ne nasan sanda na maka waya, dama ba komai bane yasa na kiraka sai maganar auren ku da Rabi, Ni na haifi maryam mahaifiyar Rabi"
Da sauri Saadik ya kalli Iyah ko kaɗan daga kammani har hali ba iri ɗaya bane da waɗancan sabida Ita wannan Tsohuwar akwai ta da mutunta ɗan adam da sanin ƙimar shi saɓanin su.
Chapter 14 · 0% Book details