← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 23

Sashe 4

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaki aure ni Baby karki damu da ina karatu, wallahi ina zuwa kasuwa Ina da halin da zan riƙe ki"
Ya faÉ—a Cikin kashe Murya.
Zuciyarta ce tai rauni, tabbas Inda da dama gwara ta auri Habeeb akan ta auri wancan garan da Abbah yake son Liƙa mata.
Cikin Nutsuwa tace.
"Zanyi tunani akan maganarka Habeeb ka É—an bani lokaci"
DaÉ—i yaji har cikin zuciyarsa.
Da kansa yaja Motar tata seda ya kaita har ƙofar Gidansu sannan ya fita ya bata Key ɗin yana ɗaga mata hannu.
Lumshe idanunta tayi tana Jin wani irin yanayi mai kama da amsuwar tayin soyayyar Habeeb acikin zuciyarta.
Gidan nasu yayi shuru, alamun ya nuna kamar babu kowa room É—inta ta shiga tayi wanka ta saka doguwar riga marar nauyi ajikinta sannan ta nufi Room É—in Momi
************

A gajiye liss ya shiga Gida Lokacin ana Kiran sallar Magarib seda ya wanke jikinsa damma yana amfani da safar hannu wajan awon ƙarafan amman duk da haka seya yi wanka in ya dawo Gida.
Yayi shiri cikin Farar shirt da Baƙin jeans, Ya fesa turare mai sauƙin kuɗi.
Masallaci yaje yayi sallah tare da Baba suka jero zuwa gida yana ƙoƙarin shiga ɗaki Baba ya kira shi.
"Sadauki,Muje muci tuwon dare tare mana"
Ya shafa kanshi kana yabi bayan Baba.

A rumfar Baba suka zauna tare suka ci tuwon da Mahaifin sa bayan sun kammala ya É—auke kwanikan yakai Kicin.
Daga nan fita yayi dan yasan Ba komai bane yasa Baba Yi masa hakan face yana son yaji yadda sukai da waccan yarinyar shi kuma bai san me ze cewa Baban Ba.
Karo suka ci da juna goshin su ya gwaru waje É—aya, dafe goshin nasa yayi........09022260850
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *004*

Zama tayi a gefen gadon Momi tana jiran ta sabida ta jiyo alamun saukar ruwa wanda ya bata tabbacin wanka momi take yi.
Babu jimawa Momi ta fito daga cikin toilet Jikinta rufe da Ƙaton Hijabi ganin haka yasa Adaah fita falo domin ta bawa Momi damar shiryawa kusan awa Guda da fitar tata Momi ta biyo bayanta.
A kusa da ita ta zauna tana jan tsaki.
"Shalele Mahaifin ki yayi min shigar sauri a lamarin auren ki sai dai ni kuma zan nuna masa Nina haifeki wallahi Koda kin Auri yaron nan ba zaki Zauna lafiya a gidan ba har sai Kin kaso wannan ƙaddararren aure na kwaɗayi sabida anga ke ɗaya ya haifa shine za'a ƙaƙaba maki auren dangi"
Taɓe baki Adaah tayi tana Jin zafin furucin kalmar auren nata da Momi ta faɗi kafin tace.
"Yanzu Momy ke kina tunanin zanyi rayuwa da shi? Haba Momy kimin Fatan alheri mana dan wallahi dana aure shi gwara na auri Habib duk da Habib É—in ba wani shigemin rai na yayi ba"

Da tarin takaici Momi tace mata.
"Inda dama mahaifinki ya bayar akan ki fidda Miji ni kaina dana haÉ—aki da Yaron Hajiya Lubna
Maheer amman kina kallo fa umarni ya bamu bawai dama ba wannan makircin Na rasa daga ina ya fito hatta Mahaifiyata anje an faɗa mata ƙarya da gaskiya"
Zaro ido Adaah tayi haÉ—i da saurin cewa.
"Iyah aka faɗama maganar auren nawa? Wayyo! Shikenan yanzu zata ce in baki bari ba Bata yafe ba Haba Abbah yaya zeyi min haka ya rasa da wa zai haɗani sai Ƙasƙantaccen Mutum ɗan talakawa"
Kuka Adaah take mai cike da tsananin ƙiyayyar Auren da za'ayi mata Tin Momy na rarrashinta Har abin ya faskara sai ta zuba mata ido tana kallonta domin duk yanda take zato Adaah ta fita Ƙiyayyar Auren har akai sallar Magarib tana zaune batare data Miƙe Domin gabatar da sallah ba tana ta kuka a wurin Gajiya Momi tayi ta Tashi ta nufi Bedroom Domin gabatar da sallah.

Ana idar da sallah Abbah ya shigo Jin Shashsheƙar Kukanta yasa shi ƙarasowa wajanta ya fasa hawa saman dayay niyya Gyaran Murya yayi tare da Zama a kusa da ita Wanda Itan kuma tai saurin Zamewa ta zauna a ƙasa tana Goge hawayenta.

Da sassauci acikin Muryar Abbah ya dube ta.
"Rabi'atuna kukan mai kike ÆŠiyar Abbanta kome Kike so ki faÉ—a min Kinji bana son damuwarki"

Jin wannan kalmar daya ambata sai taji zuciyarta tayi sanyi ta ƙara Goge sauran hawayenta tare da cewa.
"Abba dan Allah karka aura Min shi wallahi har cikin raina bana son shi"
Tsira mata ido Abba yayi tare da kamewa sosai ya kalleta na wani Lokaci sannan yace.
"Ko kina da dalilin Ƙin Yi mini Biyayya wadda bata saɓawa Allah ba? Ni  Mahaifin ki na zaɓa maki Mijin Aure Kice zaɓina bai maki ba Ko kina da zaɓin ki? sannan Ki bani dalilin Ƙin wannan aure da Kike?"

Daburcewa tayi seda ta aro jarumta wurin furta kalmar.

"Abbah ka duba Gidannan ka duba tsarin shi sannan ka duba tarin dukiyar dake gareka sannan ka duba yanda na taso Sannan Abbah kace zan auri wanda Da ƙyar In yayi karatun Boko ma daga ganin shi yafi kama da ƴan jagaliyar anguwa Abbah na roƙeka karka aurawa Ƴarka tilo ɗaya tal wanda ba tsaranta ba kuma ba ajinta ba"

ÆŠaga mata hannu yayi tare da dafe saitin zuciyar sa.
"Innalillahi wa'innah Ilaihirraju'un"
Ya furta a fili yaushe Rabi'ah ta ɓaci haka yaushe ne ta zama mai raini da ƙasƙanci ga mutane tabbas ba laifin kowa bane face na Mahaifiyarta shiba zama yake a gari ba yawanci In yazo baya daɗewa yake tafiya dalilin daya sa harya ƙauracewa zuwa gidan Yayan nasa kenan sedai ya aika masa da kayan abinci da kuɗi wanda takanas Shi Kuma Baban Chiranci ya aiko masa da cewar Ya daina amsa shiba wannan yake soba Zumunci yake so Yanayin kasuwanci yau ya fita ƙasa kaza gobe ya fita ƙasa Kaza shine silar tarwatsewar Komai, Gudun kar Ƴarsa ta Koyi Wata Tarbiyar yasa ya hanata Karatu a ƙasar waje ashe Gudun Gara yayi domin ya mance yawanci Ƴaƴa suna samun tarbiya ne daga wajan Iyayensu mata.

A fusace ya shiga Kiranta.
"Maryam! Maryam!!Maryam!!!
Da tsananin zafi ita kuma da tsananin sauri ta ƙaraso Falon.

"Alhaji sallah na idar ina addu'a kana kirana da ƙyar na shafa wallahi ka ɗagamin hankali"

"Dole na ɗaga miki hankali Maryama Kin kyauta da tarin tarbiyar da Kika bawa Ƴarki Amman Ina so a daren nan Ki shaida mata waye Abubakar a wajena waye mahaifinsa wacce Irin Rawa mahaifinshi ya taka a rayuwata Kuma ki sanar mata In Mutuwa tayi zan kaita Gidan Mijinta daga nan a suturtata akaita makwancinta Amman Auren ta da Abubakar Babu fashi In har Nine mahaifinta"

Fuww Ya tashi yabar wajan Tagumi Momi ta zabga wato duk yadda take zaton lamarin so yake ya fi ƙarfinta, Mijinta mai son ta da ƙaunarta Ko magana zai mata baya mata ita cikin faɗa sai a hankali sabida Gudun Ɓacin Ranta kasancewarta mai kirsa yanda take wa Alhaji ba zaka ce Wannan matsala zata zo ta shiga tsakanin suba duk yadda takai da kirsarta a Lamarin Auren nan ta kasa dannewa jita ke ba zata iya Gani talaka yazo ya aurar mata ƴaba kuma Ama rasa daga ina zai fito sai daga gidan maƙiyanta dan Momi a duniya bata Ƙaunar Baba da Innah domin sai da takai ga har Gida taje ta Yiwa Innah gargaɗi akan mijinta ada sanda Yake Musu Hidima sosai kafin ta janye shi da Kinibibinta.

Duk da sanyin falon Momi zufa take Adaah kuma na kuka wayarta dake Gefen Kujera ta janyo ta shiga Kiran Ƙawarta Lubnah.

Hajiya Lubna dake zaune Tare da Ɗanta Maheer suna tattaunawa taga wayar Ƙawarta Murmushi tayi tare da cewa.
'Kaga Æ´ar halak kamar tasan zancenta Muke"
Da sauri Maheer yace.
"Mama ki É—aga mana Kiji"
Gyara zama tayi tare da ɗaukar wayar daga ɓarin Momi a gigice ta shiga zayyanewa Hajiya Lubnah Halin data ke ciki.
Tsaki Hajiya Lubnah tayi.

"Ga Hanya mafi sauƙi na faɗa Miki kizo mu fita da tuni wata maganar ake Keni In ba zaki bi malamai akan wannan matsalar ba dan Allah karki sake Kirana"

Tana Ƙoƙarin kashe wayar Momi tace.
"Zani wallahi dole ma naje inya so saina nemi gafarar Iyah In komai ya daidaita Amman ba zan ga wannan abun na bari ba wato in suka aura masa Ita shikenan Komai Namu ya koma Gindinsu Daga ƙarshema su gaje Dukiyarmu tinda Ƴar tawa dana Ke tutiya da ita ta koma cikinsu wallahi Hafsatu ba zata ci galaba akaina ba"

Dariya Hajiya Lubnah ta saki gami da cewa.
"To ai tuni nake faɗa maki karki ga kin sami daula dole sai kin Miƙe tsaye to gashi nan dai Kirsar da kike cewa kina da Ita bata hana Mijinki Botsare miki ba"
Momy ta ɓata rai.
"Keni kada ki faÉ—a min magana mafita kawai nake Nema Amman Ni nasan Kirsata tai Min maganin waÉ—ancan tsinannun"

Taɓe baki Lubnah tayi tare da cewa.
"Yanzu dai turo min wani abun Da zan turawa malam ya fara Bincika mana Halin da ake ciki"

Da sauri Momy tace.
"Baki da matsala bari na sako Miki Kuɗin nan ƙawata Aminiyata ta duk duniya dan wallahi Kinfi min ƴan uwana don basa damuwa dani kamar Ke"
Lubnah tai dariya tare da cewa.

"Karki damu Komai nai miki kaina nayi wa Kin manta taren fa bata yanzu bace, Nima Kin min Komai a rayuwata duk da Mijinki yafi nawa arziƙi Amman baki taɓa yada ni ba Komai naki sai kin saka dani Allah dai yabar mu tare"

Bayan sun kashe wayar Momi ta rarrashi Adaah Ta nufi ɗaki domin sallah, Ita kuma Momi ta zauna tana turawa Hajiya Lubnah kuɗin data Buƙata Bayan Awa Biyu Hajiya Lubnah ta Kira Momi tare da ce mata Lamari fa ya wuce nan dole seta zo sunje tare dan bayani a waya ba zai yuwu ba.
Chapter 4 · 0% Book details