Sashe 12
So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari wajan taran safiya Abbas ƙanin Momi ya kirata a waya bayan sun gaisa yace.
"Yaya maryam dama Iyah ce tace na kiraki gata zakuyi magana"
Jikin Momy a sanyaye ta fara gaishe da mahaifiyarta.
Cikin dattijantaka Iyah tace.
"Maryam ya shirye shiryen aurem Rabin?"
Momi ciki ciki ta amsa da Sai Godiya Innah bata jira cewar Momi ba ta cigaba da yi mata magana kamar haka
"Amadu yace daya dawo za'a ɗaura aure, sabida haka nake son Ki turo Min Rabi tunda Ni ban isa an kawota wajena a matsayina na kakarta ba, To nina na roƙa Ki kawon Ita ta Koyi wasu abubuwan Kona kwanaki Ne kafin tariyarta Kin san Dole sai Ƴarki ta sake halinta ta Koyi tarbiyar Gidan Miji sannan zamanta zai yi daidai"
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Momi ta sauke kafin tace.
"Iyah don Allah Kiyi haƙuri wallahi Nasan Adaah ba zata zo gidan kiba, kinga da nan da wajanki akwai bambanci sannan maganar Aure kuma Iyah babu Ita in sha Allahu Adaah ba zata Auri Wannan Baƙin Mugun ba"
Momy ta ƙarasa maganar tana Haɗe ranta, sabida tasan koda wasa Adaah ba zata zauna wajan Iyah ba duk da ta ƙere Gidan Iyah amman ba wani babba bane tasan ƴar tata akwai Tsurfa kwata kwata bata ma saba da Zuwa gidan Iyah ɗin ba tafi zuwa gidan Ƙawayen ta masu cewa tazo ta kwana haka zata haɗa kayanta taje can Shiyasa sai daga baya ta ganar da Adan cewar bafa ƴan uwanta bane waɗancan Ƙawayene.
To yanzu ma kwata kwata bata zuwa ko ina tinda ta ƙara Girma Daga makaranta sai Gida Ko sunce taje bata zuwa.
Ba tare da mamaki ba Iyah tace
"Nasan zaki faɗi fin haka Maryam tinda Allah ya ara miki dama har Kike ganin dan Ƴarki tazo wajena Ƙasƙanci ne, Nima ina ga bada ban albarkacin haihuwa ba da tuni Kin sakeni Kin ɗauki Duniya da ƴan duniya Kin maidasu dangi Ai shikenan Maryama duk yadda kika gani Kiyi duniya ce"
Iyah ta kashe wayar Jikin Momi na rawa take sake Kira amman ba'a ɗaga ba Inda dane da hankalinta baze kwanta ba har sai tabi Iyah gida ta bata haƙuri amman yanzu da yake hankalinta baya Tare da ita yana can wajan son cikar Burinta bata sake Bi takan Iyah ba ta shiga Kiran Lubnah.
Bayan Lubna ta ɗauka tattaunawa sukai akan zuwan Mahir wajan Adaah.Wanda suka bari akan yau zai shigo da Yammah tana gama wayar Kiran ƙawarta Hajiya Sa'a ya kuma shigowa akan yau ake kawo Lefen ƴar ta, wadda zata auri ɗan sarkin Yola.
Momi dabur cewa ta kuma yi a daddafe sukai sallama da wannan ƙawar tata ta shiga sintiri kai ai bama zata bari Adaah ta auri wannan yaro ba ina sam ai hakan babban Ci bayane a agare ta.
Cikin shirin Makaranta Adaah ta fito doguwar Rigar Material mai mayafi ce ajikinta har Lokacin Fuskarta bata saɓe daga Kumburin kuka ba ta ƙaraso ɗakin Momy domin tai mata sallama Momy ta zubawa Ƴar tata ido kafin tace.
"Kai Allah ya isa! wallahi duk wanda yayi silar Jefaki a damuwa Allah ya saka miki Jibi Yadda kika Koma don Allah Kije ki saka kwalli ki gyara anjima Maheer zaizo wajanki ÆŠan Babarki Lubnah in kuka daidaita Kawai auren ki zeyi mu huta da wancan auren tsiyar"
Dafe gefen kanta tayi,tana rintsa ido tana so taiwa Momi magana amman ta kasa saboda yadda kan nata Ke faman sarawa
Se zama tai a bakin gado da tausayi momi tace mata In bata Jin daɗi ta haƙura da zuwa makarantar.
Kwanciya tayi a gefen gado tai lamo tana Tuna waye ma Mahir Ita yaushe rabonta da shi
Waya tayi wa ƙawarta Husnah akan yau ba zata iya shiga School ba bata jin daɗi Husnah tai mata ya jiki sukai sallama a ɗakin Momy taita Birgima har bacci yayi awon gaba da ita dama rashin baccine yasa mata ciwon kan.
Bayan sallar la'asar tayi wanka tayi sallah tana zaune Mahir É—in ya faÉ—o falon yana faman Kiran Momi kallo É—aya Adaah tai masa ta shaida shi kauda kanta tayi ko kaÉ—an bai mata ba, bama kalar Namijin data ke so bane.
Ita ko Momi Sai Murna take suruki yazo se sawa take ana kawo masa kayan Motsa baki shiko ya wani kafe Adaah da kallo tsaki taja ta bar Mishi falon kuma duk yadda Momi ta Bita ta rarrasheta akan tazo su gaisa da mahir taƙi daga ƙarshe ma seta sa kuka tana cewa.
"Yaya zanyi ne Abbah ya kawon ɗan jagaliya ke kin kawon mai kama da fefe tsakani da Allah wazan zaɓa wallahi Momy bai Yi min ba Koni fa na fisa tsayi Ga shegen rawar kan tsiya gaskiya Momy ki sake shawara Nidai abar min Habib yafi min su dukan su"
Ran Momi ya ɓaci tana gudun kar tirjiyar Adaah ya basu matsala da ƙawarta fita tayi ta bawa Mahir haƙuri akan Cewa Adan bata da lafiya ne ta kwanta.
Da rawar Jiki yace amata sannu zai dawo domin shi kam yaga waje dan baya jin zai iya haƙura da Neman aurenta koda in ya auren ta zata kashe kanta ne sabida wannan Dukiya daya hanga a gidan yasan in ya auri Adaah Kakarshi ta yanke saƙa ai shi du yadda Mamanshi ke kwaɗaita masa abin Bai tabbatar ba seda yazo dan shi bai taɓa shiga Cikin Gidan ba sai yau ko kawo mamarsu yayi to daga waje yake Juyawa.
Tare suka jero da Baba shi ya dawo daga shago baba kuma ya dawo daga kasuwa, Hannun Saadik riƙe da manyan ledojin daya yo musu siyayyar gida.
Har tsakar gida suka ƙarasa Innah tana daka daddawa Saadik ya mata sannu da aiki ya aje Ledojin yana ƙoƙarin ya juya Baba ya kira shi.
Ya dawo gaban baba ya tsugunna Baba yace.
"Sadauki nikam banji kana yin shirin bikin kaba, kaga jiya Amadu ya min waya yana ƙara tabbatar Min da ɗaurin auren ku bayan ya dawo"
Cije yatsa yayi sam ya manta da maganar gaba É—aya Tunanin shi bama ya kan batun
"Baba akwai wasu kuÉ—aÉ—e dana aje akan fara ginina In sha Allah zan kaiwa Aunty Amina a fara haÉ—a lefe sannan batun wajan zama wannan Gidan da yake kallon mu naga masu gidan sun tashi zan wa mai gidan magana in babu wanda ya kama ni Ina so"
Baba ya faÉ—aÉ—a far'a tare da cewa.
"To Allah yayi jagora Ubangiji ya sawa abin albarka yanzu naji batu"
Innah kam dakanta ta cigaba dayi dan ba zata tabbatar da Murna ko takaicin auren ɗan nata ba tana dai yin addu'ar zaɓin alheri kawai.
Tashi yayi tare da nufar É—akin shi.
Har ji yayi kansa na juyawa sabida Tada maganar da Baba yayi.
Ya zira Key a jikin Ƙofa Yaji alamun Kuka a bayan shi da sauri ya juya sukai idanu Huɗu da Jiddah Kwanon abinci ne ta kawo masa tazo Baya ɗaki zata Miƙawa Innah ta aje masa ta kuma gaida Innar wadda tace bata shigo wa kwana biyu tana shirin shiga Gidan taji maganar Baba wadda yake wa Saadik kuma tasan ba akan ta bane to wacece wannan wadda zata aure shi in ba ita ba inko itan ce ai ba shirin yanzu bane tinda taji Baffa yace seta gama makaranta.
Tana ƙara kallon shi sai taji zuciyarta ta karye wani Irin ƙaƙƙarfan kuka na ƙara tawo mata.......
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*009*
Yana sa ƙafafun sa a ɗakin sukai idanu huɗu da ita kallon juna suka shiga yi kafin da sauri ta janye idanunta daga cikin nashi tana mai juya kanta gefe bata sake kallon shiba.
Saiti da Fa'izu suka sami gurin zama suna gaida ummah saɓanin Shi daya ƙarasa gaban gadon yana zubawa inda ta juya idanu.
Tsananin kunyar Umma tasa ya nemi gefe ya jingina kafin yaÉ—an rissuna ya shiga gaisheta.
Ba yabo ba fallasa umman take amsawa fuskarta É—auke da damuwa.
Maganar fa'izu ce ta katse shurun É—akin sabida tinda suka gaisa babu wanda ya kuma yin wata magana.
"Ummah wai me ya sameta har kuka zo asibiti?"
Shuru ummah tayi kafin ta furta.
"Shirme ne kawai irin na Jidda da yarinya yo Allah na tuba namiji goma uba goma ne ni wallahi tin kafin ayi auren nan lamarin nan ya fitar min da ga rai"
Saadik ya rintse ido ya shiga furzar da iska mai zafi, yaji ɗacin maganganun ummah domin tana Babba bai dace tana faɗin irin haka ba, in rai ya ɓaci zuciya ake dannewa bare ma shi bai ga wani abun zafi daya ma ƴarta ba.
"Umma wani abunne ya faru da Jiddan ni duk kin sakani a duhu na kasa fahimtar abin da kike nufi wallahi"
Ƙaramin tsaki taja.
"Wai dan mahaifan Abbakar sunce zasu aura masa Æ´ar uwarsa shikenan ta faÉ—i a soron gidansu ta suma yana kallon Æ´ar tawa ya tsallake ya tafi ya barta a haka ba da ban Allah yasa mutan gidan sun ganta ba da ko mutuwa zatai babu wanda ya sani ni wallahi Jiddah batai zuciyata ba sam danni inda nice da yanzu wata maganar ake ta daban banda abin ta menene na É—aga hankali akan namiji"
Murmushi fa'izu yayi gaba É—aya kunyar abin da mahaifiyar shi tayi yanzu ta gama kamashi inya fahimta ummah tana cikin zafin kishin Æ´arta ne shiyasa take faÉ—in duk maganar data zo bakinta.
"Ummah bai kamata ki dinga faɗin irin haka ba shi aure nufin Allah ne karku bar shaiɗan ya raba alkairi don Allah ku dinga sauƙaƙa zuciyarku"
ÆŠaga masa hannu tayi da sauri Saadik ya fita daga É—akin yana jin ba zai iya jure cin fuskar da mahaifiyar Jiddah ke masa ba kuma baya jin zai iya tanka abin da take faÉ—a sabida yana ganin girmanta.