Sashe 13
So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nura da kansa ya kulle da lamarin shiya iya musu sallama ya baro ɗakin a titi ya hango Saadik yana tafiya sabida saurin da yake har yayi wa Nura nisan da bai tunani ba sai da Nura ya ƙarasa da gudu sannan ya cimmasa.
Tafe suke babu wani wanda yace wa É—an uwan shi wani abun, sanin halin Saadik da Nura yayi in yana cikin damuwa baya magana har sai ya huce damuwar ta tafi sannan yake samun damar yin maganar.
Da ƙafa suka ƙarasa gida a ɗakin Saadik suka yada zango Nura ya zauna a gefen katifa shi kuma Saadik ya shiga banɗaki ya jima aciki sannan ya fito ya ɗauki Jallabiya ya koma banɗakin ya saka sannan ya dawo ya zauna.
"Wai Dagiya meya ke faruwa ne?, gaba É—aya kaina ya kulle kaifa kana da matsala wato mu semu faÉ—a maka duk abin da yake damun mu amman kai zurfin cikin tsiya baka bari a tattauna damuwarka"
Yaja ajiyar zuciya mai ƙarfi saman hancinsa kamar kullum yayi jajir sabida ɓacin rai da damuwa idanunsa ya kaɗa yayi ja ya kalli Saiti tare da cewa.
"Aure baba zai mini, auren dole shine ita kuma take wannan shirmen har take kwanciya a asibiti"
Da mamaki saiti yace.
"Aure kuma kai ban fahimta ba aure da wa kuma?"
Ya lumshe ido kafin ya buÉ—e a wahalce yace.
"Wata yarinya ce ƴar ƙaninshi da sukai alƙawari zasu haɗa auren mu, to abin nima kaina da ka ya zo mini"
Saiti me zeyi in ba dariya ba harda kifawa ganin Yadda Saadik ya haÉ—e ranshi yana cewa auren dole baba zai mashi.
"To kai kam kaji daɗin ka ina ma nine aure a wannan ƙadamin ai sai ka shirya, Allah ya tabbatar da alheri inna fahimta Maman Tafisu taya ƴarta kishi take yi har taso tai abin kunya a gabanmu"
Jingina kanshi yayi da jikin bango ya rintse ido maganganun Ummah sun ƙona masa ranshi, inya fahimta Jiddah ce ta haɗa masa ƙarya da gaskiya a wurinta shine ita kuma ta hau ta zauna ta goyi bayan ƴarta in ko haka rayuwarsu zata tafi akwai matsala babba tabbas!
Nura ya tashi yana masa sallama tare da ce masa gobe zasu haÉ—u dasu Babu a tattauna akan bikin shidai bai cewa Saiti komi ba har ya bar masa É—akin.
Dama ya ɗaura alwala a banɗaki sabida haka sallar isha'i yayi har ya cire jallabiyar jikinsa zai kwanta ya tina bai leƙa wajan innah ba yasan ko yayi bacci sai ta tashe shi yaci abincin dare, sabida haka rigar ya maida a jikinsa ya saka takalmi ya fita cikin gidan.
Da umar suka ci karo zai shiga cikin gidan shima, umar yaja baya yana bawa Saadik wuri don ya wuce, sai da ya shiga sannan umar yabi bayan shi yana cewa.
"Dama Kawu Saadik neman ka nake naje ɗakin ka na ganshi a kulle lissafin kuɗin ƙarfan motar nan ne"
A hankali yace.
"Umar kaje ka huta mu barwa safiya mana sai kace zaka gudu"
Dariya umar yayi yana cewa.
"Gobe ina da Exams a school zan fita da wuri sabida karatu"
Ya É—an juyo yace.
"Ban gane sabida karatu ba, da me kake yi da baka yi karatun jarrabawar ba?"
Umar ya shafa kai tare da cewa.
"Kasan yanayin shagon yanzu anfi ciniki sabida masu cire rodin aikin titi, shiyasa bana son na motsa ko ina, kasan su Usman ba kamar niba in aka ga sune a shagon raina musu hankali ake su tsula kuÉ—i suyi tsada"
Saadik yaɗan ja ƙaramin tsaki.
"Wannan ba dalili bane, kada ka kuma sake jarrabawa tazo bakai karatu ba, ka miƙo makullin shagon ni sai na zauna kai kuma ka dinga zama a gida kana karatun ka har ku gama jarrabawar Allah ya bada nasara, in da wani abun da zasu siya kuma ka sanar dani koka ɗauka kawai"
Umar ya rissuna cikin ladabi yana masa godiya su kam tsakanin su da kawun nasu sai dai addu'a amman abin da yake musu a rayuwa na kyautatawa yafi gaban baki ya furta.
Shiga É—akin Innah yayi shi kuma Umar ya shiga nasu É—akin da yake kusa dana Baba.
Da sallama a bakin sa ya zauna a gefen gadon innah kafin ya jingina kansa ajikin gadon ya zuba mata ido tana lazumi ne carbi mai dubu a gabanta.
Har ya soma bacci sama sama yaji muryarta tana tashin sa.
"Sadauki! sadauki!! bawan Allah wato har yayi bacci"
Ya Mitsika idanun shi waɗanda suka ƙanƙance sabida bacci yana kallonta.
"Innah wai sai yanzu kika kammala kenan na dawo ne shine nace bara na zo muyi sallama sai da safe kuma"
Ya faɗa yana miƙewa yana saka hannu a baki yana hamma.
"A,a sadauki ka daure kaci tuwo mana kada ka kwana da yunwa"
Ya wani zaro ido ya saki ƙaramar dariya.
"Haba Innah so kike dole dai na zama É—an gargajiya, tuwon darannan kumbura min cikina yake amman ke dole sai naci"
Dariyar itama ta saki.
"Dama kai tin kana yaro baka son cin abinci sosai to yanzu bara na dafa maka ruwan shayi kasha sai ka kwanta, Yaya jikin Jiddan?"
Ya lumshe ido ya buÉ—e tare da cewa.
"Da sauki tana ma gaishe ki"
Ya ɓoye mata zuwa asibitin da kuma maganganun ummah sabida su iyaye ba komi ake son faɗa musu na ɓacin rai ba.
"Innah kibar shayin nan zan fita na sayi kankana da lemo na sha na kwanta"
Ta zuba masa ido cikin so da kauna tace.
"To kadai kafe amman mai kankana zata maka maza jeka ka siyo É—in kada dare yayi"
Ya fita yana dariya ƙasa ƙasa tin yana yaro innah ta saba masa da zaman gida in baya gida yana wajan neman kuɗi ko makaranta, bata son yawo ko kaɗan kuma bata son yawan abokai ko su Nurah ma don abokan shine tin na ƙuruciya shiyasa ta barsu tare amman innah macece mai saka ido sosai akan lamarin ƴaƴanta ta gwammace in yana gida ya zauna suyi hira ko girki tare, to hakama ƴan jikokin nan nata Motsi kaɗan tace a duba mata wane takan ce Allah shike da rayuwa dai amman kaima ka kula sosai ka kuma haɗa da yin addu'a.
Sai da ya je ya siyo kankanar ɗauri uku aka masa ya kai tasa ɗaki ya miƙawa Innah leda biyun aiko tana tsakar gida da fitila a hannunta.
"Yawwa dama kai nake jira ka shigo to sai da safe"
Ta karɓa ta juya ɗakinta.
Shima nashi ɗakin ya ƙarasa yayi duk abin da zai ya sha kankanar ya yi brush haɗi da ɗaura alwala sannan ya kwanta nan da nan bacci mai daɗi ya ɗebe shi.
***
Sai da Momi taga fitar Mahir sannan taja ajiyar zuciya ta shiga sintiri a falo kanta ya ɗau zafi gaba ɗaya lamarin Adaah nason bata matsala tana ganin kawo Mahir shine mafi sauƙi da kuma mafita a garesu amman Adaah zata ce beyi mata ba.
Da sauri ta koma cikin ɗakin Adaah wadda take zaune ta zabga tagumi Motsin Momi yasa ta ɗago ta zubawa momi idanu har momi ta ƙaraso bakin gadon ta zauna jiki a sanyaye.
Ta dubi Adaah kafin tace mata.
"Ki nutsu zamuyi magana"
Cikin sanyin jiki tace.
"Ina sauraron ki Momy"
Momi ta gyara zama tare da tattara hankalinta ga Adaah kafin tace.
"Ni ban gane miki ba fa Adawiyyah jiya kinsan wahalar dana sha kuma duk akanki, tafiya mukai tamkar zamu bar garin muka je wajan wani shahararren malami shiya ce mana dole auren ki da Mahir shine mafita sauran bayanan kanki bazai ɗauka ba, amman dai don Allah kada ki watsa min ƙasa a ido duk wannan wahalar dan wa nakeyin ta hatta mahaifiyata fushi take dani duk akanki"
Adaah ta nisa kafin tace.
"Momy nifa fahimtata ce baki ba, wallahi gaba É—aya Mahir É—inne bai yi mini ba kar nazo na aure shi ku sami matsala da aminiyarki"
Momi ta kwantar da murya ganin yadda jikin Adaah yayi sanyi tace.
"Ki haƙuri ki min biyayya, Adaah ki auri mahir kodan mu bawa marar ɗa kunya kinji ƴar albarkar momynta in sha Allah wannan haɗi namu alheri ne abin da nake so dake da zarar abbanki ya dawo ki kafe kice ke Mahir kike so kinga daya bamu dama mu dama a shirye muke"
Adaah cikin rashin madafa tace.
"To Momy zan yi yadda kike so É—in amman nikam bai mini ba"
Momi tayi murmushin cin nasara kafin tace.
"Zai miki ne da zarar kun zauna waje É—aya Allah dai ya maki albarka"
Kwanciya Adaah tayi a cinyar Momy idanunta suka cicciko da ruwan hawaye don dai kawai bata son ta zubawa momin ƙasa a ido ne sannan kuma ta bata tausayi na wahalar data ce mata ta sha shiyasa zata karɓi auren Mahir ɗin.
Sai dare sosai Momi tabaro É—akin Adaah har sai da ta tabbatar ta saki jikinta damuwar da ke tattare da ita ta kau sannan tai mata sallama ta baro É—akin ta koma nata waya tayi wa Hajiya Lubna akan gobe mahir É—in zai iya dawowa su gana da Adaah dama É—azu ciwon kaine ya saka bata fito ba.
Makirin murmushi lubnah tayi tare da cewa.
"Kai haba Maryam wajan jibi ya dawo abarta ta ƙara hutawa shima kin ganshi tinda ya dawo ya ɗagamin hankalina akan ciwon kan nata"
DaÉ—i ne ya rufe momi cikin farin ciki tace.
"Ga wanda ya dace ƴata ta aura wanda ya san darajarta yasan damuwarta harya ji ya damu da damuwarta ba wancan shegen baƙin mugun ba, daya zo ya gargasa mata baƙaƙen maganganu ba, ta mutu ko tai rai shi babu ruwan sa tinda su in da zata mutu ba so zasuyi domin suci gado"