← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashin hankalin ƙaryar da zatai wa Abbah ta shiga domin tasan Ba zai barta Ta fita cikin sauƙi ba Koda kuwa da Jikin Iyah tayi ƙarya A haka ta kwana tana Juyi tare da saƙe saƙen yanda zatai Cikin Ikon Allah ma washe gari da asubah Abbah ya zo mata sallama akan zashi lagos sati ɗaya zai yi wato rashin Jituwar da basa yine bai faɗa mata ba, Itama babu wata walwala tai masa fatan dawowa Lafiya ta Juya ta cigaba da uzirin gabanta.

Sai da taji fitar shi sannan ta kira Hajiya Lubnah Akan fitar tasu da magagin Bacci Lubnah ta miƙe se Lokacin ma tasan Asubah tayi Ta shiga Toilet dan ta kintsa domin a cewarta fitar wuri zasu yi.

Itama Momi Kintsawa ta shiga yi tasan Adaah inta farka taga bata nan ba damuwa zatai ba dan haka data kammala shirin sai ta zauna tana Jiran isowar Aminiyar tata.

Abbah Har ya nufi Airport Sai ya cewa driver ya koma da baya suje Chiranchi tinda akwai sauran Lokaci kafin tashin Jirginsu Suna tafe yana duba hanya don ya kwana Biyu bai zo wajan ÆŠan uwan nashi ba sanda Motar su ta shiga Layin Baba yana Addu'ar fita daga gida sabida sammako zaiyi Abbatuwa wajan sarin nama domin Idan kana son Nama mai Arha sai kayi Asubanci.

Da sauri Abbah ya Ɓalle Murfin Motar ya fita ya ƙarasa gaban Baba ya tsugunna har ƙasa tare da cewa.
"Yaya barka da Asuba"
Baba ya miƙawa Abba Hannu cikin so da ƙauna irin ta Jini Abba ya kama Hannun Baba ya miƙe suka shiga Cikin Gidan.

Da Saadik suka ci karo wanda yake zaune a bakin Rijiya yana Brush cikin sakin fuska Abba yace.

"Malam Abubakar ashe yau zamu haÉ—u barka da asubah"
Sai da ya wanke baki sannan ya shiga gaida Abba wanda yaketa Kallon Saadik cike da son Ƙulla Alaƙar Aure tsakanin shi da Ƴarsa shiko Saadik ɗaki ya wuce ba wata cikakkiyar walwala a tare dashi domin shi Mutum ne mai gudun ƙasƙanci.

Abba yabi bayan ɗan uwanshi yana waigen Saadik aranshi yana Jin amintar bashi Ƴarshi domin Irin Yaron da wiya mace ta raina shi, Har Saadik ya shige Abba na waigen shi Tare da Jin rashin daɗin yanda baya sakewa dashi daga gaisuwa shikenan kwanakin baya babu yanda bai da shi ba akan ya dinga zuwa kasuwa wajan shi Amman fafur Yaƙi Yace shi  Gwangwan ɗin shi ta fiye mishi zuwa kasuwa.

Innah dake fitowa daga Kitchen hannunta Riƙe da Ludayin Miya wanda take Juya Miyar da zatai Ɗumaman tuwon Ƴammakaranta ta saki fuska sosai tana amsa gaisuwar Abbah

"Dama Amadu kana duniya yaushe rabon duniya da ayyaraye rabon dana ganka har na mance fa"
Abbah ya sosa kai Zai bata amsa Baba ya É—aga Murya yana cewa.
"Amadu Rabu da Hafsa yau wasan ƙanin Miji take maka zo mu gaisa Ina sauri"

Jiki a sanyaye Abbah ya shiga Rumfar da Baba ke zaune a nutse suka gaisa dan tsananin Kunya Abbah yama kasa É—agowa ya kalli Baba shiko Baba sai jan Abba yake da Hira koda wasa bai masa maganar komai ba.

Tuwon dawa miyar kuka sai tashin ƙamshi daddawa yake Innah ta shigo masu da shi tare da Koko mai zafi.
"Wato Amadu yasa dole sena karya zan tafi kasuwa, Kin san Hafsatu fa da tuni nakai Titi Amadu wanke hannu a silba Muci tuwo".

Abbah ya É—auki ruwa ya na wanke hannun shi tare da cewa.
"Wato na jima banci tuwon Innah ba kuma ina marmarin tuwon innah kasan Yaya yawanci matan yanzu ba ko wacce bace ta iya tuwon dawa kamar na Innah"

Aiko mai innah zatai In ba dariya ba ta fice tana cewa.
"Kai Amadu kodai zolaya ta kake yi nikam ba zan tsaya jin daÉ—in bakin kaba nayi nan"

Daga shi har Abba dariya suke Suka saka hannu tare da Bismillah suka fara cin tuwon Abbah ya zage yaci sosai yasha Kokon Shi kam Baba bai ma ci da yawa ba Ya tashi ya wanko Hannu Abbah ne yakai kwanukan bakin Rijiya ya wanko hannu shima ya dawo.

Bayan sun zauna Abbah yace.
"Dama Yayah batun auren yaran nanne Ina ganin idan na dawo daga wannan tafiyar sai a ɗaura musu Auren, Batun Hidimar Aure dama nace maka bana buƙatar Komai sai sadaki Zan basu gida sannan don Allah maganar Kasuwa har yanzu Ina Barar yazo wajena Ya nemi abincin shi na bawa wasu ma waje bare kuma nawa"

Baba ya nisa kana yace.
"Haƙiƙa Amadu a baya nayi Fushi dakai sabida yadda ka ƙaurace mini ka daina zuwa inda nake, Amman yanzu na huce sabida haka Bari na kira Sadauki! inya Aminta da tayin naka sai ayi komai a nutse dama bai fara Ginin Gidanshi ba kasan yadda lamarin yake yadai sayi fili anan bayan Gidannan"

Baba ya fita yasa Ummi tayi Kiran Saadik wadda tai shirin makaranta Cikin Blue ÆŠin Uniform É—inta.

"Ke Ummi in kika fita ki kira min kawun ku a É—akin soro"

Ummi ta amsa wa Baba tana nufar soron sai dai ta ga Khadija a raɓe tana share hawaye Ummi tai saurin cewa.
"Ke kuma keda wa kike faman share hawaye?"
Cikin ƙasa da Murya Khadija tace.
"Kibi a hankali kayan kari Innah ta bani na kaiwa kawu Saadik wallahi bakiji ranƙwashin daya Min ba wai banyi sallama ba kuma nayi fa"
Dariya Ummi tayi tana cewa.
"Ba lallai Kinyi ba kuma kinsan halin Kawu su Ya Umar ma shakkarshi suke bare mu"
Ummi ta wuce A bakin Ƙofa tayi sallama sai da yaja aji kafin yace.
"Waye ne?"
Ummi tace.
"Kawu dama baba ne"
Bata ƙarasa ba jin yayi shuru sai can yace.
"Ni kike faɗawa ko ƴan Ƙofar Gida?"
Fahimtar mai yake Nufi yasa taja Labulan ɗakin nashi Ƙamshi da wani Irin sanyi ne suka bugeta daga Nesa dashi ta durƙusa duk Girmansa ya cika ɗakin.

Murya a hankali tace "Dama Baba ne yace kazo"
Ta faÉ—a tana Raba ido sabida yadda yayi mata masifar kwarjini.
Batare daya kalleta ba yace.
"Kice gani nan"
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa daga bakin katifar.

Da.
"To" Ummi ta amsa tana miƙewa ta fita daga ɗakin taje ta sanar da Baba Saƙon sannan suka tafi makaranta Lokacin ƙarfe bakwai da rabin safiya tayi.
09022260850
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *003*

Ita kuma tayi saurin taɓe baki tayi raurau da manyan idanunta waɗanda suka ciko da hawaye ta ƙura masa idanun nata duka tana kallon shi.
Murmushi yake yi har Lokacin hannunsa yana dafe da goshinsa.
"Ni da kika bugawa wannan ƙaton Goshin naki banyi hawaye ba sai ke?"
Hannu tasa ta kare fuskarta tana Murmushi ga hawaye kuma na ƙara zubowa.

Ya ƙara matsowa gabanta ya fita tsayi nesa ba kusa ba hakan ya sa ta ƙara komawa ƴar ƙarama a gabansa.
"To ni yaufa naga takaina Kinga dan Allah zoki rama Duk da nima dai naji zafi"
Dariya ta saki tana cewa.
"Kai kawu Saadik tsokanar kafa nake yi wai ina zaka je Sai ƙamshin turare kakeyi?"
Ta faÉ—a cikin sigar tsokana

Ya tsuke fuska kaÉ—an.
"Dama bana saka turare sai zan fita Hawwa'u?"
Saurin dafe baki tayi tana wara ido.
"Wasa nake maka fa"
Ya É—an kalleta.
"Wai bana ce na soke kawun nan ba su in sun cemin kawu kema sai kice min kawu maza sai wata tazo tana cemin my love ke kina faÉ—in wani kawu"
Ƙafafu ta hau dirawa ta fara Kukan ƙarya Raɓeta yayi zai shiga ɗakin shi dake soro da sauri ta bishi

Ya tsaya a bakin ƙofar ya kare hanyar da zata shiga ɗakin ya tsareta da ido.
"Abinchi na kawo maka na miƙo maka?"
Ta faÉ—a tana Waigawa bayanta tare da É—aukar Kular data zubo masa Abinchin.
Cikin tsananin so da tausayi ya dubeta.
"Bana hanaki kawo abincin nan ba yanzun nan muka kammala cin tuwon innah nida Baba"
Turo baki tayi kaÉ—an.

"Nima Gas ɗinmu ne ya ƙare  seda ummah tayi wa Yayah Fa'izu waya ya kawo mana shiyasa ban kawo maka abincin da wuri ba"

Yadda take maganar Jiki a sanyaye ta É—an bashi tausayi shikam ya rasa wani irin so yarinyar take mishi wanda yake ganin son da take mishi kamar yafi nashi duk da shima yana sonta.
Ya zira hannunshi É—aya ajikin aljihun wandon shi.
"To ni yanzu yaya zanyi da wannan abincin tinda nidai cikina ya ƙoshi"
Yanda yayi maganar ta bata haushi sai kawai ta juya tare da ficewa daga soron.

Beyi gigin bin bayanta ba dan yasan rigima ce zata kaure musu ƙarshe inta saka mai rigima ya karɓi abincin ba iya ci zai yiba inya bayar kuma taji haushi.

Sai kawai ya shiga ɗaki cikin hukuncin Allah yana shiga ana kawo Nepa ya jona cajin ƙaramar wayarsa.

Yana ƙoƙarin cire shirt ɗin jikinsa ƙaramar wayar tasa ta shiga Ƙara alamun kira yana shigowa Bayan ya ɗaga Muryar Abokin shi Nura saiti ta cika masa cikin kunnen shi.

"Wai dan Allah dagiya ina ka shiga ne?"
Saadik ya É—an ja tsaki kaÉ—an.
"Yanzu dai meke tafe dakai ko tambayata ka kirani kayi? kaje shagona baka ganni bane koka zo gida bani nan?"

Saiti yayi dariya tare da cewa.
"To sarkin fushi nai maka magana ne naji shuru, ko baka kunna Data bane yau?"

Takaicin É—azu ne ya faÉ—o masa ya fesar da huci mai zafi.
"Bari kawai Nura wayar ma bata wurina Allah yasa sim É—in yana wannan wayar"
Da sauri Nurah yace.

"Garin yaya matsala ta samu?"
Cikin son kauda zancen sabida shi gwanin zurfin ciki ne yace.
"Ya ake ciki ne kana shagone koka shigo?"
Nura yace.
"Yau na sami cinkoso ne a wajan IBB Road kasan hanyar tamu sai a hankali, Amman gani nan dama Najika shuru ne nace bari na taɓaka kako san yau Za'a Buga wani zazzafan wasa?"
Chapter 5 · 0% Book details