← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 23

Sashe 23

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin farar shadda ɗinkin babbar riga da ƴar ciki ya shirya kansa da hula da agogon silver fari a tsintsiyar hannun shi sai baza ƙamshi yake da ka ganshi kaga ango ya fita ƙofar gida abokan shi suma duk farar shaddar suka sanya irin tashi suka sanya shi a tsakiya suka shiga cikin gida Innah ta saka sabuwar atamfa sai gaisawa take da ƴan uwa ta waya waɗanda basu sami damar zuwa bikin ba.
Tana ganin tawagar su saadik ta saki Murmushi tana kawo hannu ta rungume shi bayan ta kashe wayar, sai ta hau kuka! Saadik ya sa hannu yana share mata hawayen nata su Ya Minau mai za  suyi  inba dariya ba gaba ɗaya yadda Innah tai ya bayyana tsantsar soyayyar da take wa Saadik da ƙyar ya cireta daga jikin shi suka fita wajan ɗaurin auren Ƙofar gidan sune wanda tuni ya cika da mutane sabida Abba yayi gayya Baba ma yayi gayya.
Ƙarfe goma da rabin safiya alƙawarin Allah ya tabbata Aka ɗaura auren.
Abubakar Muhammad MakoÉ—a.
                       Da
Rabi'atu Ahmad MakoÉ—a.

Akan sadaki mai daraja shaidu suka shaida,bayan anyi addu'a tare da fatan alkairi ga amarya da ango Baba da Abbah kowa ya shiga gaisawa da mutanan shi.
Duk yadda saadik yaƙi faɗin ɗaurin auren nashi hakan bai hana jama'a tururuwar zuwa ba haka kowa ya dinga janshi ana hoto sai dai fuskar shi sam babu sukuni musamman daya ga yayyen jidda da mahaifinta sun tawo wajan shi suna yi masa Allah ya sanya alkairi.

Ƙwarya ƙwaryar walima suka yi ba wani waje suka jeba anan ƙofar gida su Babawo suka dinga raba abinci a ledar takeaway wa abokansu wanda shi sam bai da labarin wannan hidima sai yanzu daya ga suna yi.

Sai wajan ƙarfe ɗayan rana jama'ar suka rarragu sannan ya sami keɓancewa da Abbah da baba da wasu daga cikin ƴan uwan su na makoɗa

Su babawo na waje suna jiran shi, shi kuma yana tsugunne a soron wajan mahaifan shi.

Abbah ya dube shi.
"Abubakar Ga amanar Rabi'atu na sabida yau ina jin na sauke nauyin dana ɗaukarwa kaina ko yanzu Allah ya karɓi raina burina ya gama cika don Allah don Annabi ka riƙe min ita amana"
Muryar Abba tai rauni sosai wanda hakan yasa jikin Saadik yin sanyi shima baba nasiha ya dinga masa kafin ya bashi umarnin zuwa gidan iyah shida abokan shi domin su gaisa da Æ´an uwan amarya.

Ba don yaso ba yabi umarnin mahaifin nashi.
Mota suka hau ta wani abokin su zuwa hotoro sabida Baba ya sanar mai acan ake taron da yake yasan gidan kakar tata shiyasa suka tafi can kai tsaye

Da yake motar gida ce sunyi saurin ƙarasawa gidan Iyah nan ɗin ma akwai taron mutane.

Ƴan uwan iya suna ganin tawagar angwaye suka hau buɗa harda masu fesa turare har falon Iyah akai wa su Saadik iso wadda ta cika da farin ciki maɗaukaki.

Suka zazzauna a saman kujerun falon masu tsokana nayi masu hotuna nayi.

Daga ɗaki Aunty mariya taitai da Adaah ta fito wajan angon nata taƙi sai ma kifa ciki datai a kan gado tana rusa kuka.

Da ɓacin rai Aunty mariya take sanar da iya batare da kowa ya kula ba.

Cikin hikima iya ta dubi saadik.
"Kasan kishiyar tawa da kunya taƙi fitowa tin safe ko zaka shiga ku gaisa ne?"
Kanshi a ƙasa yace.
"A,a dama mun leƙo ne mu gaida ku nan ma ya isa"
Ƴan uwan iya ne sukai masa caa akan sai ya shiga sun gaisa da amaryar tashi ba dan yaso ba ya miƙe Aunty mariya tai masa iso zuwa ɗakin Iya.

Ya dakata a bakin kofa batare daya ƙarasa cikin ɗakin ba.

Sautin kukan ta ya cika ɗakin da ƙyar ma idan tasan da shigowar shi.

Miƙewa tai tana rangaji zata shiga toilet sabida fitsarin daya ciyota, haɗa ido sukai da juna atare gaban su ya faɗi.

Kasa taka ƙafarta tai sabida nauyin data mata.

Shi kuma ya tsinci kanshi da kafeta da ido yana hango ramar datai ta ƙara baki idanunta ya faɗa lallai ba ƙaramar tsana taiwa auren shiba kamar yadda shima ya tsani auren nata.

Ƙaramin tsaki taja kafin ta juya da sauri ta shige toilet ɗin ta banko ƙofar.

Murmushin gefen baki ya saki tare da juyawa yabar É—akin.

Sallama sukai dasu iya suka fita zuwa mota suka nufi gida.

Sabida yawan mutane yasa yayi kwanciyar shi a shagon Nura duk da abokan su nata shigowa suna masa Allah sanya alheri.

sallah kaÉ—ai ke tada shi don bai shirya tinkarar gida yanzu ba sabida mutane.

Ƙarfe Shiddan yamma motocin dasu saiti suka nema dan ɗauko amarya suka jeru a ƙofar gidan Innah ƴan uwansu na makoɗa ne mutum biyu suka shiga motar don ɗauko amarya.

Cikin mutunci su Aunty mariya suka karɓi masu ɗaukar amarya wadda sai da akai da gaske sannan ta shirya aka fito da ita tana kuka kamar ranta zai fita.

Har motar ta tsaya a ƙofar gidan Innha Adaah tana kuka Aunty Mariya da wata ƴar uwarsu suka kamata kanta a lulluɓe suka shigar da ita gidan Innah wanda wannan shine zuwanta na farko gidan a  tun  tasowar ta da girman acire ƙuruciya bata sani ba ko an kawo ta amman dai da girmanta wannan ne karon ta na farkon zuwa gidan.

A rumfar innah suka zaunar da ita duk yadda aka so innah tai magana taƙi kanta yana ƙasa ba zaka fahimci abin da yake ranta ba ganin lokaci naja ne yasa suka miƙar da Adaah suka nufi gidanta da ita.

A ƙaramin falon ta saman doguwar kujerar da aka saka guda ɗaya suka zaunar da ita Lokacin daga ita sai Aunty mariya sauran mutanan sun fita a hankali Aunty mariya ta yaye mata mayafin.
Tare da ce mata.
"Rabi'atu kinga dai yadda Allah ya tsara miki rayuwarki ko ba a faɗa miki ba kin san gidan da kika shigo sabida haka ki cire duk wata izza da taƙama ki biyayyar aure in sha Allah zaki alfahari da wannan auren naki"
Ita dai kuka take har Aunty mariya ta gama mata nasihar tabar gidan falon ya rage da ga ita sai halinta.

Idanunta ta buɗe tana bin falon da kallo duhu ne sosai acikin sa don hasken fitilar dake kunne ya fara mutuwa alamun batir ɗinta yay sanyi, ga uban sauro wani irin zafi ke shiga jikinta ware idanunta tai wannan wani irin gida ne acikin wannan gidan zatai rayuwa ita da ko wanki bata taɓa yi a rayuwarta ba amman shine za a kawota wannan gidan wanda ko kitchen ɗinsu na gida bai kai girma ba.

Dunƙulewa tai guri ɗaya ta daddage ta zunduma ihu mai cike da tashin hankali fargaba ɗimuwa damuwa..........

SHIN WACE IRIN RAYUWA ADAAH ZATAI A GIDAN SAADIK?

SHIN WANI IRIN ZAMA ZATAI A TSAKANIN UWAR MIJI? DA KUMA BUDURWAR MIJI WADDA SUKE TSANANIN SON JUNA?

SHIN ZATA RABU DA MAHIR?

WANI IRIN SHIRI HAJIYA LUBNA ZATAI AKAN CIKAR BURINTA?

WANI IRIN MATAKI MOMI ZATA ÆŠAUKA AKAN AUREN?

SHIN AUREN JIDDAH DA SAADIK ZAI YUWU?

SHIN ZAMAN ADAAH DA SAADIK ZAI YUWU WANI IRIN ZAMA ZA SUYI WACE IRIN RAYUWA ZA SUYI ZATA SO SHI? KO SHI ZAI SOTA?

GA DAI ADAAH A GIDAN TALAKA ƊAN GWANGWAN MAI CINIKIN ƘARFE DA ROBOBI YA ZATA SHIN FIƊA RAYUWARTA AGIDAN SHI WADDA ITA TA TASO GIDAN HUTU GIDAN JIN DAƊI WANDA KO WANKI BATA IYA BA BARE SHARA BARE ƊORA ABINCI SHIN YAYA ZATAI DA RAYUWAR GIDAN TALAUCI?

AKWAI TARIN ABUBUWAN DA BAN ZAYYANO BA.

SOYAYYA ƘAUNA SADAUKARWA YAUDARA CIN AMANA DUK ACIKIN LITTAFIN SO DA ALƘWARI TABBAS IDAN GANGA TA CIKA ZAƘI FASHE WA ZATAI BAN CE NA KAI BA AMMAN ZAN ƘAYATAR DA IKON ALLAH.

DUK WANDA YA SAKA KUƊI YA SAI RABO YA RANTSE BAƘON LAMARI AI BAI NADAMA BA, BARE KUMA WANNAN DA AKA ƊAUKI TSAYIN LOKACI ANA SHIRYA SHI DUK DOMIN JIN DAƊI DA FAƊAKAR DA MASOYA KU SHIRYA BIYONI CIKIN TAFIYAR SO DA ALƘAWARI LABARIN SAADIK DA ADAAH DA JIDDAH YANZU MA AKA FARA WASAN DUK SHINFIƊA MUKAI A FREE PAGE YANZU LITTAFIN ZAI FARA RAYUWAR ƳAR MAI KUƊI MAI IZZAH DA TAƘAMA AGIDAN ƊAN JARI BOLA.

WANNAN SHINE ƘARSHEN SHAFIN KYAUTA MA'ANA LAST FREEE PAGE BIYA........

500 NAIRA A SAKAKI A PAID GROUP ZUWA ASUSUN BANKIN 0078174806 STERLING BANK KO KUMA 9022260850 OPAY BANK, GA MASU SON A SAKA SU A GRP KENAN WAÆŠAN DA SUKE SON NAKE BASU A PRIVATE KUMA BA SAI NA SAKA SU A CIKIN GROUP BA SU 1000 NAIRA ZA SU SAKA A BANKIN SAMA, A TURO SHAIDAR BIYA ZUWA WANNAN LAMBAR 09022260850.
NOTE! Idan na kammala littafin nan complt É—in sa zai koma 1000 naira ne kamar koda yaushe idan ina rubuta littafi farashin sa 500 naira ne idan na gama shi kuma complt 1000 naira ne.
WANNAN KARON BEST IN REALITY MUKA TAƁO.
AUTAR MANYA.🌹
Marubuciyar.....
*RABON WANI*
*BAƘON LAMARI*
*RABO YA RANTSE*
*FITAR RABO*
*ÆŠAN MAJALISSA*
*HASKE*
*KOBA SO*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SONTA NAKE BA*
*AUREN BARE*
*DA IZZATA*
*YANKAN ƘAUNA*
Chapter 23 · 0% Book details