Sashe 7
So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Har gaban innah Abbah yazo tare da aje mata kuÉ—i yana cewa.
"Gashi innah babu yawa ban san laifin dana wa yaya ba samsam yaƙi amsar kuɗina, wallahi ason samuna Yaya ya daina fita saida naman nan"
Baba yayi dariya kana yace.
"Wato so kake zuciyata ta mutu kenan ai in kaga na dena saida naman nan Ciwo ne ko Mutuwa amman ba zan zauna na kashe zuciyata ba"
Sai Lokacin Saadik yayi wani basaraken Murmushi tare da cewa.
"Haba Baba in sha Allahu cikin farin ciki da lafiya zaka daina wannan saida naman nan kusa"
Yana faɗa yaja baki yayi shuru shidai Abbah Murmushi yake wani farin ciki yana ƙara baibaye masa zuciyar sa.
Rabon daya sami farin ciki irin wannan harya manta dama haka kasancewa Cikin ƴan uwa yake yasha auna zuwa sai Hajiya maryam ta tare shi da zantuka a haka yake shagala sai yau Allah ya ƙaddara zai shigo wanda rabon daya zo ɗin ya jima ada kuwa Kullum ne in zai fita sai yazo wajan ɗan uwan nashi.
Sallama sukai, Da Innah Da shi da Baba suka fita sai dai Ko a ƙofar Gidan ma Baba yaƙi shiga motar Abbah babu yanda Abba bai da shi akan yazo su aje shiba Amman yaƙi Jikin Abbah ne Yayi sanyi tabbas yasan ɗan uwan nashi ya janye masa ne sosai tinda har yaƙi amsar Dukkan ta yin daya mashi.
Bayan motar su Alhaji Amadu ta tafi Baba ya fita titi ya tari abin hawa zuwa kasuwa yana jin hakan yafi masa Mutunci duk da shi ba zai ce ga wani abu da Amadu yayi mishi ba, Amman Gorin da matarshi tazo har Gida tayi musu shida Innah yasa suka tattare lamarin Amadu suka aje Kuma Allah ne ma ya rufawa Matar Amadun asiri data zo harta tafi Saadik baya gida domin ba zai ɗauki ƙasƙanta Iyayen shi ba Shiyasa daga Innah har Baba basu faɗawa kowa a ƴaƴan suba hatta shi Amadun bai sani ba kawai dai sun kama kansu ne.
Daga cikin gida Saadik ya tokare a gefen katanga.
Ya cigaba da sauraron innah wadda take miƙo masa kuɗin da Abbah ya aje mata.
"Auta ungo waÉ—annan kuÉ—aÉ—en kai da kake da hidima a gabanka Ko wani abun ka rage danni babu abin da zanyi dasu hidimar gabanka tafi tawa"
"Haba innah dan rashin imani a baki kuɗi na saka hannu na karɓa, In da dai ina da Dama da tin yana nan zance kada ki amsa masa kuɗin sa to kin riga da kin karɓa lokaci ya ƙure"
Innah ta zuba masa ido kafin ta janye kuÉ—in ta aje a gefenta kana ta dube shi a nutse.
"Zauna muyi magana Sadauki"
Da yake ita da Baba ba kasafai suke faÉ—in Saadik É—in ba sunfi kiran shi da Sadauki!
Ya nemi guri a bakin ƙofar Kitchen ya zauna.
"Mai yasa kake da sa abu aranka ya kamata zuwa wannan Lokacin , ka rabu da ƙullin ƙanin mahaifin ka a zuciyarka, Wallahi Ba laifin shi bane a rayuwa babu abin da Amadu baiwa mahaifinka ba macece Allah ya bashi marar mutunci a tarihi ban taɓa ganin mace marar kirkin Maryam ba Amman shi ka duba kodaga mu'amalar shi damu kasan akwai ƙauna mai girma"
Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace.
"Nifa innah ba ƙullin shi nayi ba, meze sa na ƙulle shi a raina bayan alhakin kulawa daku ba a kanshi ya rataya ba, kawai Innah bana son ka cika zaƙewa ne a lamarin mai kuɗi, Banyi niyyar bayyana wa kowa ba"
Sai yaja bakin shi yayi shuru ya kasa ƙarasa maganar da yake son faɗi.
Ta zuba masa ido tana son jin sauran ƙarin bayanin.
Ya fesar da zazzafan Huci yana shirin yin magana.
Suka jiyo muryar Faridah tana kiran Sajjad Sai dai tuni shi Sajjad ɗin ya biyo ƙanwar sa Sajidah sun shigo tsakar gidan Innah.
Har rige rigen hayewa cinyar innah suke suna dariya Faridah ma dariyar take bayan tai sallama tana cewa.
"Karfa ku ɓallamin cinyar uwata wallahi sena zane yaro"
Innah tana dariya tace.
"Baki isa kin taɓa yaran nan a gabana ba, keda Hajjo ƴaƴan ku basu da sakewa sam sam bini bini kun daki yaro ku haka nai rainon ku"
Dariya faridah ta saki tana kawowa Saadik dukan wasa kasancewar shine sakon ta.
"Dagiya ba magana ne ka wani cinno baki ko shagwaɓar autan ce ta tashi yau?"
Harara ya ɓalla mata da sauri tai masa gwalo ta shige ɗakin Innah ita kuwa Innah me zatai In ba dariya ba Dama indai Faridah ta zo se sunyi faɗa da Saadik, Kuma dama sun saba tin kan tai aure ita tsokana shi fushi datai masa zai kamata ya zane wani bin sai Baba ya kawo musu ɗauki to ko datai auren bata daina tsokanar shiba shiyasa basa wani shiri yafi shiri da Marigayya Mai sunan Innah Aunty uwani ita ce Mahaifiyar su Ummi wadda ta rasu a garin haihuwar zara shine Yaran nata suke hannun Innah da Baba, Kasancewar Aunty Uwani akwai haƙuri ita ce mai ɗaukar Rigimar Saadik, akaf ƴan uwan nashi.
Farida ce keta ƙwalowa Innah Kira daga cikin ɗaki tana cewa.
"Innah wannan sabon Hijabin naki ne ina so wannan Sabuwar Doguwar Rigar ma ina so"
Tsaki yaja yana cewa.
"Kedai Kinji Kunya wallahi nan gaba kaÉ—an zan soma rufe É—akin Innah duk sanda Kika zo sekin Rabata da kayanta"
Dariya ta saki tana cewa.
"Allah ma dai yasa kafin kazo duniya nazo"
Wannan kalma tana ƙona masa rai tsaki yaja wanda Innah ta fara magana.
"Kinga fito ki tsincen shinkafa tinda Allah ya kawo ki, Dama su Khadija sai ƙarfe Biyu suke shigowa gida sabida makarantar tasu akwai tazara"
Daga ciki farida tace
"Innah yau base kinyi girki ba, Abban Sajjad zai koma Gida Anjima kafin nan Mai aikina ta gama abinci zata zubo mana na faÉ—a masa ma yace zai kawo"
Innah salati tahau yi tana tafa hannu.
"Faridah wannan wani irin sakarci ne Ban hanaki dafo mana abinci in zaki zo ba to ni wannan abin kunyar bada ni ba"
"Innah wallahi shine yake sawa Ko gidansu In zani sai yasa an wa Mama Girki kuma yace dake da mama duk iyayensa ne yau ma Na shirya a makare ne shi kuma yana sauri zai ajeni da senai girkin zan tawo se kawai na barwa mai aiki nace tayi"
Innah tace.
"To madalla zan tuntuɓi shi Mijin naki na kuma haneshi, dammu ma Allah bai hanamu abinci ba"
Dariya faridah tayi sosai kafin ta furta.
"Innah shima ba raina mana yayi ba kawai kyautatawa ce, kuma Innah idan yazo É—in ki tambayeshi wallahi Innah babu yadda za'ai na É—auki abincin Mijina ko wani abun daya kawo Gida nayi kyauta dashi batare daya sani ba Komai zanyi tare da sanin sane da amincewar shi.
Murmushi Innah tayi.
"Na sani faridah Ina dai ƙara gargaɗin ki karki yarda Ki bada Kome ye na mijinki batare da sanin shiba, Kuskuren da yawanci mata suke kenan Kyautar kayan abinci komai ma suna iya badawa dan sunga na mijin sune wannan Kuskurene babba ba'a hana ka bada ba Amman ya zama ka bayar da Amintar sa da yardar sa wannan In kayi hakan babu laifi"