← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da take zama a saman kujerar, lokacin yayi daidai da sanda gabanta yayi mugun faɗuwa hannu ta ɗora a ƙirjinta wanda ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi a hankali ta lumshe idanunta ta buɗa akan shi wanda shi sai murmushi yake yi mata tsintar kanta tayi itama da sakar masa murmushin tana jin wani abu na fusgarta mai kama da so!

Ya matso kusa da ita ya zauna ƙamshin su ya gauraya wuri ɗaya.
A hankali ya miƙo hannu zai taɓa nata hannun sai tai maza ta zame tana yin ƙasa da kanta.
"Yaya jikin naki?"
A hankali ta furta.
"Da sauƙi Alhamdu lillahi"
Cikin ƙwarewa da iya hira da ƴammata yace mata.
"Baby tin jiya ban kwana cikin daÉ—in rai ba, sabida tinanin ciwon kanki"
Cikin sanyin murya tace.
"Ai naji sauƙi fa"
Bata da wani saurayi sai Habib duka shima sau ɗaya ta bashi dama sukai hira ranar daya kawota gida sabida haka sam bata da ƙwarewa a hira da Saurayi tinda ba zancen takeyi ba, sabida haka Mahir ne ya dinga hirar tana amsawa da "Eh" Ko ta ɗaga masa kai bai tafi ba sai bayan magariba har bakin Motarshi ta rakashi.
Ita dai koman ta ya tsaya tin sanda sukai ido huÉ—u da shi bata sake samun sukuni ba, Wani irin sonsa ne taji yana fisgarta.
Sam wannan aibun nashi data dinga gani jiya ya gushe a guje ta faÉ—a falo tana kiran Momi.

Cikin sauri Momi ta fito gabanta na faÉ—uwa zatonta ko wani abun ne sai dai ga mamakinta ganin Adaah tayi tana murna tana tsalle cikin farin ciki tace.
"Momy wallahi yayi min ashe Jiya ban zauna da shi bane, Nikam Ina sonshi Momy har yafi Min Habib sau dubu"
Momi ta rungumeta itama tana murnar tare da cewa.
"Barka Ƴar albarkata"
Nan suka shantake suna hirar yadda zata kaya ba tare da tinanin ayi sallah ba bare azo kan Azkar!

Da maɗaukakin farin ciki Mahir yake tuƙi ya matsu yaje gida ya faɗawa Hajiyarsa yadda sukai da Adaah sabida haka da farin ciki yakai gida shima tindaga bakin Ƙofar falo yake kiran Hajiyar tasa, Wadda itama ta taso tana cewa.
"Me ya faru ne wannan kira haka?"
Kamota yayi suka zauna ya shiga bata labarin yadda sukai da Adaah sosai tai farin ciki da jin yadda komai yazo cikin sauƙi.

Jin hankalinta take yayi mugun kwanciya kuma ta shaida alƙawarin aikin malam daya mata akan lallai sai ya juya hankalin Adaah ya dawo kan Mahir wanda ga shi kuwa tin kafin aje ko ina aikin yaci kwalliya ta biya kuɗin sabulu ƙarashen ne ya rage mata.
******

Washe gari da safe Saadik ya shiga cikin gida wajan Baba yaje suka gaisa wanda yayi shirin fita kasuwa.
Shima bai wani zauna ba ya fita Ƙofar ruwa yaje wajan wani mutumin sa wanda suke harkar Ƙarafe dashi cikon kuɗin da ya biyo mutumin ya karɓa daga Ƙofar ruwa kawai Gidan Aunty Aminah ya wuce rana gatsal a garin haka ya shiga gidan duk Gumi ya gama rufe shi.
A falonta ya zauna suka gaisa Miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki Sai gata da manyan ledoji har guda uku ta aje a gaban shi.
Sannan ta fita kitchen ta haÉ—o masa abinci da ruwa mai sanyi ta kawo masa gaban shi tana zama a kusa da shi tare da cewa.

"Auta sha ruwan sanyi kaci mutuniyar taka shinkafa da wake sai muyi lissafi"
Ya sha saman kanshi tare da yunƙurawa ya fita bakin famfon tsakar gida yaje yayi alwala ya fita masallacin dake layin yayi sallar azahar, sannan ya dawo Sanda ya shiga gidan an kawo nepa saboda haka a falon ya zauna yaɗan tsakuri abincin ya sha ruwa ita kuma Aunty Aminta tana gefen shi tana Gyaran Turaren wutar data zuzzuba a kwalba da yake tana yin su na siyarwa.

Ture plate din abincin yayi gefe yana Jan ledojin data aje masa a gabanshi tsala tsalan atamfofi ne a babbar ledar ta biyun kuma Laces ne É—ayar kuma material ne da mayafai atamfofin zasu kai Turmi Biyar Laces kuma uku material Biyu mayafai Uku.

Cikin mamaki ya É—ago yana cewa.
"Yaya minau gaskiya kuÉ—ina ba su kai asai waÉ—annan kayan ba shiyasa na biyo na kawo maki sauran cikon"
Murmushi tai tare da cewa.
"Ai kaga ma magana ta sauya na kira Hajjo da farida tin ranar da kazo nan mun tattauna shine suka ce kabar kuɗin ka kagan su a gefena na fito maka da shi du wannan kayan Hajjoh ce ta bada kuɗin aka siyo farida tace zata sai akwatina ni kuma zan ƙarasa sauran har kayan kwalliya wannan shine gudun mawar mu dakai auta"
Amaimakon ya yi farin ciki sai ya ɓata fuska yayi kicin kicin tare da cewa.
"Gaskiya ni baku kyauta min ba tayaya ko wacce tana fama da kanta a wannan rayuwar tare da Æ´aÆ´anta sannan kuce zaku Min lefe salon ma a zageni"
Me Aunty Amina zatai in ba dariya ba harda ƙwalla.
"Kai Saadik matsala ta dakai kafiya wannan kaci sunan naka Dagiyar wato kai ba za'a maka komai ba abikinka mu muke hidima kake mana duk da ba'a biki da É—an uwa amman ai kamanci kamata mu haihu kai mana kai mana abikin Æ´aÆ´anmu Kai kaÉ—ai Allah ya bamu Namiji acikinmu In bamu yi maka ba wa za muyi wa?"

Bai ce komai ba sai Miko mata kudin daya ke har lokacin dariya take kafin ta kwantar da murya sanin halin shi in har batai masa dubara ba wallahi ba zai amshi kayan ba sai dai su aje.
"Haba kawu saadik Innah fa tace bayan ka auri Adawiyya zaka auri Jiddah kaga akwai sauran Hidima akanka tinda wannan tamu ce mu mun maka ita kuma Jidda sai kai abin ka da kanka yanzu wannan kudin ka aje ka sai kayan abinci tinda Baba yace Hayar ma har ka fidda kuÉ—in Biyanta to wannan kasai kayan abinci dasu"
Ya mayar da ajiyar zuciya tare da furta.
"Allah ya saka da alheri"
Itama murmushi tai tare da cewa.
"Yauwa ko kai fa yanzu cikin wannan satin zamu kawo kayan Gidan ku in yaso Æ´an uwa suka gama gani sai akai"

"Kinga Ya Minau nifa ko taro Innah baza tai ba karma ku faÉ—awa kowa dan babu wani abu da za'ai a bari in zan auri Jiddah sai ayi taron Æ´an uwa"
Ita dai dariyar rikicin Saadik take  har ya ƙare maganar shi ya Miƙe yana mata sallama zai tafi har waje ta raka shi da yake Gidan nata ba kowa acikin yaran nata ya zaro dubu Uku yace ta bawa yara ta sa hannu ta amsa tana godiya don tasan in bata ansa ba fushi zaiyi ya tafi.
Daga gidan ya minau shago ya wuce aiko ya sami masu jiran shi sabida gaba É—aya bai buÉ—e shagon ba yau sakamakon Umar na hutun karatun jarrabawa Shiyasa ya dakatar da Usman yace Shima ya huta a gida sabida umar ya fisu Hankali In suka zauna za'a iya samin matsala.

Bayan buɗe shagon ya shiga sallamar Cincirindon matasan dake jiran shi wasu sun kawo rodi ne wasu ƙarfe wasu Robobi bai sami kan shi ba sai da akai la'asar ya kulle shagon ya tafi sallah bayan ya dawo ma sallamar mutane yake har akai magariba sannan ya kulle ya nufi gida.
Ya dakata a bakin wani shagon awo dake gab da layin su ya sai shinkafar tuwo da garin tuwo aka zuba masa a ƙatuwar leda ya ƙarasa gida.
Bai shiga ciki ba a ɗakin shi ya aje kayan daya sayo yayi alwala ya tafi masallaci da yake jikinsa babu datti domin idan zai awon ƙarafe yana amfani da safar hannu ne ta leda sannan kuma yawanci ma yana aje ƙananun kayan da yake sakewa in yana shago duk da yau yaje amakare kuma bai amfani da kayan da yake sawa ba hakan bai saka ya ɓata na jikinshi ba.
Daya dawo daga masallaci wanka yayi ya saka jallabiya Mai ruwan toka ya fesa turare mai sauƙin ƙamshi ya ɗauki ledar Shinkafar tuwon da gari ya ƙarasa Cikin gidan.

Muryar Aunty Hajjoh yaji tana cewa innah.
"To Innah ga autan naki nan hankalin ki sai ya kwanta"
Da sauri innah ta fito daga rumfarta tana cewa.
"Kaiko sadauki ina ka shiga aikena tara da abinci shagon ka baka nan"
Kamo hannunta yayi suka zauna a saman tabarmar rumfar tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalin ki innah ba zan ɓata ba ina gidan Ya Minau muna lissafi bayan naje kasuwa na karɓi kuɗi can na wuce"
Innah ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da furta.
"Alhamdulillahi ina ta kiran wayarka sai wannan baturiyar taita yarika kala kala"
Sayyidah mai zatai in ba dariya ba Khadija nayi ummi nayi Juyawar daya yi ne suka daidaita kansu.
Aunty Hajjo itama dariyar take tare da cewa.
"Wato shiyasa sayyidah tace Min Ummi don Allah kije dani gidan Innah naci dariyar soyayyarta da kawu saadik wai niko Hajiya Innarmu zaki bar ɗanki ya tare a wani gun wannan ƙauna haka"

Haɗe rai saadik yayi tare da tashi zai fita dama ya saba jin tsiyar Yaya Hajarah duk sanda tazo gidan sai yaji haushin tsiyar data ke mai ya fita ya bata gu Da sauri Innah ta riƙo hannun shi.
"Kinga Hajara ki fita daga idanuna zoki haɗa ƴarki ku bar min gida wallahi bamai ɓata min ran sadauki"
Ƙunshe sauran dariyarta ta yi tare da miƙewa ta basu guri domin tasan akan saadik zasu iya rabuwar faɗa da innah.

Tashi tayi bayan barin gun da su Aunty Hajjo sukai.
Ta shiga kitchen ta É—auko masa abinci harda ruwan shayi a fulas
Chapter 16 · 0% Book details