← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 23

Sashe 15

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta nisa kafin ta cigaba da magana.
"Munyi magana da mahaifin ka É—azu yace kace masa sai ka kammala shirin ka kafin ayi batun aure ban da abin ka naga duk gida ne mene zai saka ka É—aga hankalin ka, kaga duk abin da kake da shi kayi fatana Allah yasa inga wannan aure da raina da lafiya domin shine babban burina"

Saadik ya shiga mamakin furuncin nata kafin ya maida ajiyar zuciya yace.
"Haka ne Baba, amman kin san lamarin yadda ya zo minne duk da bai zo min cikin shiri ba dama abin da Allah ya hore min shi zanyi kuma na gode da karamci"

Iya ta kalle shi wani farin ciki na ƙara ninkuwa a zuciyarta tabbas Jikarta tai sa'ar miji.
"Kayi haƙuri da duk abin da zaka gani ko kaji nina haifi Maryam nafi kowa sanin halinta, Kuma dukkan wani hali nata ƴarta rabi shita kwafe sabida haka don Allah don Annabi ka zama namiji ka tsaya sosai akan tarbiyar Rabi domin daɗin dana ji da Allah yasa jininta zata aura ba bare ba, sabida haka kayi haƙuri ka rungumi wannan aure ina da yaƙinin alheri ne in sha Allahu"

Ƙasa yayi da kanshi yana jin ninkin sassaucin zuciyarsa na game da damuwar auren kafin yace mata.
"In Allah ya yarda Babah Nagode Allah ya ƙara girma"
Iyah ta miƙe tare da cewa.
"ÆŠan ci tuwon tsofi bari na baka guri"
Ruwan kaɗai ya ƙara sha ya saka hannu ya rafka tagumi, Minti kusan goma Iyah ta dawo wurin yana ganin ta dawo ya miƙe yana mata sallama Dubu biyu ya zaro ya aje mata tare da cewa taci goro har bakin ƙofa ta bishi tana masa tsiyar baici tuwon ta ba shidai Murmushi kurum yake harya fita daga gidan.

Wani irin ƙima da darajar tsohuwar na ninkuwa a ranshi tabbas! ya ga karamci da mutunci a tattare da ita kuma daga gani macece data san karamci.

Ya jima a titi kafin ya sami abin hawa aiko kira ne rututu Innah ke masa.
Sai da ya shiga abin hawan ya zauna sannan ya É—auki wayar tata tambayar shi take a ina ya tsaya ta aika shago akai masa abinci baya nan.

"Innah ina abin hawa ganinan In sha Allahu"
Ya kashe wayar ya jingina da ƙarfen napep ɗin yana nazarin maganganun tsohuwar can wato sudai mutan da suna da kirki da karamci bai taɓa ganinta ba sai yau amman jinta yake kamar mahaifiyar Innah sabida abin da tai masa.

Har ya ƙaraso gida yana ta Murmushi shi kaɗai a babban titi ya tsaya yayi siyayyar kayan shayi sabida Ya gaji da cin ƙosai da Kunu koda koko gaskiya gobe shayi za'ayi.
Yasai Liptom yasai madara da su sugar ya tsaya yasai ƙwai tare da ƙaton burodi.
Sauran canjin daya rage ya sayawa Innah kifi karfasa yasan tana son karfashe musamman wanda ya kwana domin maggi yafi ratsa shi idan ya tsumu.
Sai daya kammala siyayyar sannan ya ƙarasa gida ya shigo lungu suka haɗu da Babu, wanda shima dawowar shi kenan gaisawa sukai babu ya shiga gida shima ya ƙarasa gida sabida su Babu a farkon Lungu gidan su yake gidajen su na kallon na juna dana su Nura saiti su kuma su Saadik nasu gidan a ƙarshen lungun yake akwai tazara a tsakanin su.

Yana ƙoƙarin shiga gida yaganta a raɓe a bakin ƙofa yi yayi kamar bai ganta ba.
"Kawu Saadik"
Ta faɗa murya a shaƙe.
Juyar da kai yayi zai shiga soro tayi saurin tare gaban shi.
"Don Allah karka shiga ka bari muyi magana"
Cak ya tsaya tare da zuba mata ido.
"Dan Allah kawu Saadik kayi haƙuri da abin da ummah ta gaya maka nasan shiya ɓata maka ranka"
Shuru yayi mata.
"Allah fa nace"
Ta faɗa tana yin ƙasa da kanta gaba ɗaya jikinta yayi sanyi na yanayin shi data gani.
"Kin gama zan shiga gida kin tare min hanyata"
Ta langwaɓar da kanta.
"Kawu Saadik Allah fa nace maka"
Shuru yayi mata.
"Kawo kayan na riƙe maka mu shiga gidan"
Nan ma yayi mata banza.
"Lahh kawu saadik ledar burodin ta fashe, kawo na riƙe kada ya faɗo"
Shuru yayi mata ganin hakan yasa ta fashe da kuka ta durƙushe a wurin ta dinga zunduma masa ihu! ganin zata jawo hankalin mutane kansu yasan ya yayi gyaran murya tare da cewa.
"Kinga in magana zaki ƙara jawo min dan Allah jeki bana neman duk wata magana mai zafi a yanzu ki barni da abin da yake damuna"
Share hawayen take tana cewa.
"Kawu saadik yaya zanyi na cire soyayyarka a zuciyata duk yadda naso na rabu dakai kamar yadda Umma ta faÉ—a min na kasa duk rufe idon da zanyi hotonka ke yawo a idanuna"
Ya jingina da bango.
"To kibi maganarta mana, ai shawara ta baki kinga tin kafin ki mutu azo ana nine sila gwara kin kama kanki"
Sai ta É—ago ta kalle shi da kyau.
"Nike nan nake haukana ka dena sona sabida ka sami wadda ta fini ka sami Æ´ar masu kuÉ—i ko?"
Maganar data faɗa ta ƙarshen nan ita ta karya masa zuciya wato ko yayi niyyar yi mata ƙaura inta masa laifi akwai abubuwan da in tayi kota faɗa masa yake sawa yayi saurin janyewa daga ƙaurace matan.
"Hauwa waye yace maki Æ´ar masu kuÉ—i ce?"
Ta tashi tsaye ta na turo baki.
"Zancen duniya yana ɓuya ne"
Yayi murmushi mai ciwo.
"Baya ɓuya kam amma nayi mamaki kuma in tunanin ki haka ne to kinyi tunanin ƙarya domin ni har yanzu banga kuɗin da zai sa na auri mace ba kawai shi aure nufi ne na Allah"
Hawaye ta goge.
"To yanzu ka daina fushin dani?"
Ya tsira mata ido.
"Ki nutsu Hawwa wannan shirmen naki ki daina ta yaya zaki je wurin ummah ki haÉ—a min sharri ni yaushe na tsallake na barki a sume?"
Ya faÉ—a yana zuba mata girman idanun shi.
Ƙunshe fuska tai a cikin hannayenta.
"Kayi wa mai so uziri man kawu"
Murmushi yayi.
"Shine aka ce shi mai son yayi ma masoyin sa sharri yanzu fisabilillahi haka mukai dake"
Ta tura ƙaramin bakinta gaba kaɗan tare da cewa.
"Bana baka haƙuri ba ni ya kamata ma a rarrasa da aka ma kishiya amman ni na zo biko Nikam wannan mallaka da kama zuciyata har tai yawa"
Bai niyyar dariya ba amman seda ta sa ya dara.
Da sauri ya faɗa soro yana ta dariya shirmen jidda wani bin mamaki yake bashi in tai wani abun kamar ƴar fari koda yake akwai ƙuruciya a tare da ita.

Juyawa Jidda tayi don ba zata iya binshi gidansu ba tana jin kunyar suman data yi da abin da ta dinga faÉ—a akan shi a gaban Innah da baba sai yanzu abin ke bata kunya ita É—aya inta tina seta rufe fuska tana murmushi.
SaÉ—af saÉ—af ta shiga gida ta faÉ—a É—aki domin umma bata san ta fita ba sai dai duk abin da tayi umma na kallonta ta window É—aga murya umma tayi tare da cewa.
"wallahi jidda kin bani kunya na dena shiga tsakanin ki da Abbakar in sha Allah duk abin nan da kukai amman saida kika tare shi ai da fitarki da shigowarki duk ina lura"
Ƙunshewa tai a ɗaki kamar ruwa ya cinyeta har umma ta gama ɓaɓatunta daga ƙarshema baccine ya ɗauketa.

Cikin gida ya shiga har lokacin dariyar yake sai da ya ƙarasa tsakar gidan sannan ya daidai kansa duk su innah na baje a tsakar gida suna shan iska.
Yayi sallama su ummi suka shiga yi masa sannu da zuwa.

Ya kalli salmanu dake kan rijiya yana cin tuwo.
"Kai yau ina ka shiga?"
Fuska a É—aure yayi maganar.
Salman ya shafa kanshi.
"Kawu munje kallon kilisa ne"
Girgiza kanshi yayi bai ce komi ba ya ƙarasa kusa da Innah sai dai jikin salman yayi sanyi sanin shuru Kawu Saadik ba alheri bane ƙarshe zane shi zai sa Umar ko Usman suyi da safe sabida ya hana shi zuwa kallon Kilisa abin da yasa ya faɗa yasan inya masa ƙarya zai bibiya shiyasa kai tsaye yace masa ga inda yaje.

"Ai salmanu kamar mai kunnen ƙashi yake Allah dai ya shirya mana zuri'a sam baya jin magana"
Inji innah.
Saadik bai ce komi ba ya aje ledojin hannun shi tare da ma innah sai da safe.
Gaba É—aya agajiye yake ne.
Yana shiga ɗakin sa,salman ya biyo shi da kwanikan abinci ya aje daga bakin ƙofa sannan ya tsugunna yace.
"Kawu don girman Allah kayi haƙuri"
A hankali yace

"Jeka salman Bording É—in maza kawai zan nema maka wallahi na gaji da jamin magana da kake yi"
Sum sum salman ya miƙe jiki a sanyaye yabar gun yasan kawun nasu baya son naci.

Sai da yayi wanka sannan yaci abincin taliya ce jallof mai ruwa ruwa yasan innah shi kaÉ—ai taima sabida sanin aminin taliyar ne.

Ya jima bai bacci ba dan sai da yayi nafila ya daÉ—e yana addu'a akan lamarin auren nashi sannan ya kwanta.

*********

Yau gidan na Momi ya kacame Maimuna sai shiga take tana fita tsakanin Kitchen da dining ana shiryawa Mahir abinci momi sai nan nan take da Adaah gudun kada ta Botsare anci sa'a tai wanka ta shirya ta zauna zaman Jiranshi wajan Magariba ya ƙaraso gidan a babban falon da maimuna ta shirya masa abinci Momi ta sauke shi sai da Ya cika cikin shi da ci da sha sannan Adaah ta miƙe ta isa wurin shi yana zaune a saman Kujera ya wani harɗe ƙafa........
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *11*
Chapter 15 · 0% Book details