← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komai na momi ya tsaya cak sai faman zage zage take kuma tace ba zata taka ƙafarta gidan bikin ba Hajiya lubna tafi momi shiga tashin hankali data ji maganar amman data tina zagon ƙasan datai sai taji bata damu da auren ba tasan dole adaah zata fito ɗanta ya aure ta, domin ba burin ta auren adaah ba burinta dukiya.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma 9022260850 Opay bank, Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *13*

Da tsananin ɓacin rai yake shiga cikin gidan nasu, yadda ya tarar da mutane a tsakar gidan nasu suna ta ɗaga kayan cikin akwatinan abin ya bashi mamaki ba kaɗan ba.
Ya tokare a bakin rijiya tare da zuba hannayen shi a saman ƙirjin shi sabida yadda ranshi ke ɓace baya tinanin ma na tsakar gidan sun ji sallamar da yayi.
Innah ce ta farga da tsaiwar ta shi ta taso ta iso inda yake tana cewa.
"Sadauki! lafiya na ganka a tsaye ka ƙaraso mana, Allah ya sa ƴan uwan naka basu tafi ba dama kai suke jira"
Ya É—ago tare da zuba mata jajayen idanunshi murya a raunane yace.
"Yanzu innah sai da kuka aika azo aga lefen nan fisabilillahi mai iyayen jiddah zasu É—auke ni?"
Sai ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana cije bakin shi, sauran maganar ta tokare a maƙoshin sa.
Innah ta zuba mai ido tana ƙara jinjina son da yake wa jiddah tinda har yana gudun ɓacin ranta da kuma na iyayen ta.
"To sadauki ya za'ayi da ƙaddarar Allah tinda Ubangiji ya ƙadarta ba Jiddah bace matarka a farko ba, yaya zamuyi gaba ɗaya haƙuri zamu yi tare da addu'ar alheri acikin lamarin"

Jinjina kanshi yayi tare da cewa.
"Tin da kika ce Allah magana ta ƙare"
Bai iya faɗa mata maganar da maƙocin nasu ya tare shi da ita ba sabida masifar zurfin ciki.

Ya na ƙoƙarin juyawa ya koma ɗakin shi su Ya minau suka ƙaraso wajan da shirin tafiya gida faridah sai tsokanar shi take yayi mata banza ya wuce ya barsu a wajan.
Innah tai murmushi tana kallon Aunty Hajjo tare da cewa.
"Yanzu goben ƙarfe nawa za a kai kayan? sai na kira Nafi kuje da ita amman ban da abinku da kun bari maza sun kai yanzu yaushe rabon da ku ga mata sun kai lefe?"

Da sauri faridah tace.
"Ban da abin Innah mazan su waye zasu kai? abu duk É—aya Mu dai ki bari Muje mukai"
Ba yadda Innah ta iya ta amsa musu kamar yadda suka buƙata Ya Minau ce tace.

"Innah ni naga Saadik na haÉ—e rai wai meke faruwa ne?"
Innah cikin basarwa tace.
"Ke rabu da shi ya ƙarata da Ƙuncin sa"
Har soro innah ta raka iyalan nata tana musu addu'ar fatan gamawa da duniya Lafiya suka fita titi ko wacce ta hau motar gida.

Ba jimawa da fitar tasu Baba shima ya shigo gida lokacin mutanen dake ganin kayan lefen duk sun tafi sai su Khadija dake tattare tsakar gidan.
Baba ya zauna a saman tabarma a rumfa Hasken farin ƙwan tsakar gida ya hasko har cikin rumfar da yake zaune yabi akwatinan da kallo Fuskar shi dauke da maɗaukakin farin cikin haɗin zumuntar da zasuyi da ɗan uwan shi ya dubi Innah dake haɗa masa abinci yace.

"Haƙiƙa Hafsatu naji daɗin wannan aure ina fatan Ubangiji yasa sai mutuwa ce zata raba su, tabbas Amadu ya wanke duk wani laifi da ya min abaya domin duk duniya ba wanda zai iya riƙe Ƴar amadu kamar Sadauki kinga munyi tuwo na mai na"
Ya faɗa yana sakin ƙayataccen Murmushi, Itama Innah Murmushi tayi tana cewa.
"Allah dai yasa ayi lafiya a gama lafiya niko burina na goya ƴaƴan ɗan auta tin da ƙwarina Kuma Allah ya cika min, sai batun kai Lefe kunyi magana da shi Amadun ne? waɗan nan yara fa sun kafe sun ce sai sune zasu miƙa kayan"

Baba ya É—aga kofin da innah ta cika mai shi da ruwan sanyin randa mai daÉ—i yace.
"Munyi waya ɗazu yace min Gobe da safe zai sauka kano Wajan yamma sai su miƙa abu duk na gida nida ma niyata ma a bata kayanta ranar ɗaurin aure, to tinda sunce zasu kai kar a katse su duk cikin murna ne"

Ire iren hirar bikin suka cigaba dayi har zuwa Lokacin kwanciya bacci.
*******
Adaah bata san waya bawa Mahir Numbern wayarta ba amman tafi zaton Momi ce ta tura masa shiyasa sanda taga kiran shi cikin dare batai mamaki ba hira mai cike da so da kulawa yake mata har sai da ya tabbatar ya dasa mata son sa acikin zuciyarta sannan ya barta aiko daren bata rintsa ba duk juyi shi take tunani abin ka da farin shiga.
Washe gari sai wajan taran safiya tayi sallar asubah sabida wayar da suka sha da Mahir ta makara ne tasha baccinta ta gode Allah wanka tayo ta shirya cikin Riga da skirt na Jar Atamfa Java bata ɗaura ɗankwaliba a haka ta fito Parlour tana kiran Maimuna da sauri maimuna ta ƙaraso ta rissuna tana cewa.
"Gani uwar É—akina Barka da asubah"
Cikin halin ko in kula tace.

"Kije ki wanken toilet ki gyaran É—akina ki kunnan turare akwai undies É—ina da zaki wanken washing machine É—in toilet É—ina ya lalace"
Har lokacin maimuna bata É—aga kanta ba har sai da Adaah taja aya sannan maimuna tace.
"An gama uwar É—akina ga break É—in ki can na haÉ—a komai kawai ci zaki yi"
A ya tsine ta amsa wa maimuna da.
"Ok"
Sannan ta wuce dining ta zauna ta haɗa tea ta ɗauki bread tana haɗawa da soyayyen ƙwai tana ci da yake Allah ya ɗora mata ci kamar gara ita Ko irin rashin cin nan ma na ƴaƴan masu kuɗi bata da shi.
Sai da ta share wannan bread da ƙwai tas sannan ta goge bakin ta da tissue ta ƙarasa cikin parlour ta kwanta tana canza channel.
Momi ce ta fito sai baza ƙamshi take.
Ta ƙaraso gaban Adaah tare da cewa.
"Tashin ki kenan na lalleƙa ki naga baki farka ba, Nima fita zanyi yanzun nan zan dawo"
Adaah tabi momi da kallo kafin ta kawar da kanta, ba tare da gaishe da mahaifiyar tata ba.
Momi tana ƙoƙarin fita daga Parlourn Sukai Kiciɓus da Abbah wanda shigowar sa gidan kenan hannun shi riƙe da ƙaramar jaka ta matafiya.
Momi zamewa tai a wayance ta zauna a saman kujera tana aje ƙaramar jakar hannunta dama lefen ƴar ƙawarta zata je gani sam bata kawo Abba zai dawo yau ba shiyasa zatai gaban kanta sabida ana faɗin irin dukiyar da aka laftawa ƴar ƙawar tasu.

"Sannu da shigowa Alhaji, amman dawowa babu sanarwa"
Ta faÉ—a tana sosa kai alamun rashin gaskiya.
Bai kulata ba sai Neman gurin zama da yayi da sauri Adaah ta diro tana sauka ƙasa har tana ƙwarewa wajan yiwa mahaifin nata barka da zuwa sabida shi tana shakkar shi ba kamar Momi ba.
Abbah ya bita da kallo ba tare daya amsa gaisuwar tata ba.
"Rabi'atu mai kike agida yau baki je makaranta ba?"
Sai ta hau kame kame sabida sarai tana da lecture ranar amman taƙi zuwa.
"Wato asarar kuɗina nake a banza ba karatun kike soba ko da yake ai magana ta ƙare dama abin da yasa na rabu dake na zaci zaki dage ki karatu ne, amman tinda baki son makaranta zan faɗawa Mijin naki ko bayan aure karya barki Fita ki haƙura haka abin da kika samu Allah yasa mai albarka"

Haɗe rai tayi nan da nan ruwan hawaye ya fara firfitowa daga idanunta ta jefa kallon ta ga Momi wadda ta kafe Abbah da ido tana jijjiga ƙafa.
"Wannan wace irin magana kake Alhaji wai shi wannan auren dole ne? haba yarinya bata so nida na haifeta bana so gaskiya ba zan lamunci a cusawa ƴata ƙatoton jahili ba, ce maka akai bata son karatu bayan ita kaɗai Allah ya bamu Tarin dukiyar da Allah ya baka in baka barta tai karatun ba waye zai riƙe mana ita nan gaba"
Abbah ya zubawa Momi ido cike da ɓacin rai, sam tinda lamarin auren nan ya tashi momi bata saurara mai bata masa ta sauƙi hatta ga kalamanta kawai yana kai zuciyar shi nesa ne yana duba wasu abubuwan jiba yanzu yadda take masa magana agaban ƴarta ba ladabin harshe ko tauna magana.

"Maryam sai fa Rabi'a ta auri Saadik koda gawarta ce wallahi zan kai gidan ƙarewar ƙiyayya in an aura masa ita tasa Ashana ta kunnawa kanta ta Ƙone ta mutu Ki sanar da ƴan uwanki anjima Za a kawo lefe"
Daga haka ya miƙe yabar Parlourn zamewa momi tayi daga saman Kujerar tana yarfe Zufa.
Da sauri ta É—aga waya tana Kiran Hajiya Lubna.
Daga ɓarin Lubnah dake kwance domin har Lokacin bata tashi daga baccin safe ba.

Ta ɗaga wayar tana jan ƙaramin tsaki.
"Maryam yaya akai wannan wayar da farar safiya?"
Momi ta yarfe zufa a karo na barkatai kafin tace.
"Kinji wata sabuwa anjima zasu kawo lefen Adah ni kaina ma ya kulle"
Da sauri Lubna tace.
"Kamar yaya dama baki zuba masa magani a ruwan ya sha ba har ya sami zarafin maganar auren?"
Momi ta juya tana kallon hanyar da Abbah yabi taga ya ƙullewa ganinta sai tace.
"Yau fa ya dawo gari yanzun nan ya sauka yake wannan bayani wallahi bai ma bani fuskar na bashi ruwan ba bare akai ga na saka ke nifa gani nake suma aiki suke akan Alhaji duk yabi ya birkice min kamar ba shi ba"
Chapter 20 · 0% Book details