← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nurah yace.
"Okay ba matsala sai batun lefe kuma?"
Ya É—an haÉ—e rai.
"Nikam titsiye ni kuka zo yine to ban yi ba"
Babawo yayi dariya tare da cewa.
"Kaifa ka zama ɗan alallaɓa yanzu Angon Rabi in ma bakai lefe ba mu sai muyi karo karo"
Wani kallo ya watsama Babawon tare da cewa.
"Kasan dai ni ba rago bane babu abin da yake firgitani, Lefen yana gidan Yaya Minau kun san gidan sai kuje ku gani"
Saiti yace.
"Baka isa ba dole a kawo min kayan madam nai mata É—inkuna masu fisgar hankali tasan ta auri abokin telan mata"
Ta shi yayi cak ya tada sallar shi sukam maganganun su suka cigaba dayi akan bikin kafin su miƙe su fita.
Shikam ya jima a sujjadar shi yana ƙara jaddada neman zaɓin Allah akan lamarin auren wanda dama wannan addu'ar yake ba dare ba rana in har yayi sallah sai ya miƙa koken shi wurin Allah akan lamarin auren nashi.

Bayan ya sallame ya na ɗe abin sallar ya kashe ƙwan ɗakin yayi kwanciyar shi.

Da asubahi suka haɗu da baba a masallaci wanda baban yake masa magana akan shirin auren bayanin yadda ake ciki yayi ma baba cikin ladabi, baba ya ƙara da cewa, mahaifin jiddah ma yay masa magana jiya akan wai sukai kuɗin aure in yaso in ta kammala karatun sai ayi bikin.
"Baba ka basu haƙuri kaga duk ƴan kuɗaɗen hannun nawa na haɗa zan kai kuɗin gidan can su min alfarma bayan biki sai na bada akai"
Baba ya murmusa tare da cewa.
"Hakane sadauki, amman tinda suka nemi akai to akai ɗin ni zan bada kuɗin akai musu kaga sanda zamu kai kuɗin Amadu yazo min da batun auren ka da rabi'ah to kar suga kamar ba zaka auri ƴarsu bane mutanan nan babu abin da zamu ce musu sai godiya da irin ƙaunar da suke nuna mana sabida haka Amadu yace jibi zai dawo kano in ya dawo zan bada Kuɗi suje su kai gidan su jiddan shida sauran ƴan uwan mu na ƙauye"
Saadik ya rissunar da kai ƙasa tare da cewa.
"A,a Baba Kana ta kanka ka É—orawa kanka wahala ka bari bazai gagaraba in sha Allah, Burina akai lefen sannan na bawa masu gidan can kuÉ—in su sai hankalina ya kwanta"
Baba yace.
"Banda abin ka Sadauki In da ni mai hali ne ai da na ɗauke maka komai na hidimar aure, to ni babu mahaifiyarka babu sai kai kaɗai da Allah ya bawa ƙarfin zuciyar nema ga shi yanzu Nauyi zai ƙara ninkuwa akanka bayan namu Allah ya maka albarka kuma zan cire kuɗin auren akai Musu In sha Allahu"
Daɗa rissunawa yayi yana wa baba godiya sannan suka ƙarasa gida.
Ɗaki ya koma ya sake kaya dan ko wanka bai yi ba, a gurguje yaje suka gaisa da Innah ya fice shago tin sassafen don abin kari ma sai Usman ne yakai masa dole yabar Usman a shagon Shi kuma ya wuce Ƙofar ruwa.

Wajan ƙarfe Sha ɗayan safiya gaba ɗaya iyalan na Innah suka hallara agidan Aunty Amina da Ƴaƴanta jawahir wadda ba a jima da bikinta ba sai Hussaina wadda za'a ma biki kwanakin nan, Aunty hajjo da Fatima ƴarta wadda ke dauke da tsohon ciki sai Sayyidah, Sai faridah data zo tare da Sajidah da Sajjad ga kuma su Ummi nan don bama suje Makaranta ba ranar shiyasa gaba ɗaya gidan na Innah ya gama cika da Ƴaƴanta da Jikokinta ƙatuwar tukunya Khadija ta wanke aka ɗora wake da shinkafa a tsakar gida wadda za a ci da rana.
Babu komai da yake ta shi sai hayaniyar su, ta surutun su kuma duk akan bikin auta ne suke ta faman maganganu na yadda bikin zai tafi.
Shigowar Sayyid da Hassan ce ta sa surutun ya ɗan lafa, Sayyid ɗan Aunty Hajjo Hassan ɗan Aunty Amina, Suka shigo da akwatina niki niki da alamun daga kasuwa suke sai da suka shigo da akwatina saiti Biyar cif da ƙatuwar gana Hassan yay miƙa yana cewa
"Washh Allah Ummah ba ƙaramar wahala muka sha a kasuwa ba, da ƙyar Abba ya samo ɗaya atamfar nan fa"
Aunty amina ta fara janyo akwatinan tana cewa.
"Allah dai yay muku albarka dama nasan za a ci wahalar kafin a samo, da kuka amso ne kuka je gida kuka É—auko akwatinan? to kun sallami mai É—an sahun daya kawo ku?"
Sayyid yace.
"Eh mun sallame shi yama tafi Ummi nina wuce school"
Ya faÉ—a yana kallon Aunty Hajjo.
Innah da bakin ta ya ƙi rufuwa cewa take.
"A,a ku bari kuci abinci mana Allah ya maku albarka kuma ya ninka musu abin da kukai"
Matasan dai fita sukai sunawa Innah murmushi, tare da amsa addu'ar da tai musu suko su Ya Minau kayayyakin sukaita É—agawa don an karo wasu kayan akan na da faridah ce mai shirya kayan ko wanne tana haÉ—e shi a inda ya dace.
Kafin Ya Minau ta cewa su Ummi suje maƙota su farfaɗa azo aga lefen kawun su saadik aiko Su Ummi fita sukai gida gida sukaita faɗa kafin kice kwabo gidan Innah ya cika da mutane ƴan kallon Lefe.
Sai dai mahaifiyar Jiddah furr taƙi zuwa ta kuma kafawa Jiddah takarar ko kallon saadik karta ƙara yi ranar Jiddah taci kuka ta godewa Allah, domin Wata irin ƙaunar Saadik ce ke ƙara ninka mata ruhinta.
Maƙota kowa yazo sai ya tambaya gidan su Jidda za'a kai sai Faridah ke musu bayanin Ai ƴar ƙanwar Baba zai aura Jiddah kuma sai ta kammala karatun ta wasu suyi fatan alheri wasu kuma su tafi suna ƙus ƙus ranar har dare ana shigowa kallon Lefen wanda kowa ya gani sai ya yaba shi kan sa Baba yayi mamakin rawar ganin da ƴaƴan nashi sukaiwa ƙanin nashi aiko sai saka Musu albarka yake.
Saadik bai shigo gida ba sai bayan Isha'i shima wayar innah ce ta saka ya tawo sabida a kwanakin nan cikin taskar Allah yana samun ciniki ne fiye da yadda yake yi ada shiyasa yake jimawa a shagon.
Tin daga bakin layi yaji mutane na masa Allah ya sanya alheri wani maƙocin su ne ya tare shi sanda zai shiga gida yana ce masa.
"Malam saadik ashe lokaci yayi to Allah ya sa alheri"
Dama da mamakin yadda ake masa Allah sanya alheri ya ƙaraso sai kuma ga wannan maƙocin nasu shima ya tare shi yana masan.
Ƙaƙalo murmushin dole yayi tare da cewa.
"Amin ya rabb! nagode"
Ya faɗa yana ƙoƙarin shiga gidansu.
"Amman Saadik kaji tsoron Allah naji ance ba Waccan yarinyar jiddah zaka aura ba, ƴar ƙanin mahaifinka zaka aura mai kuɗi shiyasa ma kuka haɗa lefen ƙarya, amman gaskiya bai ci kaiwa Jiddah haka ba kowa yasan yadda kake da yarinyar nan amman ka yaudare ta"
Da sauri ya ɗagawa maƙocin nasu hannu tare da faɗawa soron gidansu da sauri.........
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *14*

Ya lumshe idanunsa yana fesar da Numfashi ƙasa ƙasa Sautin Kukan Ya Minau na ratsa dodon Kunnen shi, Kafin ya ɗago da idanun nashi ya dire kallon shi akan Innah wadda tai tagumi tare da zubawa Ya Minau Ido takaici da tarin damuwa ne bayyane a saman fuskarta.

Tsaki Aunty Nafi taja tana cewa.
"Haba Yaya gaskiya a sake tunani danni kam banga alfanun wannan aure ba, kowa ni ɗa namiji yana fatan samun macen ƙwarai wadda ta fito daga gidan martaba amman wannan kam mahaifiyar yarinyar nan ba ƴar mafuta bace"

Cikin damuwa Innah ta dubi Ya Minau tana cewa.
"To yaya zamuyi wannan ƴar, Babanku ya kafe akan ayi auren nan ni kaina ba so nake ba sabida Maryam ba ƙaunata take ba to abin ne yafi ƙarfina dole na tattara na zubawa sarautar Allah ido duk abin da Allah yayi akai daidai ne"

Faridah ma mita take Aunty Hajjo kam ta kasa magana sai faman Jijjiga ƙafa take duk irin wahalar da suka sha wajan haɗa lefen nan amman wannan cin zarafin ne zai biyo baya.

In kujerar daya ke kai tai motsi to Saadik yayi motsi acikin maganar su, sai dai zuciyar shi ƙunci ne tare da tarin damuwa haka ya cigaba da wanke takalmin shi ya kaɗe ruwan ciki ya jingine a jikin bango ya miƙe yabar Musu tsakar Gidan to shi mai zai ce, bayan duk Babane yaja musu da bai karɓi tayin ubanta ba da wannan tozarcin bai faru a gare suba.

Ɗaki yaje ya shirya cikin Jc jajaye wandon iya gwiwar shi sai farar safar ƙafa sai farin takalmin Ball ya fito bai ma shiga gidan ba ya wuce filin ball cikin son kau da damuwar daya bar ƴan uwan shi suka fara buga ƙwallo.

Da ƙyar innah ta rarrashi ya minau sabida dama itace babba amman tafi ƴan uwan sanyin zuciya da rauni har magariba suna gida suna jira shigowar Baba ganin bai shigo ba har bayan sallar yasa suka tattara suka wuce gidajen su duk rai babu daɗi.

Sai bayan sallar isha'i baba ya shigo gida sam innah batai masa maganar ba har sai da yaci abinci ya zauna a tsakar gida yana sauraron labarai a Radio.

Innah ta aje masa kofin Furar data damo masa.

Ya dube ta tare da cewa.
"Hafsatu mai yake damunki ne? gaba É—aya tinda na shigo gidan nan na fuskanci yanayin ki ba daÉ—i"

Innah ta rausayar da kanta gefe cike da zurfin ciki tare da danne abin da ke cin ƙasan ranta tace.
"Babu komai Babansu ga furar nan ko sai anjima zaka sha?"

Baba ya fuskance ta.
"Haba Hafsatu bafa yau na sanki ba, wallahi shiyasa inna ga Sadauki ya ɓoyen abin da ke damun shi nakan ce barewa batai gudu ɗanta yayi rarrafe ba, yanzu dai faɗa mini mai ke damun ki?"

Ya faÉ—a yana maida hankalin shi kaco kam izuwa gareta.
Chapter 18 · 0% Book details