← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Innah nikam a ƙoshe nake naci abinci gidan ya minau sai dai Ruwan shayin zan amfani da shi anjima"
Ta ɗan ɓata fuska.
"Kaiko kaci dambu ne na tsaki mai daÉ—i irin namu na mutan da"
Ya kalleta dama duk sanda taga ba zai ci abinci ba sai tai masa wannan dabarar yake ci.
Aiko janyo kwanon yayi ya sa cokali ya hau ci duk da ya ƙoshi amman haka yake cusawa a cikin sa don hankalinta ya kwanta ta ga dai ya ci ɗin.
KaÉ—an ya rage yayi Hamdala sannan ya kira Ummi yace takai kwanon kitchen tare da Ledar Daya shigo da ita.
"Kinji innah su Ya minau sun min lefe"
Innah tai murmushi tare da cewa.
"Yanzu muke maganar da Hajjo faÉ—a take tayi wai akan mai yasa ba'a faÉ—a musu da wuri ba da sunyi shirin daya fi haka"
Ya lumshe ido wato ada yana jin takaicin tasowar shi, shi ɗaya acikin mata kuma shine ƙaramin su amman daga baya sai ya dinga ganin Cewar Matan suna da matiƙar jin ƙai da tausayi uwa uba kuma suna son shi sosai.

"Ni kam innah faÉ—a ma nahau yi don me zasu É—orawa kan su nauyi"
Innah tai murmushin jin daÉ—i tare da cewa.
"Haba sadauki in su Hajjo ba su maka ba wai wa za su ma duk duniya ka ma daina maganar nan Ni dama burina Allah ya haɗa min kanku yau daɗin dana ji ko yanzu Allah ya ɗau raina babu abin da zan ƙara masa sai Godiya domin nasan zaka zame musu uba su kuma su zame maka iyaye"

BuÉ—a Aunty Hajjoh take daga cikin É—akin Innah kafin ta fito tana cewa.
"Wai innah dole muyi ƙara'i a bikin ɗan auta, ranar kawai nake fata tazo nasha rawa son raina"
Innah ta hau salati.
"Haba Hajjo da ƴaƴanki har kina shirin karɓar jika kiyi rawa wannan son rawa taki naga ranar denawa"
Da sauri Saadik yace.
"Innah kima faÉ—a musu babu taro in taro za su yi su bari sai bikina da Jiddah don wannan auren dole ne"
"Kai da kata bafa zaka hanamu sakewa ba kaji da gulmarka kuma duk ranar dana ga kana kuka akan soyayyar adawiyya sai na maka tunin wannan maganar kuma abin da nake so dakai shine tin yanzu ka koyi adalci duk matan kane in ma kana son wata to ka barshi a ranka amman batun auren dole duk bai taso ba, Adawiyya ƙanwar ka ce daga baba sai kawu Amadu duk duniya bamu da kamar mahaifinta a cire maganar mahaifiyarta da ita kanta a kalli Zumuncin Allah duk wanda ya ɗauki ɗansa ya baka wallahi ya gama yi maka ƙarshen ƙauna"
Innah ta zubawa Hajarah ido tana kallon yadda take zabgawa Saadik faɗa shi kuma yay ƙasa da kanshi domin ba zai iya musu ba dama duk ƴaƴan nata Hajarah ce tsayayya bata ɗaukar raini sannan akwai tsage gaskiya shiyasa suke shakkarta dama gata ma sha Allah duk tafi su ya minau girma in ka dubeta sai kace ita ce ma babba acikin su.
Sosai Aunty Hajjoh tai masa faɗa mai haɗe da Nasiha sannan ta cewa ƴarta ta haɗa musu kaya zasu tafi gida shiya raka su titi har suka je babban titi tana ƙara Yi masa nasiha da koya masa dubarun zama da iyali.
Shiya biya mata na Mota sannan ya wuce shagon su Nura Saiti.
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma,9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *12*

Sadiq Babu, Nura saiti, babawo duk suna cikin shagon Nuran suna Buga lido ga kofunan shayi nan irin ƙananun nan na buzaye a gefen su ihun su ya cika shagon, duk sallamar da Dagiya yake yi basu ji shiba tsaki yaja kaɗan ya nemi gefen katifar saiti ya zauna.
Babu ne ya kula da shigowar Saadik sabida haka ya dakata da Buga lidon hannun shi ya zabga ihu tare da cewa.
"Sai angon mata biyu na rabi da hauwa mai abin mamaki" Saadik ya haɗe fuska ya sha kunu ya na lalubar wayar shi da ke ringing, Nurah ya ƙunshe dariyar sa ganin rabin hararar akan shi take sauka.
"Haba Dagiya auren ka guda ya tashi amman ka kasa faÉ—a mana sai a bakin Nurah muke ji?"
Cewar Babawo daya juyo yana kallon Saadik, Shidai bai tan ka suba kuma bama shi da niyyar ya tanka sun sai ma hararar da yake sakarwa Nurah wato bin da yay masa rakiyar dubiyar Jidda shine ya zo yana tsaigunta wa su Babawo lamarin auren nashi daya jiyo, ƙwafa yayi tare da tashi yana ƙoƙarin fita daga shagon da sauri Babu ya tare mai hanya yana cewa.
"Mu zaka mayar marasa hankali mu kome muka yi sai mun faÉ—a maka amman auren ka guda ka kasa faÉ—a mana bada ban Saiti ya bika duba tafisu ba da bama zamu ji ba"
Saiti ya cafke da cewa.
"Ai kasan dana ji a wurin maman tafisu wajan Baba naje shiya faÉ—an komai na auren nashi, wallahi kai dai Dagiya ka daina haka zurfin cikin nan naka har ya fara isata, to me kake nufi da sai dai muji auren naka daga sama ko yaya, ka fa tina mu yanzu mun wuce Abokai wallahi mun zama Æ´an uwa in ma kai a abokai ka É—auke mu to mu a É—an uwa muka É—auke ka"
Ganin duk sun masa caa sai jikin shi yayi sanyi sanin kan shine ya san bai kyauta ba, ko yace ma baya kyauta wa su suna faÉ—a masa duk wata damuwar su hasalima shike kawo musu masalaha in wani abun ya taso musu amman shi da wiya suji lamarin shi haka tsarin shi yake kuma hakan halitta ce daga Allah wani bin ko innah baya faÉ—awa damuwar shi sai dai abin yayta cin ranshi.

Komawa da baya yayi ya zauna a saman kafitar Saiti ya dafe kan shi da hannu biyu, Ya jima a haka kafin ya É—ago idanun shi ya sauya kala ya koma ja, alamar damuwa ta bayyanar masa.
Gyaran murya yayi kamar kullum cikin ƙasa da murya kasancewar sa mutum marar son hayaniyya ko ɗaga murya.
"To babawo yanzu mai kuke son nace muku? so kuke na fito fili na bayyana muku cewar Baba auren dole zai mini ko yaya?"
Mai su Babawo za suyi in ba dariya ba Babu harda ƙwarewa ganin yanda Saadik ya taƙarƙare yana cewa auren dole.
Ganin zasu mai da shi sakarai yasa ya ƙara miƙewa a fusace ya bangaje saiti ya fice daga cikin shagon.
Saiti ya tsagaita dariyar tashi yana cewa.
"Kunga ku zo mu bishi dole ai zama akan auren nan, Domin Dagiya É—an halak ne ba zamu bar shi da É—awainiya shi kaÉ—ai ba kuma don Allah kubar dariyar haka ai maganar hankali, Kun san halin shi kamar kuturu yake zuciya da fushi ba sabon abu bane wurin shi"
Ta shi sukai suka rufo shagon suka bi bayan Saadik da yake basu da nisa tuni suka shiga gidan su saadik ɗakin shi dake soro suka shiga baya ciki da alamun yana banɗaki Nura ya zauna a saman kujerar roba su babawo kuma suka zauna a saman carfet ya kusa minti goma a bayin kafin ya fito shige su yayi ya nufi hanyar ƙaramar wardrobe ɗin shi, ya ɗauki abin da zai ɗauka ya koma bayin Minti kaɗan ya fito cikin farin wandon polo da farar rigar polo marasa nauyi da alamun na baccin sa ne, ya ɗauki turare ya fesa sannan ya shinfiɗa darduma yayi sallar isha'i ganin yayi sallama yana kokarin mai da ta nafila Nura yayi gyaran murya.
"Kaga muma fa musulmai ne na ƙwarai tinda kayi sallar Isha'i ka bari muyi magana muma muje muyi tamu in mun fita sai kayi Nafilar"
Dan dai kawai É—akin shi suka zo ne bai son suji ba daÉ—i shiyasa kawai ya juyo yana fuskantar su.
"Mu yanzu a matsayin mu na abokanka zamu É—auki nauyin wasu abubuwan kama daga kayan abinci zuwa sauran hidimar tura motoci zuwa gidansu amarya"
Sai da ya É—auki lokaci bai magana ba sannan yace.
"To nagode" a taƙaice.
"To ya batun mazauni fa?"
Cewar babu.
Ya shafa kanshi yana cewa.
"Nan gidan dake kallomu na kama kasan masu gidan zasu tashi shine ni zan shiga"
Babawo yace.
"Kai gaskiya yayi maka kaɗan kuts ni kaf arear nan ma akwai ƙaramin gida kamar wannan kuma har mata biyu zaka saka aciki"
A zafafe ya ce.
"To daidai ƙarfina kenan uban wa yace maka duk su biyun zan aura lokaci ɗaya ina zan kaisu Jiddah sai ta gama karatu kafin nan na fara ginina In sha Allah ko ɗaki biyu nayi saisu koma su duka mu zauna a muhallina"
Nurah yace.
"Eh to tinda mace É—aya ce ai ya isa sai ai maganar gyare gyare zan saka Mizambilun gidanmu yaje yaga gidan tinda ya iya painti sai yaje yayi maka shafen É—akuna dana tsakar gida"

Saadik yace.
"Wasu É—akuna É—aki É—ayane ciki da falo sai kicin da bayi amman bakaji kuÉ—in da suka sawa gidan ba haka dai zan biya tinda nina fi son kusa da innah gaskiya"
Chapter 17 · 0% Book details