Sashe 22
So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajan magariba wasu daga cikin Dangin su Iyah suka dawo daga gidan Amarya sai dai motar data ɗauki kayan ɗaki ta dawo da fin Rabin kayan ɗakin a cewar wata daga cikin ƴan uwan iya ai kujera ma guda ɗaya ce doguwa kaɗai ta shiga falon, Uwar ɗaka kuma sun saka katifa don gadon ma yaƙi shiga sai akwatinan da aka sa don su madubi ma duk sun ƙi shiga sabida kayan ba ƙananu bane.
Ataƙaice dai yadda suka sanar da Iyah falon ya sami carfet sai doguwar kujera guda ɗaya sai labulaye suma ba duka ba uwar ɗakan kuma katifa da akwatinan Adaah, Kitchen ma Gas yaƙi shiga sai tukwane da ƴan tarkacen ƙananun kaya ne suka sami zama sabida rashin wadataccen faɗi a gidan
Iyah ta maida ajiyar zuciya tace.
"Ai babu damuwa Allah ya sa albarka hakan, bari naiwa mahaifinta magana in yaso sai a maida kayan kawai"
Sabgar haÉ—a miyar taushen biki aka cigaba da yi.
Adaah na ɗaki tuni zazzaɓin takaici yayi awon gaba da ita
*****
"Yanzu saratu duk yadda Jiddah tayi wa Saadik halacci haka zai mata kawai sai ganin katin É—aurin aure mukai ana rabo?"
Cewar wata maƙociyar su Jidda mai suna talatu.
Umma ta kama haɓa tayi tagumi
Cikin damuwa tace.
"Ni duk ba wannan ba, na samu wannan uwar nacin ta rabu da shi gaba ɗaya ta fitar da shi daga zuciyarta ta nuna da shi da babu duk ɗaya amman taƙi kullum kuka wallahi jiya daga ni har mahaifinta bamu rintsa ba ni yaya zanyi ne"
Ummah ta faÉ—a duk damuwa ta bayyana a saman fuskarta.
"Hmm saratu ai tashi tsaye zaki ki samawa ƴarki farin cikinta, wannan aure ai na kwaɗayi ne naji ance ƴar ƙanin mahaifin sace mai kuɗi kuma ita kaɗai ubanta ya haifa kinga da zarar ta haihu ai dukiya ta su ce sabida haka idan har kina buƙatar taimako akwai wani da zan haɗaki da shi a jawo hankalin Saadik ya birkice muku"
Umma tai jimm kafin tace.
"A iya ganin idanuna ai kamar soyayyar da yake wa Jiddah ma ta wadatar in muka ce zamu haɗa da bin malamai zamu shiga haƙƙin sa, Ni kin san talatu bana harkar biyar malaman nan nafi gane tsaiwar dare, Nidai barni in raina ya ɓaci zanyi faɗana sosai amman bana raba imanina biyu in har Allah yace jidda matar Saadik ce zasu yi aure amman in har Allah bai ƙaddara ba babu wanda ya isa ya basu junansu"
Cikin rashin samun nasara talatu tace.
"Haka ne saratu to Allah ya daidata lamarin bari na ƙarasa gida"
Ummah ta raka talatu har bakin ƙofa ta tafi.
ÆŠakin jiddah umma ta shiga ta sameta kwance da rigar baccin jiya a jikinta, ummah ta sami guri ta zauna a gefenta tare da kamota zuwa jikinta.
"Kinga har yanzu jikin ki akwai zazzaɓi don Allah jiddah ki bar wannan damuwa nina fiki shiga tashin hankali amman yaya zamuyi mahaifin ki ya baki haƙuri nina baki haƙuri amman kinƙi daina kukan nan"
Muryarta sanyi ƙalau tace.
"Ummah kawu Saadik fa aure zaiyi gobe, duk yadda nake son shi ya kasa aure na a karon farko sai wata haba umma ta yaya zan sami Nutsuwa umma ki taɓa zuciyata kiji yadda take harbawa"
Cikin faÉ—a ummah tace.
"Zaki kashe kanki, ne a banza kinga sun kasa bikin su? ko kinga sun dena shirin su ina ba har lefe ya haɗa mata ba to in zaki gane karatun ɗa namiji ki gane, ni inda kinyi zuciyata da shi da babu duk ɗaya ki tattare su har mahaifiyar tashi ki watsar itama banda munafurci meye a auren da bakwa so harda gayawa maƙota su zo suga lefe in zaki buɗe idanunki ki kalli gaskiya ki buɗe, don Allah ko yayi miki magana karki kulashi ki gasa mai maganar da zatai mai ciwo"
Jidda ta juya tare da lumshe idanunta tana jin son shi aduk kan gaɓɓan jikinta soyayyar shi na motsa mata kamar yanda Numfashinta ke fita sam bata jin maganganun umma zuciyarta ta tafi tunanin shi har umma ta gama faɗanta ta fita.
A hankali ta jawo wayar umma data ɓoye a ƙasan pillow ta miƙe tare da rufo ƙofarta gudun dawowar umma.
Ta kunna wayar tare da zuba wa wayar ido can kuma ta shiga Jera lambobin sa data haddace su akanta ta shiga kira.
Saadik dake kwance don har lokacin bai ji daidai a zuciyar shiba, tinda ya dawo daga sallar asubah yake juyi a katifa yana jiyo sautin share sharen tsakar gida da yara keyi sai haÉ—a kayan gidan suke sabida shirin É—aurin auren gobe.
Baida niyyar tashi bare akai ga batun yayi wanka, gaba É—aya jikinsa yayi masa nauyi dama abinka da jikin wahala an saba fafutukar nema.
Wayar shi ta shiga ƙara alamun kira na shigowa, a hankali ya lalubi wayar ganin lambar dake yawo a saman screen ɗin wayar yasa shi sakin murmushi har kiran ya katse sannan ya shiga kira yaushe rabon daya ji muryarta yaushe rabon da su haɗu gaba ɗaya ta yi masa yaji ta ɗauke masa wuta tinda maganar auren shi ta fasu shi kuma yana jin nauyin zuwa inda take duk da akwai shirin kai kuɗin auren shi gurin ta kamar yadda baba ya sanar da shi.
Bayan ta É—aga wayar shuru tayi masa.
Cikin tattausar murya yace.
"Ƴammatana an dena fushin dani kenan?"
Turo bakin ta tayi kaÉ—an kamar yana kallonta kafin ta share hawaye.
"Sabida kaga ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba ya sa ka zaɓi yi min haka?"
Ya saki murmushin takaici.
"Hawwa yaya kike so nayi ne mu duka bamu isa mu ja dayin Allah ba"
Sai ta saka kuka.
"Dama haka zaka ce daga nai magana sai ka faÉ—i haka amman ai wani abin ma akwai son zuciya acikin sa"
Ta faÉ—a har lokacin tana kuka!
"Kinga idan kin san ɓacin rai kika kira ki sa min zan kashe wayata haba ke wace mutum ce yaya kike so nayi ne kin san abin da yake damuna kin san meke zuciyata so kike na bujirewa mahaifina ne sabida farin cikin ki ko yaya?"
Ya faɗa yana hucin ɓacin rai.
Cikin sanyin murya tace.
"Kayi haƙuri nima bani na ɗorawa kaina soyayyarka ba ka tayani da addu'a Allah ya yaye min"
Sai ta saka masa rauni a zuciyarsa muryar shi a kwance ya shiga rarrashinta.
Sai ga shi ta ware tana dariya, sam ta mance ma da damuwar data shiga cikin kwanakin nan ta kuma yi watsi da huÉ—u bar umma ta saka aranta Saadik ne farin cikin rayuwarta.
Lokaci mai tsayi suka É—auka suna hira kafin suyi sallama shima yaji wani sashi na zuciyar shi ya sami nutsuwa jin tana cikin farin ciki.
Innah ce ta turo ƙofar ɗakin nashi ta shigo bakin ta dauke da sallama.
Da sauri ya tashi daga kwanciyar da yake.
Ya shiga gaishe da ita cikin ladabi
"Sadauki ina ta zuba idanun ɓullowar ka gidan shuru, shiyasa nace bari naji ko lafiya?"
Ya sauka daga katifa ya miƙe ƙafafun sa ya zube su a ƙasa yana cewa.
"Lafiya lau, innah zan shigo sai nayi wanka yau na tashi da nauyin jiki ne"
Ta kalle shi da kulawa
"To kayi hanzarin fitowa ciki ka sa wani abun acikin ka kaga rana harta fito"
Cikin kulawa yace.
"In sha Allahu"
Innah ta fita shi kuma wata wayar ya ɗaga wani mutumin sa ne dake siyan ƙarafan shi a kasuwa suka gaisa mutumin yace.
"Malam Saadik ashe lokaci yayi Allah yasa akhairi jiya Yaron ka ke faÉ—a min nazo shagon naka baka nan yace kuna shirin biki ne amman abin alkairi yazo ba labari"
Yayi É—an murmushi kaÉ—an.
"Wallahi abin ne yazo babu shiri amman kayi haƙuri"
Mutumin yace.
"Ba damuwa ba zan sami damar zuwa ba, amman ga saƙo nan ba yawa na sa maka ta account Allah yasa albarka"
Saadik yace.
"Harda hidima to Allah ya sa ka da alkairi na gode ƙwarai"
Sukai sallama daya duba kuwa dubu ashirin ne mutumin ya tura mishi.
Wanka yayi ya shirya cikin ƙananun kaya ya fita cikin gida
A bakin ƙofar kitchen ya sha shayi da biredin da innah ta haɗa masa Atm ɗin shi ya bawa Umar yaje P.o.s ya ciro masa dubu ashirin ɗin da mutumin ya turo masa gaba ɗaya ya bawa Innah yace ayi cefane anjima zai kawo shinkafa zai je janguza domin tafi sauƙi acan.
Inna ta karɓi kuɗin ta ƙirgi dubu goma ta miƙa masa sauran.
"Dubu goma ta isa sadauki ina da shinkafa ta ba sai ka siya ba, ka bar kuÉ—in ka ni ba wani taro zanyi ba idan Æ´an uwana sun zo sai Æ´an uwanku na makoÉ—a shikenan sai waÉ—annan yaran"
Ya ɓata fuska.
"Innah me kike siyarwa da zaki ce zaki hidimar Æ´an biki nifa innah ban so ki É—aga hankalin ki Allah ya rufan asiri komai zanyi"
Fafur taƙi amsar kuɗin nashi.
Sabida tausaya masa take nauyin yayi masa yawa yayi nasu yayi na marayun gabansu sannan ga na gidan shi zai fara.
Haka ya fita ba dan yaso nauyin data ɗora wa kanta ba, zuwa rana ƴaƴan innah sun hallatara sai matar ƙaninta da matar yayanta sai Yayarta da Anty nafi sai wasu daga cikin dangin su Baba na makoɗa da suka zo miya su Aunty hajjo suka ɗora a ranar dai kwanan hira akai damma burin da suka ci abikin bai cika ba sabida ɓacin ran da suka kwaso washe gari maƙota suka shigo tayin kwasar tuwo wajan takwas an haɗa komai na ɗaurin aure.
Tin ƙarfe goma su nura suka ishi Saadik daya shirya sufa sun kintsa sabida goma da rabi za'ai ɗaurin auren.