Sashe 6
So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yanda Saadik ke son kallon Boll sam yau ya mance zasu je kallo kwata kwata sabida haka tsaki yaja dan baida karsashin fitar ma gaba É—aya Nafila zai yi kawai ya kwanta yasan Baba zai fita waje shan iska bayan ya gama jin Labaran sha É—ayan dare ya rufo gida shiyasa zeyi kwanciyar sa.
"Nura Kuje kawai kaida su Babu danni gaskiya yau É—innan ba zan iya zuwa gidan kallo ba"
Daga haka ya kashe wayarsa gaba ɗaya ya mayar chaging ya koma ya kwanta ya zurfafa acikin tunanin wannan lamari mai girma daya faɗo masa ko a kanshi bai taɓa tunanin Baba zai masa auren dole ba, dan shi kam wannan aure na dole ne yana zaman shi lafiya Baba ya bashi Umarnin zuwa inda za a ɓata mishi rai.
Maganganun Baba na jiya da daddare ne suka soma dawo masa cikin kansa.
"Sadauki!Waye mahaifinka?"
A lokacin sun kammala cin abincin dare ne duk suna zaune a Rumfar Baba shida Baban da Innah wadda take cin GyaÉ—a marau marau.
Ya Nutsu sosai tare da cewa.
"Baba duk duniya ban san wani a wannan matsayin na uba ba face kai"
Baba yaji daÉ—in kalamin shi duba da yanda yayi Murmushi a lokacin haÉ—i da samai albarka kafin ya fara dirar mashi da maganar data haifa masa É—aukewar Numfashin wucin gadi.
"Sadauki jiya mahaifin Wannan yarinya Hauwa'u mai haƙuri da kawaici ya kirani akan maganar auren ku sabida karatunta daya kusan zuwa ƙarshe, Bayan nai masa na'amm da maganar sai na ɗauki wayata na Kira ɗan uwana wanda duk duniya bani da kamarshi Amadu uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya nina saki Nono ya kama na shaida masa batun Auren ka"
Baba yaja fasali.
Saadik yaji wani irin farin ciki a zuciyarshi.
Innah ma sai ta hau murmushi sabida Jiddah ta cancanta ta zama surukarta duba da yanda yarinyar ke son É—an nata tilo tal namiji aduniya kuma auta acikin Æ´aÆ´anta waÉ—anda dukka mata ne Allah ya bata shi kaÉ—ai ne namiji acikin su kuma shine auta.
Maganar baba wadda ta katse Murnar Innah da Saadik ita ce ta cika Kunnuwan su.
"Sai dai Amadu ya katsen hanzari, ya mini kyauta kuma na amsa tinda bahaushe yace yaba kyauta tukwici dik da kyautar dama bata yanzu bace amman Lamarin daya zo ya cuɗe a tsakanina da shi yasa na fidda rai akan kyautar ta shi Sadauki Amadu yace kaje ka Nemi auren ƴarsa RABI'AH duk da maganar ba sabuwa bace a wajena nida Hafsatu mahaifiyarka Tin ranar da Aka haifeka da Amadu ya ɗaga ka yace In har Matar sa ta haifi ƴa mace yayi ALƘAWARIN ba tada Miji sai kai to yanayin yadda Zumuncin mu ya lalace da shine yasa Ban ɗauka zai cika wannan Alƙawarin ba sai kuma gashi ya cika don yace sadaki kaɗai zaka bada Rabi'atu dai ƙanwarka ce da ubanta dani cikinmu guda dan haka In har ni na haifeka kamin alfarma kaje ku sasanta In yaso ita Hauwa'u sai ka aure ta inta kammala karatunta ba zan hanaka auren wadda kake so ba Amman Nima ka auri wadda Mukai Alƙawari Nida ɗan uwana ko Allah yasa silar auren ku zumuncin mu ya daidaita"
A lokacin jikin Saadik babu abin da yake sai rawa hatta bakin shi Gumi ya jiƙa masa rigar shi, Dama ga zafin ɗaki dan lokacin babu wutar Lantarki.
Inna zatai magana Baba ya ɗaga mata hannu alamun baya buƙatar cewarta, Sai taja baki tayi shuru.
Numfashi ya dinga ja yana ambaton sunan Allah kafin ya samu Nutsuwar Furtawa Baba Kalmar.
"Amman Baba hakan ba zai jawo mana ƙasƙanci ba, Mutumin da baya neman ka Yana matsayin ƙaninka amman ya nuna yanzu Shi mai Kuɗi ne ya janye zumuncin dake tsakanin ku, Baba ka rabu da shi Ka Nema min Auren Hawwa'u ita ce wadda take matiƙar sona domin Allah Nima Kuma nake sonta Amman ita waccan da ban santa ba bata sanni ba Ko sunanta ban sani ba tayaya zan aureta Baba?"
Baba yayi murmushi irin nasu na manya kana yace.
"Ka bar batun Amadu Yaro ne ɗan halak Shu'umar macce kawai Ya haɗu da ita Ina son ka auri Rabi'ah ne Ko ta sanadin auren ku Allah zai sa Zumuncin mu yayi ƙarfi nida ɗan uwana, Fanni zamantakewa kuwa nasan Autana Ba ragon namiji bane in mace Huɗu ya aura zai iya ɗaukar Nauyi ci da shanta Hauwa'u Kuma In Allah ya yarda bata da Miji Sai Kai Kodan karamcin Mahaifanta garemu"
Yayi Biyayyar Amsawa Baba tare da amsar Auren ne badan komai ba sai dan tsan
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
    Â
     *NA*
*AUTAR MANYA*
           *005*
Da sassarfa yake tafiya cikin gidan nasu harya ƙarasa cikin rumfar da mahaifin nashi tare da ɗan uwan shi, suke zaune da sallama a bakin shi Ya Nemi Gurin zama daga Nesa dasu yaɗan Sunkuyar da kanshi a ƙasa.
"Sadauki! dama Babanka Amadu ne yazo min da magana shi ne nace a kira ka Amadu ga É—an naka nan sai kuyi maganar"
Har Lokacin bai É—ago kanshi ba Abbah ya gyara Murya tare da cewa.
"Kwanakin baya na taɓa zuwa da maganar ka fara zuwa Inda nake a kasuwa amman ka nuna baka ra'ayi shine nace yanzu meze hana kazo wajan nawa Kodan Iyalin da zaka fara riƙewa kasan yadda rayuwar ta koma, Batun auren ka da ƴar uwarka Ina son daga na dawo ai maganar auren ku sadaki kaɗai nake buƙata zan baka Gidan zama da Mota sannan kuma ga kasuwa duka Allah ubangiji yasa wa auren ku albarka Amin"
Baba ne kaÉ—ai ya taya Abbah amsawa da Amin amman gogan naku ko gezau bai yi ba sai da Baba ya kuma cewa.
"Wai Sadauki! ba kaji maganar Kawun naka bane?"
A hankali ya É—ago fuskar shi wadda tai jajir abin ka da fari yawanci in yana cikin damuwa Fuskarshi ja take Musamman saman Hancin shi.
Murya a shaƙe kamar an masa dole yace.
"Abba nagode da karamcin auren da kabani ma kaɗai ya wadatar sauran duk na yafe, da farko ina da sana'ata duk da a wajan wasu kamar ta ƙasƙanci ce amman ni a wajena sana'ata tana da Muhimmanci a gareni domin da ita na dogara har na tsaya da ƙafafuna, Gwangwan nake kamar yanda ka sani ina Auna ƙarafa ina siya nima na siyar na sami abinci, Sannan Batun Auren gaggawa dan Allah Abbah ayi min uziri kaɗan zan ƙarasa shirina sabida Kutsen da aka min son samu na zauna agidan kaina amman hakan baze samu ba dan haka zan kama haya Kuma zan mata lefe daidai ƙarfina son samu ta saka kayan Da Mijinta ya ɗinka mata sabida haka ayi min uziri har na kammala komai sena yi magana"
Gaba ɗaya Abbah shagala yayi da kallon Saadik a ranshi kuma yana jin wannan shine Mijin da ya cancata Ƴarsa ta aura sabida ta Ko'ina jarumi ne, Baba kuwa baiji mamakin furucin ɗan nasa ba Yasan shi sarai shiyasa yaƙi amsawa Abbah tayin daya masa Sabida yasan da wiya Saadik ya amsa aikuwa gashi nan ba'a je ko ina ba yaƙi.
"Shikenan Abubakar! Allah yasa albarka a lamarin Na gamsu da bayananka, Kuma Ina fatan Zaka riƙe ƴar uwarka da amana"
Bai Motsa ba, bai kuma tankawa ƙanin mahaifin na shiba.
"Zaka iya tafiya"
Cewar Baba.
Da sauri Abba yace.
"A,a dan Allah Abubakar, ka ƙara komawa wajanta Ku sake tattaunawa sabida Ku fahimci Juna don zaman lafiyar auren ku shine kwanciyar hankalin mu"
Tausayi Abba ya bawa Saadik da É—an sassauci yace.
"In sha Allah"
Yana danne takaicin ta na jiya dan shi ba soko bane baya jin zai iya kai ƙarar mace bada ban haka ba da yace ya mata faɗa ta gyara kalamanta dan gudun kumburin baki.
Kafin Saadik ya kai da ficewa Abbah ya dakatar dashi tare da ɗauko waya ya shiga Kiran Adaah Ƴar Mulkin anci sa'a tai tashin wuri tana bakin gado taga Kiran Abban ta ɗauka Magana ɗaya yayi mata ya kashe wayar Umarni ya bata kamar haka:
"Ki shirya Anjima kaɗan Ɗan uwanki zai ƙara zuwa Ku tattauna Saura naji Kin masa Shirme"
Tana shirin magana ya kashe wayar ƙafa ta fara dirawa tana ita Babu inda zata kuma fita Seta tafi wajan Momi sai dai koda taje Room ɗin Momi bata sameta ba.
Juyawa tayi cikin Rooom ÆŠinta tana gunguni.
Tashi Abba yayi bayan ya direwa Baba damin Kuɗi Amman fafur Baba yaƙi amsa Da damuwa Abba ya maida kuɗin gaba ɗaya Yanayi Baba baiwa Abba daɗi ba wato shi horo wani bin base an maka faɗa ko an maka magana ba.
In har kana da hankali in ka ɓatawa Mutum rai zaka gane a mu'amalance kuma cikin sauƙi.
Sanda Saadik ya fito daga Rumfar Baba ɗakin sa yayi Niyyar wuce wa sabida yana son yau yakai wasu ƙarafa daya siya can ƙofar ruwa shine yasa ma har yayi tashin wuri.
Innah ce ta tare shi da Kofi fal koko aciki.
"Dan Allah karka fita baka sa komai cikin kaba zoka sha kokon nan yaji sugar na sanka gwanin shan zaƙi"
Murmushin daya kasa yi a rumfar Baba ya sakar mata yana ƙarasowa gabanta.
"Innah akwai abin kari a ɗakina fa Naga ni baki sako min tuwo ba Ƙosai kika zubon da Kunu"
Ya faɗa cikin tausayin mahaifiyar shi wato shi ta bambanta a wajan karin kumallon ta soya mai Ƙosai tai masa Kunu gida Kuma tuwo ɗumame da koko.
Bai bata zarafin magana ba ya karɓi Kofin yana ɗan Kurɓar Kokon adaidai nan Abba da Baba suka fito Fuskokin su ƙunshe da Murmushi wanda zai nuna maka girman soyayyar Junansu a fili.