← Book details So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 23

Sashe 1

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *001*

Lumshe idanunshi yake yana shaƙar sassanyar iskar dake kaɗawa a harabar ƙaton gidan a hankali yake jan tsaki ƙasa ƙasa yana sake duba agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannun  shi ya kai mintina goma a zaune babu alamun zata zo, tsaki yaja a karo na barka tai gaba ɗaya ranshi ya gama ɓaci a duniya idan da abin da ya tsana shine jira Kasancewar shi mutum mai kazar kazar da zafin nama, marar haƙuri da ɗaukar raini Zuciyarshi ce take zafi nan da nan idanunshi yayi jajir Gumi na yanko masa daga saman goshin sa ƙurawa hanyarta idanu yayi har ya tashi ze bar wajan ƙamshin turarenta yayi masa sallama tun kafin ta ƙaraso wajan ƙamshin haɗaɗɗan turarenta ya gama cika wajan.

Tafiya take kamar ba zata taka ƙasa ba, cikakkiyar Budurwa ce Ƴar Gajera  baƙa mai jiki, baƙinta irin mai ƙyallin nan ne dan irin sune ko man saka haske suka shafa ba lallai ya amshi fatar suba amman da yake akwai hutu da jin daɗi a tare da ita se Baƙin nata ya murje ya ƙara mata ɗan karan kyau.
Babu wani abu a fuskarta mai haske se fararen idanunta waɗanda baƙa ƙirin ɗin ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata idanun nata Zanan idanun nata kuma se yayi kamar ta shafa kwalli daga saman hancinta kuma gumi ne wanda ze tabbatar maka da ita ɗin babu sauƙi mafaɗaciya ce bata wasa ba, tana tafe tana huci harta ƙaraso inda yake.

       
Ƙerere ta tsaya a saman kanshi tana karkaɗa jikinta ta saka hannu ta kama ƙugunta, Nuna wa yayi kamar bai san da wanzuwarta a wajan ba, wanda hakan seya ƙara tunzura zuciyarta wannan wani irin ƙasƙanci Abbanta yake son yayi mata duk faɗin samarin ta babu wanda Abbanta zece ta aura se wannan gajan kuma yaro ƙarami wanda bai fi sa'an haihuwar ta ba dan bata jin zai girme mata, tun jiya take son fahimtar da Abban ta cewar ita fa tana da wanda take so yake son ta amman yaƙi sauraren ta akan wannan kucakin, Tun da take da Abbah bai taɓa Yi mata faɗa kamar na jiya ba kuma duk silar zuwan wannan yaron da Baban Chiranchi Ya turo wai ya aure ta Tsaki taja acikin zuciyarta tana kau da tunanin Ɓacin ran da suka kwasa jiya ita da Momi Mahaifiyarta akan zuwan wannan ƙolon.
Jitai zuciyarta na ingizata akan ta gargasa masa baƙaƙen maganganun da zai ji haushi Ya ƙi dawowa.

Saadik wayar shi ya ciro ya kunna data ya shiga facebook ya na duba posting ɗin jama'a gaba ɗaya ya shagala ya ma mance da ƴar rainin hankalin yarinyar dake gabanshi wadda taci albarkacin Mahaifin shi wanda umarnin shi ma yabi har yazo wajanta dan shi ne ya tursasa shi akan sai lallai yazo ya nemi auren ƴar ƙanin nashi ko Allah yasa ta silar hakan zumuncin su ya ƙara ƙarfi.
Bai taɓa zuwa gidan Kawun  nashi da girman shi ba, se yau hasalima ita yarinyar da aka turo shi wajanta bai ko taɓa saninta ba bare yasan sunanta duka se yau ɗin da yazo gidan bisa tirsasawa da bin umarnin mahaifan shi.

Takaicin yarfin daya mata ne ya fusata ta cikin zafin zuciya ta miƙa hannu ta warce wayar hannun nashi tai wurgi da ita jikin ginin dake kallon su kafin ta soma magana a zafafe!
"Aikin banza aikin wofi an gaya maka talaka yana da alfarmar wulaƙanta mai kuɗi kai ɗan gidan uban waye! da zaka.......
Bata ƙarasa faɗin maganar ba tai saurin faɗuwa a wajan tai zaman ƴan bori hannu biyu ta sa tana dafe kuncin ta sabida azababbiyar gilmawar wutar data gani a cikin idanunta.
Ba kuma wutar bace zafin Hannun Saadik! Ne ya gigita ta, Akanta ya tsaya yana huci bayan ya ƙarasa sauke mata marika har guda uku a jere Huci ya saki mai zafi yana Naushin Iska Allah ya bashi zafin rai na masifa sam baya ɗaukar raini baya son wasa shiyasa ko acikin gidansu Yara na shiga hankalin su in suka jiyo muryar shi kai babban ma idan Saadik ya rikice masa shiga hankalin sa yake.
Cikin dakakkiyar Muryar shi wadda ta ratsa dodon kunnenta ta kuma hautsina mata Æ´aÆ´an hanjinta yace mata.
"Wuce kije ki tattara min wayata banza shasha sha ballagazar mace"!
Kuka take Tuni Kuncinta ya haye kuma taƙi koda motsi a wajan sabida masifar kafiyar ta.
Tsaki yaja cike da fushi ya wuce fuww yabar mata wayar batare daya haɗa wayar tashi ba,bare ya ɗauka, sabida yana jin idan har ya tsaya a wajan ze ɓallata ɓallin masifa wannan tasa yayi gaggawar barin Gidan.

Ta ka ƙasa yake kamar ze tsaga ta tsananin zafin zuciyarsa tasa har numfashinsa na ƙoƙarin barin gangar Jikinsa.
Daga gadon ƙaya zuwa ɗorayi Chiranchi da ƙafa yaje gida Yana shiga Ɗakinsa dake soron gidan ya shige tare da faɗawa saman katifa yana lumshe ido hoton fuskarta yake gani acikin idanunshi gaba ɗaya haushi da tsanarta na mamaye zuciyar sa, sam baya son mutum mai izgili da girman kai, baya son mutum mai wulaƙanta mutane, domin baka san baiwar da Allah yayi wa kowa ba.
Anya zai iya bin umarnin Baba? shi kam yana jin yafi ƙarfin mace ta wulaƙanta shi duk kuɗinta duk mulkinta domin bai nema daga wajanta ba, Shi talaka ne amman mai zuciyar nema domin ta ko ina Allah bai kassara shiba ya bashi rai da lafiya da dakakkiyar zuciyar neman halak ɗinsa uwa uba wadatar zuci wadda yake jin in mace huɗu ya aura zai iya ciyar da ita da halalin sa.
Mirginawa yayi tare da miƙewa, ya fita cikin gidansu bakin Rijiya ya tsaya zai ɗebi ruwa a bokitin daya riƙo don ya watsa a jikinsa sabida Zafin ranar da ake tsulawa a garin.
"Kawu Saadik kawo na zuba maka ruwan"
Inji Khadija ɗaya daga cikin Jikokin gidan nasu waɗanda Innar shi ke riƙewa a wajanta.

Fuska babu walwala ya miƙa mata Bokitin ta cika masa shi da ruwa ya ɗauka ya koma cikin ɗakin shi ya shigar banɗaki ya watsa a jikinshi ya fito Farin yadi marar nauyi ya saka ya fesa turare mai sanyin ƙamshi ya fita zuwa cikin Gidansu sai Lokacin yaji zuciyar shi na masa sassauci na daga Ƙuncin daya kwaso Innah na tsige zogale Zarah na gefenta nashan Koko.

Da gudu ta aje kofin tazo Jikin shi ta É—ane shi ta hau yi mashi surutu.
"Kawu Saadik Innah tace dambu zatai mana, Kuma ÆŠazu Baba yace kaje wajan Matarka wai aure zaka yi?"
Murmushi ya yi kaÉ—an tare da shafa kanta.
"Zarahh Sarkin surutu mai shan koko da rana"
Sai Lokacin Innah tayi magana.
"To ya za'ai kasan Rigimar Mutuniyar taka nayi ranar abincin ne yau wai Ummi na aika kai ɓarzar tsakin masara Wallahi tafi awa biyu nace Nanah ta bita itama shuru, Ita kuma wannan sarkin cin se kuka take yi shiyasa na bata sauran Kokon Babanku"
Matsowa yayi ya zira hannu cikin zogalan yana tayata Aikin zagewa.
Batare daya ce komai ba.
"Wai yaya kukai da Gidan Kawun naka?"
Cewar Innah.
Cikin son ya basar da maganar dan tina wa ma ɓata Masa rai yake, Ya ɗan langwaɓe kaɗan tare da cewa.
"Innah nima fa yunwar nake ji, amman zan fita shago In kika gama ki bawa wani ya kawo Min"
Sarai tasan dan ya basar da maganar ne, Setai murmushi ta shiga yi masa fatan dawowa lafiya zarah na bashi saƙon abin da zai tawo mata dashi yana Murmushi yana amsawa har ya bar Gidan.

Ido jajir ta faɗa cikin katafaren falon gidan nasu wanda ya kusa girman wani gidan ihun ta har cikin ɗakin baccin momi wadda ta fito a guje dan masifar sauri zaninta har kunce wa yake yi a gigice ta nufi wajan Yarinyar tata Ƴa ɗaya tamkar da Goma kenan Ƴar gata dangin kitse a barka a inuwa ka daskare a saka ka a rana ka narke, Cikin tattali da Riritawa tamkar tsoka ɗaya a miya ta Rungumeta duk a kiɗime take mata magana.
"Babyn momi waya taɓa min ke kika shigo kina kuka kin san yadda kukan ki yake ɗaga min hankalina wallahi kaina har juya mini yake sabida azabar faɗuwar gaban da kukan ki ya haifa mini"
Shure ƙafafunta take tana ƙara sautin kukan tana janyo hannun Momi zuwa fuskarta Jikin Momi ne ya hau rawa sakamakon shatin yatsun data gani kwance a kunci shalelen tata a zabure tace.
"Kan uba waya miki wannan illar lallai ya tafka ganganci domin zanyi shari'a da kowa ye sannan kuma zan É—aure kaf ahalin su har igiya tayi rata dan uban sa!"
Sangartaccen kuka ta kuma saki lokacin Momi ta zauna ta ɗorata a kan cinyarta In kaga yadda sukai zaman seka yi dariya sabida ita aba ƙatuwa an tashi an ɗora ki a saman cinya ko Kunyar hawa ita kuma bata jiba.
Chapter 1 · 0% Book details