← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 48

Sashe 9

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ina nan zaune a bakin katifa naji alamar shigowar mutum.
Inna ladiyo ce ta dawo hannunta É—auke da kwanon abinci.
Tashi nayi na karba a hannunta kana na ajiye a tsakar É—akin.
"Sannu na barki ke kaÉ—ai koh,naje kawo miki abincine,sannan munyi magana da hajiya yanzu.
In kinci abinci kizo zatayi magana dake,ki kula sosai nasan mairo ta fadamiki haka koh?"
Daga mata kai nayi alamar ehh,daga nan ta juya ta fita,zama nayi a gaban kwanon kafin na bude a hankali.
Sakwarace a ciki da miyar ganye,kafin nasaka hannu ma sai ƙamshi takeyi.
Ban bata lokaci ba na saka hannu bayan nayi bismillah na fara zubawa cikina.
Duk yanda naso na cinye malmalar sakwarar guda biyun kasawa nayi,dan ina cin guda ɗaya naji na ƙoshi,ta biyun kada na taba..
Kwanon na tattara wai zan fita dasu,a nan gizo ke saƙar ina zan nufah a wannan tangamemen gidan haka..
Wani mutum na hanga a gefe dani na tambayeshi hanyar kitchen,gyaran wasu fulawowi yakeyi,da alama aikinsa kenan.
"Baiwar Allah ta ina zansan inda hanyar madafa take,wannan ai sai su ladiyo,amma naga sunayin wancan corridor da yayi dama"
Godiya nayi masa daga nan nayi wajen daya faÉ—amin.
Tafiya nake ina Addu'a a raina har na samu kaina a wajen dana tabbatar madafar ce,duk da bayyimin kama da wanda na saba gani ba. Wannan waje haka ƙato.
Kwanon hannuna na ajiye akan wani tebur dana gani a gabana,har na juya zan fita naji muryar wata matashiya.
"Ke daƙiƙiyar inace dazaki ajiye kwano a wajen da ake yin girki,ko kyauyen cinki bai nuna miki canne wajen wanke wanke ba"
TafaÉ—a tana nuna min wani waje mai dan rami da famfo a wajen,wanda ni sai yanzu ma na kulada shi.
Maida kaina nayi kan fuskarta,budurwa ce ko kuma nace ƘARAMAR BAZAWARA(littafin ummu najam amarsisi nayi miki miss).
Domin daga ganinta bazata fini ba.
Wasu kwanuka take jerawa a cikin wardrope,fuskarta a haÉ—e kaman anyi mata mutuwa.
"Daƙiƙiya? In daƙiƙiya ce ni ashe kekuma kece babbar daƙiƙiyar wacce ta daɗe ma a ciki,domin in ƴan aiki kike ƙira d daƙiƙai to kece babbarsu wacc....."
"Sumaimah ya isa haka,ke kuma Ummi bai kamata kina walaƙanta mutane ba duk sanda kika gansu,ke idan ba mai kuɗi ba to kowa ba kaman ba mutum ba haka yake a wajenki"
Wacce ta ƙira da ummin ta kalla tana yiwa faɗan,ana mata maganar ma tana wani fisfisgewa,wanann daga gani bata da daɗi,in kuwa hakane halinta to batada kirki sam..
"Inna ladiyo wai bakya ganine,ya za'ayi kawai ka kawo kwano ka ajiyeshi a wajen da ake abinci"
"To naji amma dai ai kinsan sabuwar zuwace ko aiki bata fara ba"
"Duk da ai......"
"Kinga ya isa haka,kici gaba da da gyaranki,ke kuma muje na gabatar dake a wajen matar gidan,anyi sa'a ma yau tana gidan"
To nace mata tareda bin bayanta muka fice daga wajen.
Kafaren wani hamshaƙin falo na tsinci kaina a ciki,dama irin wannan gini haka dole mutum yayi tunanin irin kayan alatunnan a cikinsa.
Wata mata ce a zaune akan É—aya daga cikin kujerun falon,ta saka wani kaya da ban wanne iri bane,amma ko daga gani kasan masu kyaune da tsada.
Abinda yafi bani mamaki shine,meyasa nakejin faÉ—uwar gaba dana haÉ—a ido da ita na farko,hmm anya kuwa wannan irin mutanen da mutum zai iya sakewa dasu?.
Tsugunnawa nayi a ƙasa kaman yanda naga inna ladiyo tayi.
"Hajiyah barka da warhaka,g ta nan na kawomiki itah,tazone domin ta samu aiki,da fatan za'a taimaka"
"Hajiyah barka da yamma"
Nima na fada cikin girmamawa,ganin ta kafeni da ido.
Can munyi shuru kaman ruwa ya cinyemu,nida inna ladiyo sai zazzare ido muke.
Jan ajiyar zuciya tayi tareda zare farin glass É—in dayake idonta.
"Ladiyo banason wani magana yanzunnan,kuma ba kin faÉ—amin zuwanta ba É—azu...huhh wancan yaron dama ya dawo gidan,naji waccar tsohuwar nayin mitar kan kan a samu masa wata mai aikin,tunda waccar mun sallameta,kuje ki nuna mata yanda zatayi,in kuma ta kuskure itama ya koreta kaman yanda ya saba toh sai tasan yanda zatayi.
Albashinki dubu ashirin a wata shin yayi miki ko kuwa"
Tun daga ambaton aikin naga ladiyo ta sha ruwan jikinta,koma menene naga da alamar wanda zanyiwa aikin bashida daɗin sha'ani,koma dai menene tunda naji batun dubu ashirin zanyi iya ƙoƙarina wajen ganin nayi nasara.
"Yayimin hajiyah nagode Allah yaƙara buɗi yasa kifi haka"
"Ameen ku tashi ku tafi toh,in wata yayi zanyi miki magana,idan har kina gidan har zuwa lokacin. Sannan kuma karki sake ki nuna masa cewar nina ɗaukeki aiki,kawai kice masa kin fito ne a jerin wacce zatayi masa aiki. Abu na ƙarshe banason ki yaudareni,Sannan ko nan gaba na buƙaci haɗin kanki akan wani abun dole zaki bani"
"Inshaallah hakan bazai gagara ba hajiya,kuma da sannu zanyi yadda kika ce"

____∆∆∆____

Ya yage takardu sunfi guda biyar yana zubarwa,kansa ya kulle ya rasa ma mai zayyi.
Kansa ya riƙe tareda jan gwauron numfashi.
Kwanansa uku kenan da zuwa office amma yagagara yin komai kaman nada,abubuwa da dama sun canja ciki harda tsarin wajen,abun yana cin zuciyarsa ganin duk yanda yakeson aikinsa ya tafi a gaggawa amma abu ya gagara. Duk ƙoƙarin daya dungayi a baya ya tara shaidu duk sun tafi kaman anyi ruwa an ɗauke.
Kansa ya É—ora a kan kujerar yana jinata a hankali idonsa ya rufe.
Yaji alamar buɗe ƙofa wani ya shigo,tun kafin ya bude ido yace.
"Eemran mai Abbah yace,ya bamu izinin binciken wanann gidan?"
"Am sorry sir amma har yanzu ya ƙi saka hannu,a cewarsa wai bai kamata ka fara babban aiki irin wannan ba daga dawowarka"
"Hmmm kaida Neelah ku fara aiki cikin sirri,bazan iya tsayawa da aikinnan ba"
"Amma yallabai akwai hatsari muyi batareda sanin sama ba"
"Hatsari ya wuce wanda nake ciki,kullum hankalina a tashe yake da tunanin a kowanne irin sakanni za'a iya sake farautar rayuwata ba, shin akwai abinda yafi haka hatsari Eemran?"
Duk yanda yake boye damuwarsa tun bayan dawowar tasa,amma kana kallonsa zaka san baƙaramin dauriya yake ba.
"Hakane kam ogah lamarin abin abun a dubane,nida Neelah Inshaallah zamu iya ƙoƙarinmu wajen ganin komai bai sake zuwa da matsala ba.
Wanda suke aikata waÉ—annan abubuwan da sannu zasu zo hannu.
Hular sa ya É—auka ya É—ora akan kayan uniform É—innasa,wanda suka sake fito da jarumtarsa a fili.
Yau baizo da drivernnasa ba wai mai ɗakinsa ta haihu,dan haka da kansa ya tuƙo bai ɗauki wani drivern ba,domin dukkansu ba yarda yayi dasu ba,yasan duk yaran hajiyah maryam ne.
BuÉ—e motar yayi zai shiga,tsayawa da shiga motar yayi sanadiyyar wani akwati daya gani a wajen zaman drivern..
Kaishi yayi É—ayan sit É—in,sai bayan ya zauna kafin ya É—auko shi ya buÉ—e..
B'era ne matacce a ciki sai wata wasiƙa da jan ink.
Chapter 9 · 0% Book details