Sashe 30
Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hajiyah Maryam tana zuwa nan da labarin muryarta da ƙyar take fita saboda kuka.
Yayinda nikuma a nawa bangaren badan kukan da take ba bazan taba yarda hakan ya faru ba.
Cigaba tayi da maganar wanda zuwa yanzu tana zaune tabas a tsakiyar É—akin..
"Soyayyar yarona wanda ko zafin haihuwarsa bangama ji ba,ita tasakani amincewa da kuÉ—urinta,a tunanina idan yana raye ko bana nuna masa so to ba matsala,ashe vansan jure ganin É—anka yana wahala bakada ikon taimaka masa hakan yafima mutuwar zafi,koba komai Muhammad da Amina su sun huta.
Haka na shafe wata guda ina kulada ɗana wanda nasaka masa suna Ahmad,bayan wata daya ya ƙare nasake roqarta ta ƙaramin wani watan.
A ƙarshen wata na biyunne na miƙa mata yaron,yayinda wata nurse tayimin allura yanda alamun haihuwar danayi zasu gushe.
Ina kuka ina komai haka tasaka wani dattijo data cikashi da kuÉ—i ya kaini gida,akan wai tsintata yayi a sume a gefen titi inda mukayi accident ,dan cewa tayi wai Æ´an uwan Amina ne suka kashe Muhammad ita kuma suka tafi da itah.
Kowa sai tsinemusu yakeyi,harda marigayiya Amina wacce bataji ba bata gani ba.
Kukan mutuwar Muhammad ne ya dawo sabo saboda bayyanata,kowa na cewa ana ta ƙiran number Amina amma bata shiga da gangan dama ta gudu.
Bayan sati biyu da faruwar hakan har sannan ko magana banayi,saboda kewar yarona da kuma mutuwar abokan zamannawa wanda na saba dasu.
A lokacinne kuma wata mata tazo ƙofar gida ta ajiye ahmad ta daddare haɗeda wasiƙa ta tafi.
Wasiƙar tana ɗauke da cewar wai ɗan Amina ne ta mutu su kuma bazasu riƙe jinin Muhammad ba,dan haka ga ɗanmu nan,sunansa Ahmad.
Abinnan yayimin ciwo sosai amma ba yanda zanyi,kowa bayyi na'am da Ahmad ba,saboda baƙin Amina da suke gani,sai hajiyah Mammah wacce ta rungumeshi tamkar jikanta,hakanne kuma yasa tasake fari a idon mutanen gidan,sai a sannan nagane ashe abinda take kenan.
Kwanci tashi bayan yaye har hajiyah Mammah ta yaye Ahmad kowa ya manta abinda ya faru,nikuma saboda bana kula Ahmad yasa aka faramin ganin kaman dan bani na haifeshi bane,haka na toshe kunnuwana badan komai ba saidan kare lafiyar yarona,duk da nasan kularda take bashi na munafurcine amma dai yanamin daÉ—i.
Ana cikin hakanne Aliyu ya dawo,wanda nasan duk matsawar hajiya Mammah ne,lokacin da aka tada zancen aurenmu kowa ya amince,harshi da dama sona yana zuciyarsa,inaga kumani da daman munyi yarjejeniyah da itah.
Auren bayyi wani armashi,bansan kosu yayi musu ba,amma nikam jinake kaman an ɗauramin mutuwa,kulawar dayake banine ma da zuciyarsa ɗaya,tunda nasan shi bashida laifi shiyasaka ni barin wani abun ya wuce,tunda nasan ƙaddarata ce.
Bayan aurenmu da sati ɗaya zainab tazo gidana ina kuka na faɗamata mai yake faruwa,shima kuma dan ta faramin faɗane akan kiyayyar danake nunawa Ahmad. Bayan na faɗamata saida na gargaɗeta tayi shuru amma sai taƙi.
Lokacin tana goyon Neelah, tazo gida wunin arba'in,wannan magana dana faÉ—amata nayi dana saninta yafi cikin kwando,domin a daren tana shirin faÉ—awa hajiya Fatima bakinta ya manne,tayi tayi tai magana abu ya gagara,haka aka bari akan saida safe za'a kaita wajen magani.
A daren aka nemeta sama da ƙasa aka rasa,tun masu magani suna cemana tana gari kaza har muka daina nema muka zubawa sarautar Allah ido.
A sannan ɗin ban daddara ba naso ɗaukar mataki amma banyi nasara ba. Ƙarshe ma wani abu hajiyah Mammah tasakamin a jikina,duk lokacin danayi yunƙurin bata mata shiri sai naji kamar yana zuqar jinina ta ciki.
Haka nacigaba da fama da wannan yanayi babu wanda ya sani har na haifi Maimuna,koshi Aliyu bai san mai yake faruwa.
Tun bana ganin laifin Aliyu da su Aina'u har yazamo ya fara shafarsu,kuma a lokacin ne na nemi aiki na fara saboda ya É—aukemin hankali.
Shekarar mu biyu da aure muka tare a sabon gidan Aliyu,wanda shine wannan,a sannan ne kuma aka bashi muƙamin general.
Naji daÉ—in dawowar wani gun kuma banji daÉ—i ba,saboda ninake kulada Neelah,sannan ina kallon Ahmad duk da bana kulashi,amma kuma koba komai na daina ganin hajiyah Mammah a kusada ni. Dan babu É—an adam dana tsana a rayuwata kamarta.
A haka rayuwar tacigaba da tafiyah harna haifi su Saleem inada cikin Fatee.
Lokacin na zama babbar lawyer,shikuma Aliyu yazama air marshall a shekarar,wanda duk da saka hannun abba nah,saboda rashin Muhammad yasa yake ganinsa tamkar magajinsa.
Can you imagine wani kisan raini hankali wai su abba Hamma da hajiya Fatima sun dawowa daga umarah tayar motarsu ta kunce motar ta ƙone. Ko qur'ani aka bani na danna nasan aikin hajiya Mammah ne,amma ya zanyi toh shikenan suma ta gama dasu.
Lokacin da abban nah yaji wannan labarin shima ciwon zuciyarsa ya tashi,dama ba lafiyace dashi sosai ba,yamayi retire.
Bayan wani lokaci Aliyu ya damu sai ya dawo da hajiyah Mammah gabansa,saboda ita kaÉ—aice dukka yaran gidan sunyi aure. Mariya kamma watan haihuwarmu kusan É—aya,ta haifi Mulaifah tanada cikin na biyu.
Ita a haihuwa ta rasu É—an shima ya koma,nikuma na haifi Fatee aka sakamata sunan hajiyah Fatima.
Neelah kuma saboda babu hajiyah Fatima saina kaita gidan marayun dana ke kuladashi,lokacim ma ba babba bane,amma tunda bazan iya riƙeta kusada ni ba gudun cutarwar hajiyah Mammah gwanda na kaita inda zata dunga ganin yara sa'anninta,kuma atleast zan dunga ganinta kullum.
Batayi ko wata É—aya bama Aliyu ya kaisu india itada Ahmad wajen amininsa zasuyi karatu a can.
Kasancewar lafiya suke yasa na kwantar da hankalina na cigaba da kulada wanda suke gabana.
Ana nan har akayi auren Maimuna,itakuma Neelah bayan sun gama makaranta ta dawo gida tana training É—inta a nan abuja,amma bata zauna a gidan ba saita zauna a barrack,shikuma Ahmad bai dawo ba sai daya gama komai.
A tunanin sa kokuma nace tunanin da aka saka masa kuma yake gani,nafi kowa tsanarsa a duniya,nan kuwa a kaff rayuwata dana tashi na tsinci kai na a uwa,kullum banda lissafi saina suwa yake tareda su,cutar dashi suke kokuma ahah"
Kukane ya kubce mata wanda nima yasakani kukan,dama abinda yake faruwa kenan, tabbb lallai idan kaga mutum ya kabarshi,wato kenan ita kura ce da fatar akuya tazo ta labe anan wajen.
"Kenan matar dana gani da wata ta shige jikin bango ranar danaxo gidannan......."
ÆŠago ido hajiyah Maryam tayi tareda É—aga min kai.
"Ita kika gani ba kowa ba,itada wanann shegiyar Raheenan,wacce ta É—aukemin yaro lokacin dana haifeshi,su ne kika gani inda sun san kin gansu da tuni bakya numfashi,shiyasa nake cemiki kiyi taka tsantsan kada ki maimaita kuskurena."
"Wannan hoton dana gani shine baban Ahmad,amma kince bai san Ahmad ba,ya na ganshi kuma a hoton?"
"Bada shi akayi hoton,ni kaÉ—ai nayi hoton ranar sunansa,wanda na roqi hajiya Mammah ta barni nayi,shidin bayarwa nayi aka hadamin kamar yana cikin hoton"
Uhm jijjiga kai nayi tareda jajanta lamarin,shin waye zayyi tunanin abinda yake faruwa kenan idan ba gani yayi ba,lallai in kuwa hakane akwai aiki a gaba.
"Akwai wani aikin da zakiyimin Sumaimah"
Hajiyah Maryam ta faɗa tana tafa ƙafaɗa tareda jan majina,wanda tafito saboda yawan kukan data sha.
"Please ki zauna dashi a wannan kwanakin,na É—ago cewar shiba É—an Aliyu bane,dole za'a faÉ—amasa waye ubansa,kuma ace shi É—an tubabbiyane wacce Æ´an uwanta suka kashe ubansa,daganan wanda bai sani bama zai sani,dan haka be with him"
"Ammm........amma taya zan zauna dashi bayan baisan ni wacece ba, bayason ina yin kusada shi alhalin yana ganina a matsayin wacce ba muharramarsa,saida nayi miki alƙawarin zan taimaka miki wajen ganin mai yake faruwa,sannan daga gobe zan fara aiki a sashen hajiyah Mammah,saboda gano wani abun"
"Ahah bazan sakaki wannan aikin mai hatsari ba idan tagano wacece ke bazatayi tunani na biyu ba zata kasheki,ta kashe É—anki. Kinsan ke wacece yanzu haka a wajenta kuwa......?
Matsafanta sun nuna mata wacce zata kawo ƙarshenta matar ɗan data raba da iyayensa ne wato Ahmad. Sannan matar dazatayi sanadiyyarta itace uwar ƴaƴan sa. Abinda bata sani ba ya riga yayi auren,da ta sani bazata hana Mulaifah aurensa ba,hasalima ita zata ƙarfafa hakan. Shiyasa kada ta gano matsayinki ba yanzu ba tukunna"
"Nasan da hakan kuma zan kiyaye,amma ki sani nima rayuwar É—ana data mijina nake dubawa"
"Shikenan kije ki kwanta dare yayi zanyi tunani akai zuwa safiya."
Da haka na bar sashen hajiyah maryam É—in zuwa namu sashen,duk da banida waya a hannuna amma nasan dare yayi sosai,dan tsitt kakeji babu motsin komai a gidan.
Daidai nazo farfajiyar gidan zan wuce sashenmu naga mata guda da alkyabba,wadanda dai nagani farkon zuwana gidan.
Yanzu kaman wancan lokacin ta jikin katanga suka wuce,daidai inda naga wannan zanen.
Jijjiga kai na nayi tareda cize baki,wannan karon ko É—ar na tsoro banji ba na wuce.
"Aradu kaman yanda kika gama taggunki to sai ya karye,kodan saboda rayuwar mijina dana É—ana bazan saurara miki ba sai asirinki ya tonu,wanda kike tsoron karsu gane kuma kike komai dominsu wato Æ´aÆ´an ki,saisun gane wacece ke"
To fah Sumaimah in action.......let go!!!.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...23...