← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 48

Sashe 36

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Number dakinsa kawai yabashi tareda yimasa alamar ya sameshi a can É—in,
Yagane mai yake nufi kuwa,sai yayi shuru da zancen akan zai sameshi a É—akin.
A zaune yake da labtop akan cinyarsa lokacin da musbahu yayi sallama a É—akin,bayan ya zauna shuru sukayi babu wanda yace komai,saida suka É—an ja kaman mutuna kafin Ahmad yayi masa magana.
"Naji kana magana akan goje,ga dukkan alamu kasanni lokacin ina a matsayinsa,kuma kasan inda na zauna"
Kallom mamaki Musbahu yabi Ahmad dashi kafin yace.
"Ya kake magana kaman ba kaine goje ba,shin mai yake faruwane,ka rasa hankalin ka ne a hatsarin dakayi,shiyasa ka manta komai,amma bakayimin kamada wanda ya rasa hankalin sa ba"
"Eh ba hankalina na rasa ba,nayi recovaring hankalina ne,saikuma na manta rayuwar danayi a wanda kake faɗa. Kafin muce komai zanso nasan wanene kai kuma menene alaƙata dakai a rayuwar bayan.
Sunana Ahmad Aliyu,General under Investigation division"
Zaro ido Musbahu yayi jin matsayin da Ahmad ya faÉ—a.
"Shin mafarki nake kokuma idan har kaine goje yaushene kayi karatu haka,a sanina dai dabanci kakeyi da kuma aiki ma Æ´an siyasa. Sannan kana nufin baka ganeni bane,nine fah Musbahu yayan Sumaimah matarka,duk da bakaje wajen É—aurin aurenba amma ai muna haÉ—uwa a gari san......."
"Bangane wanne labari kake min ba,kaine yayan matata,kuma banje wajen ɗaurin aure ba,meyasa toh? Barina baka labarin abinda yasa bansan kokai wayeba,sannan inaso ka bani labarin abinda yafaru daga farkon rayuwata a wannan gojen dakake faɗa har ƙarshe,harma da labarin ita matar tawa."

Bayan yabashi labarin abinda yasameshi ya rasa hankalin sa har yayi rayuwa a matsayin goje,ba ƙaramin mamaki yabawa Musbahu ba. Shima labarin rayuwarsa daya sani a matsayin goje ya faɗamasa,da yanayin aurensa da kuma yanda Sumaimah tasha wahalar zaman aurensa harda tafiyar dayayi ya barta.
Abin ba ƙaramin tayarwa Ahmad hankali yayi ba sosai,shin dama haka yake a rayuwar,a ina zai samo wannan baiwar Allah,mai zaice da ita irin wannan abun daya jawo mata.
Kama kai yayi tareda jan numfashi,tsawon lokaci ya É—auka yana jimamin abinda ya aikata.
"Zan shirya komawa gida gobe,zamu tafi ka nuna min itah"
"Ahah hakan bazai yiyu ba general,duk da nasan kai ogah ne,amma inna bika zan samu matsala a nawa training,nayi ƙoƙari sosai kafin na samu wannan matsayin.
Sannan kuma ita kanta wacce kake son zuwa wajenta bata nan,ta tafi garin abuja aikatau,saboda bayan tafiyarka hatta makarantar daka biyamata kuÉ—inta had ta gama sun hanata certificate,duk wani abu mutane sun washe ganin an É—au shekara baka dawo ba,shiyasa ta tafi neman abinda zata rufamusu asiri"
Wani irin sanyin jikin Ahmad ya sake jin wannan batun,gabaÉ—aya ya rasa mai yake masadaÉ—i.
Wunin ranar gabaɗaya ƙareshi sukayi Musbahu yana yimasa labarin goje,batun zuwa wajen Sumaimah kuwa sun barshi akan suna komawa zasu nemi inda take yaje.

∆∆∆∆

Sumaimah {POV}

Bayan wata biyu.....

Yau tun safe na tashi da tashin zuciya,abu kaÉ—an sai naji zanyi amai,da sabuluna nafarayi a banÉ—aki.
Bayan rana tayi har sannan ban saka komai a cikina ba,saboda banajin son komai.
A zaune muke nida ummi bayan mun gama aikin ranar,inata magana niban kulaba ashe kallona takeyi,É—aga mata gira nayi da alamar lafiya.
"Lafiya kalau,kawai naga kin sauyaminne kwanannan,duk da ke farace amma ƙin ƙara fari,ga wayan bacci dakikeyi,komai inkin fara saikice kin gaji"
Maganganun da ummi tayi dukka nima na kulada su,amma babban abin tashin hankalin shine abinda na zarga,wanda ban kawo shiba sai yanzun.
Wani zabura nayi nai banɗakinmu da sauri,a gaban madubi na tsaya ina kallon kaina,mamana na kalla wanda naga sun ƙara girma,rabonsu da haka tun inada cikin Sayyid.
Zaro ido nayi tareda shafa cikina,rabona da al'ada wata biyu kenan,wayyo mai nake tunda ban kulaba sai yanzu.
"Innalillahi yanzu ya zanyi kenan,kenan ciki na samu a ranar? Mai yasa dukka biyun suka faru a rashin saninsa,nasan wannan zaisan nasane,amma da wanne zai kalleshi shine tashin hankalina,ahhhhh"
Ƙarar danasaka ne yasa ummi yin magana daga cikin daki.
"Sumaimah lafiyarki kuwa?"
"Ba komai ummi"
Fitowa nayi daga bnaɗakin ina rarraba ido,yanzu wazan tunkara da wannan zancen kenan,nasan hatsarin danake ciki nida wannan cikin Allah ne yasan iyakarsa. Don yanzu su hajiyah Mammah babban burinsu shine gano ni wacece,tunda yanzu babu komai ya ruguje. A bangaren hajiyah Maryam kuwa kullum ƙara rauni takeyi,Neelah kuwa batada lokacin kanta tunda Ahmad ya tafi ya barmata ragamar hidimominsa.
Hanyar sashennasa na nufah,haka kawai na tsinci kaina dayin hakan.
Buɗewa nayi na shiga,alamun rashin mutum duk sun nuna a wajen,har ƙura ta taru a falon.
Ina shiga naji wani ƙamshi a falon,wannan wanne turarene haka dayaƙi washewa tsawon wata biyu.
Ɗakin na bude na shiga,nan kamma har yafi falon,dan ji nayi wata nutsuwa tana sauƙamin.
Duddubawa nakeyi ina neman turaren,saida na shinshina dukka turarensa amma ban jishi a ciki ba.
Wardrobe ɗinsa na buɗe,inda ya lanƙaya kayan daya saka a gefe,a jikinsu turaren yafi yawa,ɗakkosu nayi ina shinshinawa,na daɗe ina abu ɗaya,sai daga baya nagane ina abu tamkar kuliyah. Kuma mai wai tsaya,kenan ba turare hancina yake shinshinowa ba,guminsa ne,yaushe na zama mai iya shinshino yanda gumin mutum yake?.
Ajiye sauran kayan nayi na É—auki riga É—aya na boye,kan gadonsa na faÉ—a,ahhh nan ma jinayi kamar yana kai. Nice nake kewarsa kokuma É—an cikina duk bai shafen ba,tunda naji daÉ—in kwanciyar bacci zanyi kawai.
Bacci nayi na ƙoshi sai don kaina natashi,amma duk da haka banji ya wani isheni ba,mitstsike ido nayi,sai sannan na hango gari ta window yafara duhu.
What bacci nayi na kusan tsawon awa shida ko biyar.
BanÉ—akin sa na faÉ—a da sauri nayi alwala,mayafin kaina na yaye nayi sallah kafin na fito zuwa kitchen É—insa ko zan samu abinda zai iya shiga cikina.
Tundaga lokacin dana gano inada ciki,sai yazama kamar hurashi akeyi,tsorona É—aya nasan zayyimin girma fiyeda na sayyid,dan daga ganinsa ma.
Nashiga damuwa sosai da lamarin,ga banida waya ta faɗi a ruwa bare na ƙira inna na faɗa mata.
Kullum inna tashi da safe sainayi shiri mai kyau,gashi na tsiri saka hijabi da kuma É—aurin zani akan cikin. Sati uku da fara laulayin har na rame na yi fayau.
Fitowa nayi daga wanka kware kwaren danayi,to wankane babu sabulu,towel ne a jikina ina gogewa ruwan,kullum a banÉ—aki nake shiryawa,amma yau dayake naji su ummi suna aiki a babban falo shiyasa ban yi a banÉ—akin ba.
Motsin tafiya naji,hakan yaa na rarumi hijabina na saka.
"Dama kin ajiye hijabin,wannan boye boyen ya isa haka,nariga nasan cikine dake malama,inna tacemin wai ai mijinki ya kawoki ziyara,shine daga bada tsarabar ciki sai ya tafi,bazai tsaya a gaisa ba?"
Sauƙe ajiyar zuciya nayi bayan naji bayanin ummin,kenan daman sunsan inada ciki,musamman abinda inna ladiyo tafaɗawa ummi,yayi min daɗin matuƙa,kuma ya kareni daga amsa tambayoyi.
"Miye kikayi wani tsaye kamar gunki,kije sashen hajiyah Maryam wai tana nemanki,inna ladiyo ce tace na faÉ—a miki"
Karisa shiryawa nayi cikin doguwar riga ta atamfa,nasaka hijabina na tafi.
Kafinnan saida nabi ta wajen inna ladiyo tukunna tana kitchen.
"Inna dama kinsan......."
"Haba Æ´ar nan,muna tare a É—aki É—aya har mu kasa gane halinda kike ciki? Abinda zan faÉ—amiki shine ki daina wannan boye boyen haka,wanda yasani yariga yasani,wanda baisani ba kuma zaki jawo hankalin sa ne yasaka ayar tambaya"
ÆŠaga mata kai kawai nayi batareda nace komai ba,kuma maganar tata haka ne.
"Kije hajiyah Maryam tana nemanki a sashenta"
"Toh"
Shine kaÉ—ai amsata kafin na wuce can din,sai a lokacin naji rashin kyautawa ta,don rabona da sashen nayi sati biyu,wasan buya nayi tayi da Æ´an gidan,saboda karsu gane inada ciki.
Magana naji sunayi tun kafin na shiga,da waye haka suke surutu.
tura ƙofar nayi na shiga,wani saurayine amma ba zai wuce shekara sha bakwai ba.
Daga yanda suke maganar zaka gano cewar É—an uwanta ne.
"Wai huzaif yayar babanka nake fah ba kakarka,tashi to ku tafi gatanan ta shigo"
Dukkansu kallona sukayi itada shi,kallo É—aya mutum zayyi masa ya gano kamar da suke da hajiya maryam,tunda tace yayar banbansa to É—an Taheer ne kenan,babban dansa.
"Okay ni barina je waje,ki sameni a mota"
Rabawa yayi zai wuce tagaba na hajiyah Maryam tayi masa magana.
"Kai banason sakarci,bata girmeka bane da bazaka gaisheta ba"
Cikin ɗaɗɗagawa irinta masu sabuwar samartaka ya gaisheni,nidai na amsa a taƙaice ya fice. Ƙarisawa nayi muka gaisa da hajiya Maryam,sunkuyar da kaina nayi,don naji kunya sosai.
"Hhhh yau kuma kunyata kikeji,kijr zai kaiki gidansu ne akwai wanda zaki haÉ—u dasu,bansan ko ki kwana ba ga wannan ki riqe,amma ki tabbatar ki dawo gobe. Kije maza Allah ya tsare,ki kula sosai dan yanzu ba kaman da ba,na fadamasa
kada yayi tuƙin ganganci"
Nidai da toh na amsa mata dakuma godiya. Saikuma kaina a É—aure shin dawa zan haÉ—u a gidan da ban taba zuwa ba..
A haka dai na bi bayan wanda taƙira da huzaif ɗin zuwa motarsa. Ina shiga ya tayar da itah ya hau hanya ko magana bayyimin ba.

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...29...
Chapter 36 · 0% Book details