← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 48

Sashe 31

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu gudu sauri sauri tayi parcking motar a ƙofar wani gida,kaman an turata ko gama saita ta batayi ba ta buɗe ƙofar ta faɗa gidan fa gudu.
Hannunta na kan bakinta,kana ganinta kasan kuka take tarewa da hannun.
Kai tsaye wani sashe ta nufah a gidan ba cikin gidan ta shiga ba.
Domin gidan kana kallonsa da alama na haya ne amma na masu aji.
Banke ƙofar tayi ta shiga farlon,ba kowa a ciki dan haka ɗaki ta shige.
Wata matashiya ce mai matsaikacin a jiki a kwance akan gado fanka na seseta tata tana bacci.
Gadon ta hau tareda É—aga mata duka a hips É—inta.
Wata zabura mai baccin tayi tareda kallon Mulaifah cikeda mamakin ganinta da tsakar rana a gidanta.
"Ke lafiya na ganki kaman an jefoki iyanzu,daga ina haka?"
Maimakon ta bata amsar maganar ta saima kuka data kece dashi da danasani da kuma takaici.
'Magana nake miki Mulaifah amma kinyi shuru vakicemin komai ba"
"Padush na shiga uku shikenan rayuwata ta ƙare nikam wayyo Allah nah"
"Wai maiya farune?"
Wata takarda da take hannunta ta jefawa padush É—in,wacce take É—auke da sunan asibiti.
Da sauri hannunta har yana rawa ta buÉ—e takardar,zaro ido tayi da alama ta karanta abinda ya saka Mulaifah kuka.
"Ciki..... Omg how,garin ya hakan ta faru mai kike tunani?"
"Nima bansani ba besty,kuma fah ina amfani da magani yanda ya kamata"
"Uhm na waye to a samarinki,nasan bazai wuce useey ba koh"
ÆŠaga kai tayi kawai ba tareda ta bata amsa ba.
"Ya sani amma?"
"Yasani dashi ma mukaje asibitin"
"To kuma miyasa kuka dawo ba'a zubarba?"
"Hmmm sunce wai zan iya rasa raina idan natakura saina zubar,saboda mahaifata batada ƙarfi,nayi amfani da magani sosai,ga kuma abortion danayi sau biyu,idan nasake wai zan iya samun bleeding mai tsanani.
Duk da hakan ya takura akan sai an zubarmin shi bai shirya karbar dan shege ba yanzu,wai sunan iyayensa zai baci,musamman da yana neman minister.
Nikuma sai naƙi a zubar ɗin,dan gaskiya ban shirya mutuwa yanzu ba.
To akan hakane mukayi fada dashi ya tafi,yace kuma idan nasake nemansa sai ya batar da rayuwata.
Padush ina cikin tsaka mai wuya,dan Allah ya kikega zanyi yanzu?"
"Uhmm badan badan ba akwai wata shawara,cikin wata nawane"
"Two month ne fah,munje yin gwaji ne na kowanne wata aka ganshi"
Wani juya ido padush tayi tareda gyara zama,
"Badama kince har yanzu baki haƙura da auren Ahmad ba?"
"Eh ban haƙura ba amma yanzu kam kinsan bazai yiyu ba ai,tun bayan da aka ce shiba ɗan abba bane zance ya watse,bama ko magana dashi ma fah yanzu wata biyu kenan,shine ai na koma wajen usseey rage zafi,kinga abinda na jawowa kaina nan"
"To mai zai hana ki maida cikin na Ahmad inyaso,i think kaman zayyi,kinga idan ya san cewa nasane to a gidan za'a saka dole sai ya aureki,shima kuma zai dunga kulawa dake tunda yana tunanin abinda ya aikata miki. Tunda kince cikin two month ne to definatly a wata bakwai nan gaba zaki haihu kenan... Sai mu kasheshi muce É—an bakwaine batareda kowa ya ganshi ba,kinga ke kuma daga kin warware sai ayi muku aure"
"Wow wannan labarin yayi daÉ—i,amma taya zai kasance,sanin kanki ne ko karen haukane ya ciji Ahmad to bazai nemi mace ta wannan hanyar ba"
"Tsiyata dake gidadanci,to dama haka kawai zamu je masa,maganin tada ƙarfaffa sha'awa zamu saka masa,wanda ko shi robot ne to bazai iya riƙe kansa ba,saikin tabbatar yasha yafara aiki tukunna saiki je sashennnasa,daga nan ki ɗau wayarsa ki ƙira numberki.
Idan komai ya wakana da safe saikiyi kukan ƙarya,kice masa ƙiranki yayi,to da kika zo bakisan mai yake faruwa ba kawai ya afka miki,gashi da ƙarfi ya farmakeki har kika kasa ƙwatar kanki......haka haka dai nasan dole zaice ki boye abin yazama sirri,daga nan sai ki nuna masa alamar kinada ciki,saiki kai maganar wajen su Abbah.
A lokacin vashida zabi daya wuce ya aureki'"
Tun kafin padush tagama bayanin Mulaifah ta rungumeta saboda tsananin murna,ganin lokaci guda tasamu mafita akan matsalarta.
Daga haka suka cigaba da tsara yanda plan É—in zai tafi musu a cikin nasara.
Basu tashi ba saida suka ƙira wani doctor saurayin padush ɗin akan a ina zasu samu maganin amma mai ƙarfi sosai.

Sumaimah (POV)

A tsawon wannan watanni biyu da faruwar zancen auren Ahmad da Mulaifah mun samu ɗan kusanci kaɗan fiyeda na da nida Ahmad. Wanda kowa idan ya kalla yasan soyayyata ce tashiga zuciyarsa,kokuma nace zuciyarsa ta ganeni,ƙwaƙwalwarsace dai har yanzu bata ganeni ba.
Ni abinma wani lokacin har dariya yake bani,idanna ga yana hade rai idan ya ganni da Saleem ,bama ya Sameer wanda shima ya dawo daga aikin daya rafi yi,shikamma har kalmar so ya furtamin, a amma lokacin nace masa yayi haƙuri ni matar auece,lokacin dana faɗamsa bai yarda ba saida na rantse masa tukunna.Tundaga lokacin muke mutunci dashi,amma shi Ahmad bai sani ba,gani yake kaman soyayya mukeyi,nikuwa ban taba faɗamasa gaskiya ba,shima ya ɗanɗana yaji yanda naji kokuma nace nake ji. Shima Sameer yanzu nice nake yimasa abinci a gidan, shikuma Saleem in yana nan a sashen Ahmad yake ci. Sameer ma abinda yasa baya zuwa don basa shiri da Ahmad ɗinne,har yanzu yana zarginsa a cewar shiya gani a wajen satar da akayi shekara biyu baya.
A bangaren hajiyah maryam kuwa yanzu har raina nake É—aukarta tamkar mahaifiya ta,yayinda itama take ji dani tamkar Æ´ar ta,amma yawanci mukanyi zancene a sashenta inna je yimata aiki,duk da ta hanani ma amma nice na nace akan zan dunga yimata.
Yanxu ma a kitchen nake na dukka gidan ina yin abincin karyawa,Ahmad bayanan yaje Kaduna jiya,da yamma zai dawo.
Dan haka shi yau bashi a abincin safen,iyah Sameer ne kawai da hajiyah maryam,wanda don ita ma na tashi dawurin saboda zata sha magani,jiya a gidan marayunta muka wuni an ƙara mata jini. Duk lokacin danaga tana wahala yanxu haushin hajiyah Mammah nakeji,don nasan itace ummul aba'isin na duk abinda yake faruwa a gidan.
Jallof É—in taliya nayi mai ruwa ruwa tasha sardine,a warmer na sakawa Sameer nasa,ita kuma a plate na zuba saina kife da wani.
Saida na kai masa nasa kan dining table kafin na wuce sashen hajiyah maryam.
Neelah bata nan tare suka tafi da Ahmad dan haka nice kaÉ—ai mai kulada itah,tunda ni kaÉ—aice nasan abin dayake faruwa.
Bata É—akin,amma akan gadon akwai alamun bata daÉ—e da tashi ba,kenan tana banÉ—aki.
Ajiye abincin nayi na yaye zanin gadon,ganin alamar jini jini daya bata gadon,wanda nake tunanin inaga daga jikin carnular ta yafito.
Bayan na cire ina shimfiÉ—a wani tashigo É—akin jikinta da ruwa,wanka kenan tayi.
Gaisheta nayi tareda yimata ya jiki,ta amsa cikeda fara'ah,ta samu ƙarfin jikinta ba kaman jiya ba.
A bakin gadon ta zauna na miƙo mata abincin,kana na buɗe drawerta na miƙomata magani.
Bayan ta gama ɗan zance mukeyi wayar ta tayi ringing,Neelah ce taƙira taji ya jikinta. Sun fara magana kenan na dauke kwanon na basu waje. Dan yanzu babu wani zance labe na rigada nasan bazata taba cutar da Ahmad ba,kuma bugu da ƙari nariga da nasan wacce take aikata komaiɗin.
Lokacin dana maida plate ɗin ummi harta fara wanke wanke,banyi koƙarin tayata ba dannasan batason hakan.
Ina ajiyewa ma naga wayata tana ƙara.
Yau wace rana nace a raina,yah Musbahu ne yake ƙirana.
Sun fito daga wajen aikin kenan,kai mashaallah dan dama ƙiranmu na ƙarshe dashi tun kafin nazo gidanann,wai an turasu wani waje aikinsu na farko,kuma wajen ba service,harsu gama ba waya.
"Yah Musbahu kaine dagske?"
Dariya yayi kafin yace .
"Nine mana mai kika gani?"
"Wata huÉ—u fah kenan kona ce biyar"
"Uhm Alhamdulillah mungama ai,jiya na dawo gida da daddare,naje gidanki akace wai bakyanan kin tafi aiki abuja.....Sumaimah meyasa,aikatau fah akace kinayi?"
Shuru nayi na kasa bashi amsa,nasan dama dole sai yaji babu daÉ—i. Hawayene naji yana shirin zubomin nayi saurin maidashi. Inata garauniya na manta ashe inada wanda suka damu dani.
"Lahh yah Musbahu karka damu ba wani aiki bane fa sosai,bawata matsala. Ina su ammi,kaje gidana kace yasu deeja da Sayyid da inna".
"Duk suna nan ƙalau,banida lokaci gobe zan koma kaduna da nazo na ganki,amma karki damu bayan mungama da kaduna abuja za'a turamu headquarter indai an tabbatar da ƙwazonka,Inshaallah idan na dawo abuja zaki bar wani aikin aikatau"
"Tom Sheeshah Allah ya kaimu yah Musbahu nagode"
"Ameen ya Allah"
Cikin sanyin jiki na sauƙe wayar,zai dawo abuja? Kuma zai hanani aiki,idan bangama abinda zanyi a gidan kafin sannan fah,hajiyah maryam bazata iyah cigaba da yi ita kaɗai ba,don wannan jinyar da take ma ƙoƙarin taimakon Ahmad tayi ta hanyar bashi wasu bayanai akan mahaifinsa. Saboda har yafara zargin kansa a matsayin ɗan wacce ta kashe masa mahaifi. Wannan abin na kana ganin gaskiya kayi shuru yafi komai sosawa hajiyah Maryam zuciya. Dan a ranar da hajiyah Mammah ta zauna tamkar matar arziƙi tana zayyano masa labarin ƙaryar hajiyah Maryam kuka tayi ta rabza a ɗaki,musamman da taga halin da Ahmad ɗin ya shiga,da saida yayi yunƙurin nemo dangin Amina,injishi dangin mahaifiyarsa. Da ƙyara aka shawo kansa ya haƙura,shiMa bawai dukka ba,yabarine saboda case ɗin dayake handling.
"Ohh ya zanyi idan yah Musbahu yazo gidannan,komai fah zai iya wargajewa kenan."
Sashenmu na nufah domin na kwanta,dan yau bazanje sashen Ahmad É—in bama sai yamma idan yakusa dawowa.

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2*
...24...

Hankalinta kwance ta haɗa komai a hankali,don tasan tunda yace bada wuri ba,wataƙila ma sai wajen magriba su ganshi.
Bayan ta gama komai jawowa sashen tayi amma bata kulle ba,tunda tasan babu mai shiga idan ba itaba kokuma wani inya gayyaceshi.
Tafiya take tana ƴar waƙa,tamkar babu abinda ya dameta,tana shiga sashensu banɗaki ta faɗa domin ta ɗauraye jikinta,don tun ranar farkon da Ahmad ya kamata tayi wanka a banɗakinsa bata sakeyi ba,tanaso ya yarda da itah,idan zatayi nasara to sai ta haɗa da kiyaye irin waɗannan abubuwan.
Chapter 31 · 0% Book details