← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 48

Sashe 24

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Fatee ina zakije"
Hajiyah maryam ta faÉ—a a dake lokacin dataga Fatee ta dosota da alama fita zatayi.
Da mamaki tayi turuss tana kalon mahaifiyar tasu sai kuma ta cuno baki.
"Mommy dama bakya gida,nifa banyi zaton yauma a,wajen aiki kika kwana ba?"
Da Mamaki na kalli fateen,tayini a haife amma wai har yanzu a ƙaramin hankalin ta uwarta takwana tanashan jini batada lafiya,amma wai bata sani ba? Hmmm dole mutane su dunga cewa rayuwar masu kuɗi akwai wuyar sha'ani,koda yake itama hajiyah maryam ɗin na kula tana son ƴaƴan ta dayawa,amma kuma koda wasa bata nuna hakan a gaban idonsu,komai yasa oho.
"Ba wannan na tambayeki ba,wannan wacce irin shigace kike shirin fita da itah?"
Ta faɗa tana nuna riga da wandon jikinta,wanda rigar ƙaramace bata rufe wandon sosai ba,sai kuma gyale shima iya wuya. Yanayin shigar yayi kyau sosai,amma fita dashi a matsayinta na ƴar musulmai kuma hausawa bayyi tsari ba.
"Uhm uhm mommy mota fah zan shiga,ba a ƙafa zan tafi ba,kuma ma........"
"Jeki cire wannan kayan ki saka wasu"
"Amma mommy......"
Tafaɗa kaman zatayi kuka harda buga ƙafah.
"Nace jeki ciresu koh!!!"
Wannan karon da ƙarfi tayi maganar,kana gani kasan dukkan ƙarfinta na lokacin ta tattaro tayi amfani dashi.
Cikin fushi kaman zatayi kuka tabar wajen da gudu.
Tana tafiya hajiyah maryam ta tsugunna a wajen tana kama ƙirji.
Saurin matsawa nayi kusada itah na tallafi hannunta na dama,É—ago idonta tayi a hankali tareda zubasu a cikin nawa.
"Taimakamin na shiga É—akina kafin wani yazo ya sameni a haka,musamman su fatee"
"Kina fama da ciwo amma meyasa bazaki bari iyalanki su sani ba"
Cikin rashin fahimtarta tayi mata wannan tambayar,shin abin kunya ne mutum yayi jinya,da bazata iyah bayyanawa ba.
Dariyar ƙarfin hali tayimin kafin ta jijjiga kai.
"Hmmm bazaki ganeba Sumaimah,muje"
Daga nan hanyar ɗakinnata muka nufah,a bakin gado ta zauna,har Sannan haki takeyi jikinta babu ƙarfi.
"Kona kawomiki abinci kai?"
"Abinci kuma,masu girki sun farane da sassafennan?"
"Uhm akwai wanda nayiwa Ahmad a sashensa,to ko ruwan tea ma"
Na faÉ—a inason kawar da zancen farkon.
Ƴar dariya tayi tana kallon yanda nayi diri diri.
"Menene na sauya zance Sumaimah,nasan zaki fara yimasa girki ai,hakan yanada kyau sosai,domin bai warke ba amma kullum yana cikin saka rayuwarsa cikin hatsari.....hmm marayan Allah. Nagode Allah da kikaso rayuwarsa"
Kallonta nake ganin yanda take maganar cikin damuwa kuma daga ƙasan zuciyarta,shin yaushe zan gane wannan matar ne.
"Ke ba kishiyar mahaifiyar Ahmad bace,kinayin kaman keÉ—in uwace data nisanta kanta da É—anta,kuma take cutuwa dayin hakan"
Saurin zabura tayi ta kalleni,da alama maganganun da take É—azun tana zaton a zuciyarta take furtasu.
"Taya kika san hakan?"
Bayan ta faɗi hakan sake ganowa tayi tasake kwafsawa a karo na biyu,diriricewa tayi da alama tayi matuƙar razana ganin yanda sirrin dayake ƙarƙashin zuciyarta ya fito fili.
"Sumaimah zaki iya tafiya inason na jini ni kaÉ—ai"
"Toh"
Shine abinda nafaÉ—a nayi hanyar fita daga É—akin. Naji maganar ta.
"Duk da cewar abinda kika gano ɗin gaskiya ne amma ba yanda kike tunani ba.....Sumaimah har yanzu baki yarda dani ba,kuma baki shiga har yanzu matakin danake so kikai ba kafin ki san mai yake faruwa,duk ƙoƙarina na nabarki cikin duhu batareda kinsan komai ba kaman sauran mutanen gidan,amma abu yaci tura,kina cigaba da gano abinda zai iya vaki wahala. Wannan wacce irin ƙaddara ce.......koma dai menene kada kowa yaji abinda muka tattauna dake a yanzu,ki barshi a ranki kada ki fitar"
Daga haka ta kishingiÉ—a a kan gadonta,da alama ta gama maganar tata.
Jan ajiyayyen numfashi nayi tareda fitowa daga É—akin na rufe.
Kitchen na nufah na É—ora ruwan zafi,da farko tayi kamar zataci wani abun,maganar da mukayine tasakata sauya shawara,dan haka nasan a wahale take.
Idan ma abinda nagano gameda itane yasakata yin hakan da ta daina,menene abin wahalar rashin ganewar,tunda muka haɗu abinda take nunawa tayi kamada wacce take hora kanta wajen yin abinda bashine a cikin zuciyarta ba,gabaɗaya rayuwarta a wasan kwaikwayo takeyinta,ciki kuwa harda ƴaƴan ta. A fili ta nuna musu halin ko inkula,a baɗini kuma sune a ranta har lokacin da numfashinta zai fice,Musamman ma Ahmad,duk wata damuwar sa da komai nasa tasani,sannan koyaushe cikin kareshi take kota saka a kareshi daga wani abun,sannan duk sanda aka kawo zancensa inaganin nadama da rauni a idonta sosai. Wannan za'a ƙira da tsana,soyayyarsa ce a idonta irin na mahaifiya.
To amma ya haka? Mai yake faruwa a wannan kurman gidanne,idan har ba itace take cutar dashi ba to wanene,duk da itama ban yarda da itah har yanzu ba,amma kuma zuciyata tana bani,akwai wani wanda yafita dayake aikata waÉ—annan ayyukan,kuma yake tilastata akan horon da take bawa jininta bada son ranta ba.
Amma koma waye mai yasa batayi maganinsa ba,kuma ta miƙashi an hukuntashi,ina matsayinta na wayayyiyar mace kuma mai sani akan shari'ah.

Sashen hajiyah Mammah nayi bayan na kaiwa hajiyah maryam abincin danayiwa Ahmad,bataci sandwich É—in bama,iya kunun gyaÉ—ar kawai tasha.
A hanya naci karo da wani soja a ƙofar sashen,yana ɗaya daga cikin masu kulada security na gidan.
"Am gud morning,please can you send this to hajiyah Mulaifah?"
Yafaɗa yana miƙomin wani akwati irinna package ɗinnan.
Karba nayi kafin nace wani abun har yabar wajen. Banso ba haka na nufi É—akinnata,Allah yagani banason duk wani abu dazai dunga haÉ—ani da waccer matar.
Tura ƙofar ɗakinnta nayi bayan na shikenan sashen hajiyah Mammah,ko ƙwanƙwasawa banyi ba.
A buÉ—e kuwa yake bata rufe ba.
Wata irin kwanciya tayi akan gadon kaman wata Æ´ar bori,hararta nayi tareda ajiye abin akan drawerta,har na juya zan tafi naji maganar ta cikin magagin bacci.
"Ke rainin naki har yakai kishigomin É—aki kai tsaye kaman wadda muke sharing dake?"
Tsayawa nayi amma ban juyo ba,wai dama idonta biyu?
"Ga waÉ—annan kayan naÉ—eminsu kafin ki tafi"
Cije bakina nayi,amma ya zanyi,banason yazamo koyaushe muna samun sabani da itah.
Juyawa nayi wajenda take maganar,a hankali nake takawa har naje gaban wardrop ɗin,ina buɗewa kaya suka wani sako kai zuwa ƙasa. Saida na tsorita domin banyi zato ba. Zaro ido nayi ganin kusan duk ilahirin kayanta a cunkushe suke babu tsari.
Wai a hakan zata ƙira kanta mace,kuma maison mallakar wani namijin.
Fitowa nayi da kayan cikin tass nafara jerawa da É—aÉ—É—aya.
Wayar tace tayi ƙara,saida tayi ƴar ƙaramar tsuka kafin ta miƙa hannu ta ɗauka.
"Hii padush ykk"
"Ƙalau ke ya akayi jiyanne,abin yayi aiki"
"Hmmm ai nake faɗamiki fiyeda yanda kike zato ma,yace haka ne kam tunda abune da aka farashi,kuma yayi alƙwarin haɗashi yanzun bazai gagara ba. Yau ma zayyi magana da Ahmad akan zancen,zuwa gobe kowa zai shaida shirye shiryen aurena da Ahmad"
"Amma bakya ganin shi Ahmad ɗin ya ƙi amincewa"
"Nima nayi wannan tunanin amma hakan bazayyiyu ba,domin Abbah bazai taba daina yimasa zancen ba idan har ba auren aka yiba,shikuma kinsan wancan karon ma,baya iya tsallake maganar abban. Dan haka kisha kuruminki ki saurari mai zai faru"
Dariya suke sunata maganganunsu wanda sukayi amanna dasu kuma suke yi musu daÉ—i..
A yayinda gefe ɗaya kuma ni suke ƙonamin rai fiyeda yanda mai tunani zai tuna,wai dama matar nan da gaske take,mijina take son mallaka hakan ma kuma ta hanyar mallakar magani,bawai da son ransa ba?.
Rigar da take hannuna na jefar na tashi na tafi,kunnuwana bazasu iyah jin waÉ—annan maganganun ba,in kuma nace zan cigaba da saurarensu to za'a samu cikyakykyen mishkila.
Ina jinta tanamin magana amma nayi banza da itah nabar sashen.
Kai tsaye sashen hajiya Maryam nayi,saidai tun kafin na shiga nake jiyo maganar ta,da kuma muryar babban mutum,nasan babu makawa babansu Fatee ne.
"Wai bakida lafiyane naga duk kin sauya,kin rame ba kaman da ba"
"Ohh dama ka damu da hakan,sai yanzu kasani? KafaÉ—amin menene yake tafe dakai da har kazo sashena i yanxu?"
Shuru naji ya gibta,har zan juya na tafi saboda bai dace na zama kullum mai jin abinda wasu zasuce ba,hakanma kuma sabgar ma'aurata wanda bai shafeni ba.
Turus nayi tareda komawa baya,abinda naji ya faÉ—a ya shafeni.
"Akan maganar auren Mulaifah da Ahmad ne,tazo tasameni akan maganar jiya da daddare...kinsan kuma daman abune da har an farashi wancan tsautsayin ya gibta. To yanzu tunda komai yalafa yakamata a yi auren.
Yanzunnan daga office nake,nazo É—aukar abune nace barina yi miki maganar,shima Ahmad munyi magana dashi É—azu kuma ya nunamin amincewar sa."
"To mai yasa kake faÉ—amin,a matsayina nawa a wajensa"
"Maryam mai yasa kike hakane,wainikam yaronnan mai ya taremiki ne,da kullum kike nuna haka?"
"Abban Fatee mai nayi kuma,shin nasake ƙoƙarin kashe maka ɗa ne yanzun,da kake min wannan zancen. Naji abinda kace,Allah ya taimaka ya kaimu ranar auren,yaushe ka saka?"
"Wani satinne idan komai ya daidaita,yakamata yayi aure zuwa yanzu,kuma babu amfanin sake wani shirye shiryen bayan wanda akayi a baya"
"Uhm"
Shine kawai abinda na iya faÉ—a kafin nabar wajen,nikam mai yasa kullum kunnuwana sai sun jiyomin zancen wasu ne wanda zai tabamin zuciya?.
Dafa bango nake jikina yana rawa na bar wajen. Itama ta yarda da auren,shima uban gayyar ya yarda da auren,shikenan daga ƙarshe sun zabi jininsu zasu haɗashi da ita,dama nasan yafi ƙarfina tun ranar danagano wanene shi,kawai son zuciyane da yarda da abinda bazai yiyu ba yasa nake ganin watarana zai waiwayeni.
Kukane ya kufcemin mai matuƙar ƙarfi a corridon da zai fitar dani zuwa sashenmu.
Kasawa nayi,na kasa ƙarisawa na gaza,komai yayimin duhu. Nakasa dawowa dashi a cikin rayuwata,shin dama bana cikin ransa tunda ko kaɗan,da gushewar tunani kaɗai zai shafeni tass daga cikin kansa?. Dan ban faɗamasa ni wacece ba shikenan koda da sau ɗaya bazai iya cankar wacece ni ba? Idan ta ɗaukeshi wane uba zan bawa ɗana kenan,shikenan yanada uba amma kuma tamkar bashida shi_? SANADIN CACA ne yahaɗani dashi, na tsorata dashi,na ƙyamaceshi amma kuma na daure na amince dashi,na yarda dashi na taimakeshi na kuma bashi kaina da amanata,batareda na duba mai yayimin a baya ba kokuma waye shiba a baya. Amma shi mai yasa yanzu yakasa gani na,ya kasa tuno ni,yakasa karbata a rayuwarsa. Shin mai zanyi nan gaba wanda zai dawo dashi cikin rayuwata?.
Chapter 24 · 0% Book details