← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 48

Sashe 22

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tun zuwanta tab da bakin ƙofar kafin ta tura take jin nishin hajiyah maryam a cikin ɗakin.
Cire komai dayake ranta tayi ta afka cikin É—akin,ma'aikaciyar jinya ce sanye da kayan likitoci,sai É—ayar kuma kayane haka a jikinta,sai kuma Neelah da take tsaye a wajen kan hajiyah Maryam,wacce take kwance tana lumshe ido sama sama.
Sumaimah tana shiga da Neelah suka haÉ—a,wacce kallo É—aya tayi mata ta É—auke kanta,domin hankalin ta yana kan hajiyah Maryam.
Kaman munafuka take takawa har taxo daidai tsakiyar ɗakin,daidai lokacin da hajiyah Maryam tayi wata ƙara mai cikeda firgici,fizge fizge tafarayi tana ƙoƙarin yage ƙarin jinin dayake shiga jikinta,yayinda suma suka ƙara ƙaimi wajen rirriqeta.
"Innalillahi kuyi wani abun zasu cire min zuciya,wannan karon kam da ita zasu tafi,kucewa Æ´aÆ´ana su yafemin wayyo Allah nah"
Mai sanye da kayan likitanne ta kalli Sumaimah da take tsaye, tayi suman tsaye.
"Baiwar Allah miƙomin allurar can nayi mata,da alama zafin ciwone yasakata....Neelah ki riƙeta sosai fah,karki bari ta cire igiyar"
"Ai ba igiya take ja bama,anty indo,da alama ƙirjinta takeson tabawa"
Neelah ta faɗa cikin tausayawa kaman zatayi kuka,daidai kuma lokacin da Sumaimah ta miƙawa matar allurar.
Ƙarba tayi da sauri ta zuba a jikin carnular,kafin tacigaba da shafa kanta.
Sun daÉ—e a hakan kafin ta daina jijjigar,jikinta ya shika baccin wahala ya É—auketa.
Saketa sukayi sauran matan biyun suka bar É—akin,yayinda itakuma Neelah har yanzu batayi motsiba tana nan a zaune gefen hajiyah maryam É—in.
"Mai yake damunta haka?"
Sumaimah ce tayi maganar cikin kiÉ—ima da kuma É—aure kai,don abin duk wanda ya gani kam sai ya tausaya mata.
"Uhmm nima bansan sunan cutar ba ballantana nayimiki bayani akanta,yanda kika gani a yanzu haka nake gani nima tun tashi na. Nida hajiyah Maryam mun daÉ—e da sanin kina bibiyarmu da abinda muke,kece mutum ta farko data san abubuwan da su kansu Æ´aÆ´an ta basu san dashi ba. Kaman yanda muma munsanki mun san wacece ke fiyeda yanda Æ´an gidan suka sani"
Zaro ido Sumaimah tayi tareda kafe Neelah da kallo.
"Kina nufin......."
"Ehh nasan ke wacece,daga garinda kike,da É—anki wanda yake É—a a wajen Ahmad duk munsan komai,saidai shi mijinnaki bai san da hakan ba,wanda kuma hakan shine ya fi a wannan lokacin"
"Kece kika turomin wannan saƙon kenan,na karna faɗawa Ahmad wacece ni?"
"Uhm nice,amma hajiyah Maryam ce tace na turamiki,abinda kikeyi na bincike nasan kinayi ne domin kare wanda kikeso,amma ki sani zai kasance É—ayan biyune,ko kiyi nasarar kare wanda kike so,kokuma ki akasin haka,wanda sakamakonsa shine zaki cutar da masoyanki fiyeda yanda kike zato,zabi ya rage gareki wanne zaki zaba"
Dumm Sumaimah ta tsaya tana kallon Neelah,yayinda kunnunwanta suka buɗe suna jin abinda take faɗamata,kenan duk tsawon wannan lokacin sunsan wacece itah,da kuma abinda takeyi to amma meyasa basu koreta kokuma su cutar da ita ba,indai har da gaske hajiyah Maryam tana ƙin Ahmad to meyasa tasan tasirinta a rayiwarsa amma ta ƙyaleta,maimakon haka saima cewa da tayi karta bayyana ko ita wacece. Kai dole akwai wani abu ƙulalle dayake kai kawo a cikin wannan lamarin.
BuÉ—e bakinta tayi,wanda yayi mata nauyi kaman an É—aura mata dutse a kansa.
"Kun san wacece ni,kuma kunsan na ganku a abubuwa da dama,to amma meyasa kuka rabu dani,yanzu ma kunsan ina biye daku amma maimakon ku gujemin saima biyamin taxi da kikayi,kikace a shigo dani a har É—akinnan,menene dalilin hakan?"
Ɗan murmushi Neelah tayi na ƙarfin hali kafin tace.
"Sumaimah karki kuskura ki shaidi littafi daga bangonsa,ki bari saikin buɗe cikin kinga mai ya ƙunsa tukunna,idan kuma ki ƙi,a sanadiyyar hakan zakiyi nadama da tafi cikin kwando"
Kafin Sumaimah ta buÉ—e baki tace wani abu sukaji tarin hajiyah Maryam.
Dukkansu a tareda suka waiga inda take. Itama kallonsu take tareda ƙoƙarin tashi ta zauna.
"Sumaimah ke kuma menene dalilinki na bin mutum waje kawai dan kinga ya fita cikin dare,idan wajen halakane kenan haka zaki kai kanki ki cutu,miye amfanin hakan kenan?"
Duk da muryarta tana ɗan rawa saboda rashin ƙarfin jiki,amma cikin dakewa take yiwa Sumaimah magana.
"Kiyi haƙuri"
Shine abinda ta faÉ—a tana sunkuyar dakai.
"Uhm shikenan ya wuce,amma abinda Neelah ta faɗamiki gaskiya ne,kidaina jefa kanki cikin abu kai tsaye ba tareda ƙwaƙwƙwaran shiri ba,kada ki manta keɗin uwace sannan kuma kinda waɗanda suka damu dake. Neelah tashi ma mutafi gida dare Yayi sosai"
Tun kafin Neelah tace wani abun ta tashi daga kan gadom zata saƙƙo,tana miƙewa hajijiya tace jira nake,tayi taga taga kaman zata faɗi ƙasa,a tare Neelah da Sumaimah suka riƙeta.
"Mommy baki samu ƙarfin jiki ba har yanzu,bazayyiwu mu tafi gida ba,za'a iya zargin wani abun,ki baridai ko zuwa safiya"
Zaunarta sukayi a bakin gadon tana haki tareda riƙe ƙirjinta.
"To shikenan naji,amma ki maida Sumaimah gida kada a ga batanan,ke ma kuma kije ki huta,indo zata kulada ni"
"Ahah babu wanda zai nemeni,dama ni Æ´ar aiki ce,kawai zance na rakaki wani wajene zan riqemiki wani abun"
"Ni a wajena keba Æ´ar aiki bace,hasalima baki taba zama Æ´ar aikin a wajena ba,ko ita wacce ta turoki tasan bazan taba ganinki a mai aikiba,kuma tasan zan kulada ke shiyasa bata damu ba ta turoki gidannan,amma duk da haka akwai abinda bazan iya ba,dan haka kibi Neelah ta maidaki gida,sannan koba niba kada ki sake ganin anfita yin wani abun kisaka kanki a ciki batareda zurfin tunani ba"
Cikin faÉ—a take maganar,da alama tsoro da kuma fargaba sun kamata a lokaci guda,wanda hakan yasa suka haifar mata da yin faÉ—an da bata shirya ba.
Komawa tayi ta kwanta,alamar ta gama bayani kenan bazata sake jin abinda suke faÉ—aba.
Fitowa sukayi daga É—akin,har suka shiga mota suka kamo hanya babu wanda yace kowa komai.
A bakin ƙofar gidan Neelah tayi burgi bata shiga ba,kallon Sumaimah tayi alamar ta fita. Hakan yasa ta tura ƙofar motar zata fita.
"Nasan kinason kisan gaskiyar mai yake faruwa,amma sanin hakan bazai miki komai ba sai sakaki a hatsari,amma in kinga zaki iya ji to ki tambayi hajiyah maryam da kanki,zata sanar dake komai"
ÆŠaga kai kawai Sumaimah tayi,zata sake fita a motar.
"Kin yarda da itah?"
"Ahah koda na faɗa a cikin raina to hakan bazai zama gaskiya a raina ba,saidai kuma zarginta da nake na yanke kusan rabi a cikinsa. Ni zan shiga ciki nagode ki gaisheta Allah ya sawwaƙe"

Sumaimah (POV)
Chapter 22 · 0% Book details