← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 48

Sashe 33

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaji dai kaman ya tasa kai da wani abu mai tudu,amma bayyi masa kamada pillow ba,buɗe idonsa yake a hankali saboda nauyin da yayi masa kafin ya sauƙe akan cikin Sumaimah.
Ɗaga kansa yayi sai a sannan yaga ashe kan ƙirjinta yasaka kansa,mai ya kawota ɗakinsa kuma kan gadonsa,sannan ba sutura a jikinsu.
Abinda yafaru jiyane Yafara kwaranyowa cikin ƙwaƙwalwarsa.
Saurin zabura yayi ya tashi zaune tareda ƙarewa yanayinnasu kallo,jini ya gani a bargon da wajen ƙasanta,wanda yasan ba shakka daga cikinta yake fitowa,saboda tsabar ƙarfin dayayi mata a jiyan..
Hannunsa dukka biyun wanda suke rawa yasaka a kansa ya dafe,domin ji yake kaman zai cire saboda tension É—in dayake ciki,wani ihu ya fashe dashi na dana sani da kuma nadama.
Hakanne ya farkar da Sumaimah daga baccin da tayi a jiyan,wanda za'a iya ƙiranshi da ƙanin suma.
Iduwanta fulu fulu sukayi,badan fatar bakinta ta ƙasa inda ta cijeta tayi jawur.
Yunƙurawa tayi a hankali ta tashi zaune tana cicccize baki saboda tsamin da jikinta yake yimata.
Kallo tabi Ahmad dashi,wanda shiÉ—inma ita yake kallo tamkar gunki.
Zanin dayake gefenta ta jawo ta saka akan ƙirjinta,kana ta kama gashinta daya bake akan fuskarta ta ɗaure.
"Meyasa......meyasa......meyasa kika aikata haka,kinsan kuwa girma da kuma munin abinda kika sanya na........."
"Kana lafiyah,maganin yabar jikinka bazai cutar dakai ba?"
Shine abinda Sumaimah ta faÉ—a cikin dashashiyar murya.
"Naji Mulaifah tana cewa zai jawo maka babbar matsala idan ta zauna dashi a haka"
"Shine dalilin daya saka kika bada kanki,abinda yafi komai muhimmanci a wajenki,sannan kika saka na aikata abinda harna mutu bazan manta ba? Meyasa zakiyimin haka,bayan nace miki ki tafi mai ya dawo dake toh? Akan matsalata ki kalli abinda na aikata miki,yanzu ya zanyi kenan"
Maganar cikin nadama yake ambatarta kamar zayyi kuka.
Ɗan murmushin ƙarfin hali Sumaimah tayi kafin tace.
"Karka damu nidama ba budurwa bace bare kace na rasa budurcina,Sannan nayi niyyar tafiya kaman yanda kace,......."
"Wannan shine abinda yakamata muyi magana akai a yanzu?"
Daga haka ya tashi ya shiga banÉ—aki.
Binsa Sumaimah tabi da kallo tareda runtse ido. Shin wai yaushe zatayi tarayya da mijinta cikin salama ne,dan wannan ko kusa bazata ƙirata da kwanciya ba sam.
Ƙoƙarin tashi take amma abu ya gagara,ko ranar farkonta bataji wannan azabar ba,gaskiya bazata taba yafewa Mulaifah ba.
Jingina tayi da kunnen gadon,ganin duk yanda tayi bazata iya tashi daga kan gadon ba.
Jin motsin takunsa ne yasakata buɗe idanuwanta,jallabiya ce a jikinsa ruwan toka,sai ruwa daya ke fitowa daga sumar kansa,alamar ya tsabtace jikinsa. Daren farkonsu ne ya faɗo mata a ranta,yanda tayi fama dashi kafin ya tashi yayi wanka. Duk da halin datake ciki hakan bai hanata yin murmushi ba,idan tace batayi kewar goje bama tayi ƙarya.
CiÉ—ak taji ya cirata sama tareda yin hanyar banÉ—aki,da kallon mamaki tabishi kana dabi jikinta ma da kallon,zanin ya cire cinyoyinta duk bushashshen jini. Runtse idonta tayi wannan kunya har ina.
Da sauri ta buɗesu jinta a cikin ruwan zafi,saida tasaki ƙara jin yanda ya shigeta.
"Ki zauna a ciki zafinsa inya ratsaki zakiji ƙarfin jikinki ki iya gyara kanki. "
Daga haka yabar banÉ—akin,ajiyar zuciya ta saki tareda sake jikinta a cikin bahon wankan,tasan yanzu yafijin haushinta ma fiyeda wacce tayi silar shigarsa cikin wannan yanayin.
Ta daÉ—e a ruwan,bayan yayi sanyi ma tasake saka wani ruwan zafin.
Saida taji jikinta ya É—an dawo daidai kafin tayi wankan tsarki ta fito.
Towel É—insa ta É—auka tayi amfani dashi,lokacin data fito baby duvet É—in ya cireshi,ko ina ya kaishi oho.
Hijabinta ta É—auka tayi sallahr asuba,dan rana harta fara fitowa a lokacin.
Addu'o'i ta dungayi daga zaunen,ta daÉ—e kafin ta tashi ta naÉ—e sallayar.
Falon ta fito domin hada abinda zataci.
Idonta ne yakai kan dinning inada aka ajiye leda,tasan Ahmad ne ya ajiye,tunda jiya babu ita a wajen.
Sannan abincin datayi masa jiyan shima yana wajen.
Ƙarisawa tayi wajen ta buɗe ledar,magani ne na relief pain a ciki.
Tea ta haÉ—a tasha kana ta sha maganin. Daga nan ta tafi sashensu,dan ma Allah ya taimaketa safiya ce ba mutane sosai,su inna ladiyo kuwa batada matsala dasu ,dan yi zatayi kaman ta dawo daga sashen hajiya maryam,tunda ko badan haka ba wani lokacin takan kwana a wajenta.
Bayan ta kwanta akan katifar tata abubuwa ne da dama suka fara yawo a cikin kanta,shin da wannne ido kenan yanzu Ahmad zai dunga kallonta.....runtse ido tayi ko bacci zai É—auketa.

A bangaren hajiyah maryam da taga rana tayi sosai Sumaimah bata zo ba sai hakan ya tabbatar mata da zancen da Neelah ta ƙira ta faɗamata.
Safa da marwa take a É—akinnata tarasa abinyi,so take taje taga mai yake faruwa,dan indai yana cikin magani zai iya yi mata illah sosai.
"Kai wannan mutane wannan mutane,wato so take ta laƙaba masa cikin shegen da tayi?. Allah sarki koyah Sumaimah take,nasan tunda banganta ba yanzu to tasha wahala a wajensa"
Waya ta ɗauka taƙira Sumaimah ɗin,saida tayi ƙira kusan sau uku kafin ta daga cikin magagin bacci.
"Hello Sumaimah kina jina,kina ina ne,sashensa ko kuma naku?"
"Uhmm ina É—akinmu"
"Dan Allah ko zaki daurewa kizo,idan nace zanzo wajenki hakan zai zama abin magana,ya jikinnaki?"
Saida tayi jimma kafin ta amsa,wanda hajiyah maryam É—in rasan kunya taji da kuma mamakin ya akayi ta sani,amma wannan bashine a gabanta ba dan haka ta basar.
"Ehh.....zan iya zuwa,bacci ne ma ya É—aukeni"
Bayan ta kashe wayar bayan gida ta shiga,da alama wasu dabaru zata haÉ—awa Sumaiman saboda jikinta.
Lokacin datazo ta ƙyar ta haɗa ido da hajiyah maryam,ita a dole kunyar ta takeji,ita dai bata ce mata komai ba,har ta gama wankan ta fito.
Wunin ranar Sumaimah a sashen hajiyah maryam ta wuni,duk wani abu ita tayimata,tun tana noƙewa har ta saki jikinta,musamman dataga hajiyah maryam din batayi mata labarin abinda ya farun ba.
A bangaren Sumaimah kuwa da tunanin Ahmad ta wuni,shin yana ina,ko ya zasu cigaba oho,shin zai sake yarda ta shiga sashensa ma kuwa? Tasan yanacan yana É—orawa kansa laifin abinda ya aikata mata.

Washagari jikin Sumaimah ya ware,dan harta koma ayyukanta na yau da kullum,sannan kaf gidan babu wanda yasan mai ya faru sai hajiyah Maryam da kuma uban gayyar..
Bayan ta tashi saida ta gama da sashen hajiyah Maryam kafin ta wuce sashensa,har dare dai yayi bata ganshi ba,shin ya dawo ma oho.
Ba kaman ko yaushe ba yauÉ—in da É—ar É—ar na zuciya ta buÉ—e sashen,yana nan kaman yanda ta fita ta barshi jiya.
Abinda ya farune ya dawo mata cikin kai,amma tayi saurin maidashi ta É—auko mopa.
Tana cikin goge goge Ahmad ya fito daga É—akinsa,yana sanye da dogon wando da kuma vest,turus yayi dan bayyi zaton zata dawo aiiki ba,haka itama batasan yana nan ba.
Bakinta yana rawa haka cikin dauriya ta gaisheshi,jin bai amsa ba ya tsaya ƙyam kaman gunki yasakata ɗago idonta,haɗa ido sukayi dama ashe ita yake kallo.
"Mai ya dawo dake sashennan,yanzu duk abinda yafaru dake baki É—aukeshi a ishara ba kika sake dawowa inda nake,mai yasa bazaki tsaneni ba kuma ki zageni akan abinda nayi miki,saima dawowa dakikayi cigaba dayimin aiki....mai kike nema haka a wajena?,bakya tsoron abinda ya faru ya sake faruwa?"
Ƙaremasa kallo tayi jin yadda yake sambatu cikin karayar zuciya.
Idanuwansa sun faɗa gefen idonsa yayi baƙi,ga bakinsa ya bushe yayi fayau yini ɗaya kaman majinyaci,ko ita batayi haka ba bare shi.
Ajiye mopar hannunta tayi ta matso kusada shi tana cigaba da kallonsa.
"Karka cemin blaming kanka ka dungayi tsawon wannan lokacin,bakaci abinci ba kuma bakayi bacci ba......shin sau nawa zan ce maka ba laifinka bane,Mulaifah ce ta zuba maka magani saboda ta cimma wani ƙudirinta akan ka,bai kamata ka.........."
"Idan ita tayimin haka tsakanina da ita ne,kikuma da kika shiga tsakani miye ma'anar hakan kenan"
"Ohhh kafi son na barta ku aikata sabo da ita kenan,alhali inada damar magance hakan,Sannan kuma ta laƙaba maka ɗan da ba naka ba,ko kuma na barka hakan ya cutar dakai?"
"Kema da kika tunkareni muka aikata hakan miye maravarsa da natan kenan,Sannan nifah nace miki ki tafi amma kika dawo"
"Duk naji sannan na yarda ka saka laifin dukka akaina,amma ka daina yiwa kanka wannan hukuncin. Nina É—auka laifina ne,amma kai ba naka bane tunda baka cikin hankalin ka. Zancennan ya wuce sannan ya tsaya iya nan,zan É—au komai akaina"
Taƙarisa maganar tana nuna kanta,hawayen dayake idonta ta share tana binsa da kallon tausayin halin da suka tsinci kansu,da kuma tsantsar kulawa.
Shi har yarasama mai zaice da itah,saidai bi da ido.
Haka yana nan a falon ta gama gyara ko ina ta gama abinci ta kawo masa.
Duk abinda take tanajin idonsa a kanta,komai yake saƙawa a ransa oho.
Bayan ta kawo masa abincin har sannann bai dawo hayyacinsa ba,shurunne yayi yawa hakan yasa Sumaimah yin tafi a daidai fuskarsa,ganin taje ta dawo amma har yanzu bai motsaba.
"Mai yafaru haka?"
"Sumaimah ina son na aureki idan zaki yarda"
Maganar ta daketa sosai,sannan ta bata mamaki a lokaci guda.
"Aure kuma? Shin saboda abinda ya faru a tsakaninmu ne yasa kake wannan tunanin?"
"Eh dashi É—in ma,amma kuma daman ina son hakan a raina"
"Kayi haƙuri bazai yiyu ka aureni ba a yanzu"
"Meyasa nasan abinda kikemin soyyaya za'a ƙirashi, wanda saboda hakanne nima na fara sonki a cikin raina"
"Ba iya soyayyar bace kaÉ—ai zata wanzar da aure,saida sharaÉ—i tukunna,sannan cewa nace maka bazayyi yuba,ba wai bazan amince ba."
"Meyasa bazai yiyu ba toh,nariga na keta miki mutuncinki,zuciyata bazata juri ganin abinda namiki ya tafi haka ba,dan haka ki amincemin aurenki ta hakanne zanji na rage wani abun"
"Kona amince maka baya halatta nayi aure guda biyu"
"Aure biyu,mai kike nufi da hakan?"
"Inada aure,harda yaro a garinmu"
"Whattttttt!!!!!!!!!!!!"
Shine abinda Ahmad ya faɗa tareda miƙewa kaman an tsikareshi.....
"Am dama........"
Tun kafin Sumaimah tace wani abun ya toshe kunnensa.
"Shut up,don't say anything,banason jin komai daga bakinki,sannan kuma ki fita daga sashennan,banason ko ido nasake haÉ—awa dake daga yau"
Taƙarfi ya faɗi hakan har saida ta razana,tashi tayi da sauri ta bar sashen tana hawaye,shikenan komai data dade tana yi ya wargaje a yau ɗin.

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem
Chapter 33 · 0% Book details