← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 48

Sashe 5

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A ranar aka sallamemu muka tafi gida,kasancewar na farfaÉ—o kuma babu wata matsala.
Tunda mukaje asibitin ammi ce kawai taje,shima ina kwance bansan taje ba.
Ranar daza'ayi dakan yaji dama ban saka a raina za'ayimin komai daga gidan mu ba. Inna ce ta yankamin kaji guda biyu wanda take kiwo a can ƙyauyensu.
Abin suna kuwa dama tun cikina yana ƙarami ta siya ta ajiye a garinnasu,ana gobe suna aka kawoshi,ragone amma ba babba sosai ba,saidai kuma baza'a ce masa ɗan ƙarami ba.
A zaune nake ranar sunan da safe ina bawa sayyid abincinsa,hankalina gabadaya ya karkata kansa,maganar Shareefah naji tamkar a sama,yaushe ta dawo na faÉ—a a raina,don ita a boarding take makaranta.
"Mashaallah ƙawata da beautiful baby,sauƙata kenan a garin naji wannan labarin."
Murmushi nayi cikeda jin daÉ—in ganinta.
Gaisawa mukayi na yaushe gamo,miƙa mata yaron nayi sai tubarakallah take cewa,ba yabon kai ba kam kowa yaga yaronnawa sai ya faɗa,kyakykyawa dashi gashi ba rama a jikinsa.
Nima kuma lafiyata ƙalau,iya kula muna samu a wajen inna sosai,dan ranar sunan ma lace ta ɗinkamin ja mai kyau.
Lokacin dana ga abubuwan da tayi mana har kuka saida nayi,domin abun ya bani mamaki sosai,abinda inna takeyimin ko mahaifiya ta iyakaci.
Anyi daÉ—i anyi ba daÉ—i dukka a taron sunan,har aka watse kowa yakama gabansa,aka barni dagamu sai halinmu.
Washagari da safe hayaniyar a da ake a cikin gidanne ta tasheni,dan yanzu na dawo É—akin inna kafin nayi arba'in.
Muryar inna ce da kuma gaji suna sa'insa.
Wai gaji ce ta tashi da sassafe ta ɗauko wuƙa zata fara aikin naman suna,ita kuma inna tace bata yadda ba. Duk aikin da akayi a gidan babu wanda ta taya sai wannan.
"Amma dai gaji bakida kunya,tunda muka dawo daga asibiti ƙafata tana ciwo,amma baki tayani da komai ba na aiki sai yanzu,dayake nama ne zaki fito sassafe kifara gyarawa"
"Ohh kura kika maidani komai,kina nufin kice saboda namane shiyasa nazo nake tayaki?"
"Ahh to da ba haka bane,kinyi wani aikinne bayanshi,dan haka ki barshi zamu gyarashi nida Deejah,tunda na da bai kashemu ba na yanzu ma bazai kashemu ba da ikon Allah"
"To shikenan dama ba'ayi muku gwaninta,saikuje kuyi kayanku gayyar tsiya arna a idi,uban É—an ma ya gudu ya barku ai ballantana wani"
Ni dariyama abin ya bani danaji maganganunnasu,narasa meyasa gaji bata jin kunyar yin wani abun.
Gidannamu kenan ko yaushe wasu abubuwan zasu zama tarihi oho,ji nake a jikina kaman wasan yanzu ma aka fara.

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa. *PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka

09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade

Muna maraba daku a kowanne lokaci🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*BOOK 2*
...5...

*Bayan Shekara da watanni*......

"Ke maza kiyi abu da jiki,menene haka kaman bakida laka a jikinki,idan har ya iso baku gama komai ba sainayi mungun saba muku"
Cikeda masifa Mulaifah take magana,gabaÉ—aya duk ta fita daga hayyacinta,bayan wannan tsawon lokacin yaune Ahmad ya yanke shawarar dawowa gidan,dama Abbansune ya damu akan ya zauna jikinsa ya dawo yanda yake.
Kawai dai yana can É—inne,amma plan É—insa gabaÉ—aya babu wanda ya tsayar dashi,komai yana tafiya normal a tsaikaninnasu shiga abokan aikinnasa,wato Eemran da Neelah.
Yanzu ma buƙatar dawowarsa office ce ta taso shiyasa zai dawo gidan.
Hajiyah Maryam wacce ke zaune a falonta ko gezau batayi ba,tunda AM Aliyu yace mata Ahmad zai dawo daga to bata sake tari ba.
Iya Maimuna ce da Saleem kawai suke murna,saikuma murnar Fatee wanda dan taga yanda abin zai ƙare shiyasa takeso ya dawoɗin. Sameer kuwa an turashi can wajen gyembu wani aiki (Zasuyi bincike akan ƙungiyar BB ta bombi dake cikin dajin)😁😁😁.(uhm mutanen littafin BAƘAR AYAH) munayi musu fatan NASARA littafin na Maman Abdoul. Allah ya bar ƙauna...........
Chapter 5 · 0% Book details