← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 48

Sashe 23

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Sumaimah yau ba baccin asuba ne,mai yake damunki naga ko da daddarema duk sanda na farka saina ganki kina juyi"
"Uhm ba komai ummi,ki koma baccinki kawai banajin yin baccinne yau"
Tashi nayi daga kan sallayar har rana ta fara fitowa saboda daɗewa da nayi a zaune. Hijabin na cire na yafa ƙaramin gyale akan rigar jikina na fita.
Gidan tsitt yake babu kowa, sai kukan tsintsaye a lambu.
Leƙawa nayi ruwa yana gangarawa wajen tsirran da suke gurin.. Haka kawai ban sani ba na tsinci kaina dayin murmushi, domin Allah yayini da son Yanayi(nature).
Zama nayi a kan dutsen danake yada zango ko yaushe idan naje wajen. Kasancewar da É—an duhu ma bana ganin wajen sosai.
Jiya kam nayi wani abu waishi tunani,tareda neman mafita na lamarin danake ciki. Wani bangare na zuciyata nason yarda da hajiyah Maryam dakuma abinda nagani,yayinda wani bangaren kuma yana gargaÉ—ina da yardar,duk abubuwan dana gani har yanzu saina cigaba da abinda hankali bazai É—auka ba?.
Tunowa nayi da ashe an kawo kayan abinci a sashen Ahmad,bamma je nagani ba,ga kuma ƙarin aikin sashen hajiyah Mammah da zan dungayi,duk da ma shi ba mai yawa bane. Mariya ce in jisu da faɗa take mata abinci,saboda tafison na gargajiya. Ni gurbin wacce take ɗan tayata da aikace aikace zan maye,sai goge goge.
Tashi nayi daga wajen na nufo sashen sa,ƙofar falon na tura na shiga,nasan dama ba rufewa zayyi ba bayan ya dawo daga masallaci.
Kai tsaye kitchen É—in na nufa,yana cikeda kaya kowanne da gindinsa suka ajiyeshi. Kama kunkumina nayi tareda jijjiga kai, maza dai sai a gaishesu dan ma Allah ya taimakeni na gyara kitchen É—in.
Kayan nafara ciccirewa,kowanne ina sakashi a wajen daya dace dashi,na fridge na sakasu. Har sun fara tsami,musamman kayan marmarin da kuma kaji.
Saida na gama gyara kitchen É—in tass kafin na É—aura girki. Sandwich nayi da kunu gyaÉ—a,saboda naga harda garin kunun suka kawo.
Bashida bata lokaci dan haka da wuri na gama,ina cikin goge goge na inda yaÉ—an baci naji motsin mutum a bayana.
Juyawa nayi da sauri muka haÉ—a ido da Ahmad,vest ce a jikinsa sai 3 quarter,shima zabura yayi daya gannin, domin bayyi zaton nazo ba.
Saurin sauƙe ido nayi da muka haɗa ido,yayinda shima yafara kame kame ya rasa abin cewa.
To mainene ma ni É—in na wani sunkuyar dakai.
Ɗaga idona nayi na kalleshi kafin na gaisheshi a taƙaice,har yanzu kaina a cunkushe yake,aikin ma inatayi duk rabinsa a tunani ya ƙare,har a garin yin kunun saida na zubar bansani ba.
"Meyasa kikazo da sassafennan?"
"Saboda nagama da wuri kafin ka fita aiki,sannan hajiyah Maryam ta ƙaramin wani aikin,inason inna gama wannan na tafi"
To kawai yace da kansa,kafin yaje inda fridge yake sai É—au ruwa,ina gani ya tsaya yayi jimm yana kallon cikin wajen,nasan bazai wuce yanda yaga na cika wajen da abubuwa ba,komai da nasa wajen.
Ɗaukar ruwan yayi zai fita,har yaje bakin ƙofa nayi masa magana.
"Nagama abincin,a falo zan ajiye maka kokuma na shigo dashi É—aki?"
"Ahah ki saka a dining ma ya isa"
Daga haka nacigaba da goge gogena shikuma ya fita.
Jera abincin karyawar nayi a dining kaman yanda yace, daga nan kuma na fara gyara falon.
Fitowa yayi sanye da kayan aikinsa na uniform,dayake kalar yanada duhu,sai yayi masa kyau sosai,dana kalleshi wata faɗuwar gaba ce ta riskeni tareda mararin jina a jikinsa,saidai nasan hakan bazai yiwu ba,koma zai farun banan kusa ba. Dan haka shiyasa na binne komai a ƙasan zuciyata nacigaba da aikina.
"Uhm da kika gama kallonnawa ai ba aikin zaki cigaba ba,saiki zo ki zubamin abincin koh?"
Ajiye mopar nayi na nufi gabansa,dama na gama da falon.
BuÉ—e plate É—in nayi kawai,saboda bamma sakashi a cikin warmer ba.
Fork na saka masa a gabansa,tareda zuba mata kunun a kofi shima na miƙa mar.
Saida naga yaÉ—au fork din zai faraci kafin na tafi. ÆŠakinnasa nashiga,nan ma saida na tattare kayansa komai nasaka shi a muhallinsa kafin na share.
Daga wannan sai wannan nakebin aikin daki daki,dan yanzu inaga ko idona rufene to zan iya yin komai.
Lokacin dana gama na fito daga É—akin ya riga ya fita,dan haka zama nayi naci abincin a wanda ya bari na kai kwanukan kitchen.
Bayan na wankesu nasakawa sashen turaren wuta na fito,saikuma da yamma idan na daidaici yakusa dawowa.
Nafito kenan mukaci karo da hajiyah maryam,shigowarta gidan kenan da alama,amma ba kayan da tafita dashi bane jiya a jikinta kokuma nace aka fita da ita kai.
Wasu kayanne daban masu kwarjini da suka boye faɗawar da fuskarta tayi,saikuma abin hannu shima daya boye ƙofofin tabon carnular da take hannunta a jiyan. Amma fah hakan zai boyune kaɗai ga wanda baisan mai yake faruwa ba,bandani da naga komai.
Gaskiya na jinjinawa ƙarfin halin matar nan,ta tsaya ƙyam akan dogon takalmi cikin izza,kaman ba itace take nishi da ƙyar ba jiya.
Kallo É—aya tayimin ta É—auke kanta,nima banyi niyyar tacemin komai ba ai. Duk da kuwa zuciyata cike take da zumuÉ—in son sani mai yake faruwa,domin ta hakanne kawai zan ga wanne irin taimako zan bawa uban É—annawa.

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

*BOOK 2*
...17...
Chapter 23 · 0% Book details