← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 48

Sashe 18

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na É—aya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

*BOOK 2*
...14...

Jallof É—in taliya nayi da ice fish,saina markaÉ—a ayah nayi kunun ayah mai kauri.
Abinda yasa nayi na kula ko lokacin da yana goje yanason a sarrafa masa taliyah..
Ina yin abincin amma gabaÉ—aya tunanina ya rabu gida biyu,shin zai ci kokuma ahah,idan bai ci ba yazanyi?.
Na sauƙe abincin kenan ina sakawa kunun ayan ƙanƙara naji motsinsa falo..
Leƙowa nayi a hankali kaman munafuka,a zaune yake a akan kujera yana kallon wani labarai a bbc.
Komawa nayi da baya ina kallon kwanukan abincin dana shirya.
Ta maza nayi tareda yin shahada na É—auki tiren nafito zuwa falon.
Har na ajiye akan center table bai kalleni ba,nima kuma ban fasa ba. A flate na zuba masa sai ƙamshi takeyi,dan murmushi nayi ganin yanda ya haɗiyi yawu ta gefen idona.
Tura masa nayi gabansa bayan na saka fork akai,shima kunun ayan na zuba a kofi na miƙa masa.
"Bismillah gashinan na gama,kaci koda kaÉ—anne saboda yanayin da kake ciki,barina tafi idan kagama zanzo na É—auke"
Yajini sarai amma bai kalleni ba sai kace gunki,a raina nace wannan inaga da a gidan sarauta aka haifeshi bazaiyi magana ba ma.
Tashi nayi daga durkushen danake nafita daga sashen.
A bakin ƙofa na haɗu da Saleem zai shigo.
"Ahah Sumaimah ya mutuminnaki ne?"
Ƴar dariya nayi kafin nace.
"Ehh to bazance komai ba,nayi masa abinci dai,amma har na fito bai yimin magana ba"
"Iyee kafin kayan abincin suzo harkin fara girkin,toh nima cikinnawa bai ɗauka ba,barina shiga na tayashi. Am yawwa naje na kaimusu list ɗin abinda kike buƙata,zasu kawo a motar shagonnasu in anjima zuwa yamma"
Jagayeni nayi ya shige ciki hana murza hannu,hakan da yayi sai ya bani dariya. Shikam babu ruwansa kaman ba ɗan gidan ba. Sashenmu na nufa,inyaso in an kawo kayan na dawo. Ina can inata kulada shi ashe ni banci abinci ba tun safe. Cikina sai ƙiran ciroma yakeyi.
Ina shiga akan kwanon abincin na dura babu tsayawa.
"Kina can kina aikin da ba'a sakaki ba,saida kika É—ebo yunwa kafin kikasan da nan koh,nayi zaton ai kinci abincin a can"
Ummi ce tayi maganar tana fitowa daga banÉ—akinmu,fuskarta da ruwa,da alama alwalar la'asar tayi.
"Kinci abinci ne?"
"Meyasa kika tambaya,mai zan jira?"
"Saboda naga ranar dana daÉ—e ban dawo ba bakisan natafi siyayya da umaru driver ba kinyi zaton bata nayi,ko abinci baki ci ba"
"Waye yace miki,ni ban nemeki ba kawai dai banajin yunwa ne,yanzun tun É—azu a ina kike,nasan dai a kin daÉ—e kikai Azahar"
Tana maganar ne bayan ta saka hijabi tana shimfiÉ—a sallaya.
Kallonta nake da mamakin halinta,a yanzu in wani ya ganta zaice tafi kowa tsanata,amma allah ne kaÉ—ai yasan tunani da tayi da bana nan.
Fuskar damuwa na É—ora akan fuskata bayan na rufe kwanon abincin na turashi gefe..
"Hmmm bashida lafiya ne,ni bansani ba saida dr Saleem ya faɗamin ashe ciwon yayi tsanani sosai,matuƙar bazai dunga cin abinci akan kari ba to ciwon zai tashi. Gashi wai bayacin abincin gidannan"
"To miye naki a ciki,ƙaramin yarone da sai an faɗamasa lokacin da zaici abinci saboda kada yayi masa illah? To yanzu da kike faɗamin mai zakiyi akai,sufah masu kuɗinnan duk da suna burgeni to kuma suna bani haushi"
Kallonta nake yanda ta zage tana ta masifah,nayi zaton bataganin laifin masu kuɗi sai talakawa ko ƴan ƙyauye,to ashe ba haka bane,kowama bata barshi ba,duk da cikin zuciyarta ba hakan bane.
"Na yanke shawarar zan dungayimasa girki a sashensa,dan haka bazan dunga dawowa da wuri ba"
"A nawa zaki dunga yimasa kuma"
"Wannan ba zancen kuÉ—i bane,nice na saka kaina bashi yace nayi ba"
"TabÉ—i kyauta kuma,ina kanki ya shiga,ko kema sonsa kike kaman sauran wanda sukayi masa aiki a baya kai?"
"Ahah ba haka bane,bazaki gane bane ummi amma......"
"Kinga bazan gane ba,ba kuma saina gane ɗin ba,dan haka karki takurawa kanki wajen yin bayani,barikiga nayi sallah kar lokaci ya ƙuremin. Ohh yawwa nama manta,in kingama aikin saka kan kada ki manta hajiyah Maryam na nemanki,yau baki gyara mata side ɗin ta ba,bayan kuma kinshiga sa safen"
Dumm gabana ya buga,sai yanzu na tuna abinda ya faru,tabbas na shiga kaman zanyi aiki,amma sainayi bincikena kawai na fito.
Runtse ido nayi tareda jijjiga shi,Allah gani gareka.

Ahmad (POV)
Chapter 18 · 0% Book details