← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 48

Sashe 20

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

"Tambayar ki nake,meyasa yau baki yimin aikiba,kuma ance kin shigo,to me kikayi bayan shigowar?"
Shuru nayi ina kallonta,daga baya na sunkuyar dakai,shin mai zan ce mata ne ma,ni dai ba nace na shigo nayi mata bincike ba. Ohh wayyo Allah nah.
"Uhm Hajiyah nashigo amma kafin na fara aikin sai nace barina fara yiwa Yallabai tukunna,to kuma danaje bashida lafiya saina manta ban dawo ba. Kiyi haƙuri hajiyah"
Tunda na fara maganar kafeni tayi da ido,da alama bata yarda da abinda nake faÉ—a ba sam.
"Yaushe kika zama mahaifiyarsa da idan bashida lafiya bazakiyi wani aikin ba uhm?"
"Uhm kiyi haƙuri hajiyah,dan Allah za'a iya bani iya aikin sashensa kawai,in yaso a ragemin albashina sai a ɗau wata"
Banida zabi daya wuce na faÉ—i hakan,duk da nasan hakan kasada ce,tunda banyi aikin da nazo yi ba,shi ya riga ya koreni banida albashinsa,iyah na hajiyah maryam ne,to ita kuma idan na haÉ—a da aikinta bazan samu damar kulada sashensa ba sosai.
"Meyasa kikace haka? A tunanina iya shara da goge goge kike yimasa,a kaf ma'aikatan gidannan ke kaɗaice mai aiki kaɗan,amma a hakane zaki rasa time na yimin aiki,lokacin da kikazo fuskarki ya nuna buƙatar kuɗin aikin ki muraran,amma yanzu kina cewa kin yarda a rage kuɗin aikinki saboda aiki a bangare ɗaya?.
ÆŠazu ance kin haÉ—u da hajiyah Mammah har tayimiki magana,alamu ya nuna ta yaba da hankalin ki. Koda kin bar yimin aiki to inaso na sakaki a sashenta,zaki dunga yimata goge goge da shara,zan sauya mai aikinta"
Meyasa zata sauya mai aikinta ta sakani,nace banason nayi mata kuma tasake turani wani wajen?.
"Amma hajiyah....?"
"Kince bazaki yimin aiki ba na yarda toh,amma wannan ba wai turasasaki zanyi ba,ahah ina roƙonki ne kiyimin wannan aikin,saboda dake kaɗai na yarda a kaf cikin gidannan. So nake kiyi mata aiki amma ki zama idona da kuma kunnena a sashen. Amma idan kinje karki sake ki nuna nina kawoki kokuma kinada alaqa dani, idan hakan ya fito kina cikin hatsari. Ki kuma yi taka tsantsan da komai,kije inada abinyi yanzu,gobe zaki fara yimata aiki"
Tana gama faɗin hakan ta shige banɗaki,jan numfashi nayi tareda kallon hnayar da tabi ɗin,wannan matar mai take nufi,kota kula nayi mata bincikene shiyasa take ƙoƙarin turani wajen waccar dattijuwar kai.
To amma meyasa naga tarin damuwa a idonta lokacin da take roqona,babu wannan jiji da kan da kuma É—aga kai,tayimin kama da wacce takeso ta kare wani abu nata.
Ƙarar shigowar message nagani a wayata,da bazan duba bama,domin a zatona mtn ne zasuyimin tujarar bashin danaci.
Ba sunan mtn nagani ba,wata number ce babu suna,hakan yasa na tsaya na buÉ—e.
_zama dashi yasa kin fara mantawa da halin da kike ciki da kuma shi,ki kusa dashi amma kiyi taka tsantsan,sannan duk rintsi karki bayyana masa matsayinki a wajensa,yin hakan a yanzu hatsari ne gareki da kuma É—anki_

Zaro ido nayi tareda maimaita saƙon akai akai har bansan adadi ba..
Waye yasan wacece ni,waye yasanni a gidannan bayan inna ladiyo ita kuwa batada waya bare ta turomin saƙo,ba kuma Saleem bane,domin shima bai san wacece ni ba.
Shin na yarda da gargaÉ—in kokuma na watsar,idan da gaskene nima na fara zargin Ahmad yana cikin hatsari a gidannasu,to amma waye yake haddasa komai,ina zargin hajiyah Maryam,amma kuma a raina ina jin kamar ba ita kaÉ—ai bace akwai wata.
Ajiyar numfashi na sake tareda wucewa sashenmu,naso zuwa sashensa a yanzun nayi masa abincin dare,bashshi kawai sai gobe naje.

........
Chapter 20 · 0% Book details