← Book details Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 48

Sashe 7

Sanadin Caca Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade

Muna maraba daku a kowanne lokaci🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*BOOK 2*
...6...

"Sumaimah me kikeyi a waje haka,dan kare yana haushi saika biyeshi kayi,ko kin manta da matsayinki ne"
Kuka na rushe dashi tareda tsugunnawa,dan bansan mai zance mata ba,abin ya tarumin sosai.
Tsayawa tayi da faɗan tana rarrashina,saida nayi mai isata kafin na kula da Sayyid wanda yake hannun Deejah yana kuka. Karbarsa nayi na fara bashi abincinsa,da ni naƙi cin nawa ba kamata shi na hanashi ba.
Sai bayan nagama bashi har yayi bacci kafin na tashi nayi alwala.
"Ya takardar gamawar kin ƙarbo ina?"
Jijjiga kai nayi bansan taya zan fara yimata bayani bama,domin maganar akwai nauyi..
"Inna basu bani ba,sunce wai saina bada dubu hamsin tukunna,wai shine kudin da suke bina bashi"
"Bashi bashi kaman yaya,naga yabiyasu kuÉ—in komai harki gama?"
"Uhm sun sani,kawai yanzu ne suka kawo maganar,ina dawowa kuma na haÉ—u da waÉ—ancan suma"
"Hmmm ƙaddarace in muka jure watarana sai labari,bari komai ya lafa saimu samu abinda zamuyi"
"Inna inason tafiyah babban birni yin aikatau,naji ina kayi dace da gidan masu hannu da shuni ana samun kuÉ—i sosai"
Zaro ido inna tayi tana kallona,da alama tayi mamakin furucina.
"A ina kikaji wannan zancen haka?"
"A makarantar islamiyya ne wata take faÉ—a,wai yanzu hakama wai suna shirin tafiya a satinnan,magana tayimin akan ko zan tura Deejah,tunda yara ake turawa,shine nace mata zan duba nagani"
"To mai yasa kikace ke zakije?"
"Inna bazan iya tura Deejah ba,har yanzu bata mallaki hankalinta ba,ina gudun wani abun ya sameta,sannan bayan hakan nasaka a raina zan sakata tayi karatu kaman yanda yah Musbahu ya sakani. Na yanke shawarar zuwa aikin,idan da rabo goje ya dawo sai ku faÉ—amasa inda nake. Idan na turo kuÉ—in aikin inna ku dunga amfani dashi,harda kudin makarantar deejan"
"Naji abinda kikace Sumaimah,irin wannan kyakykyawar niyya da Allah yabaki Allah yabaki mai yi miki,yasa komai ya wuce sao tarihi,dama akwai wani bayani danace miki zanmiki,ita tunanin yanda zan farashi,amma tunda kinkawo wannan zancen a ranki ta kwana gidan sauƙi.
Nayi aiki a garin abuja tsawon shekara talatin,dan haka babu abinda bansani ba gameda aikin,bama saikin bi waÉ—ancan ba akwai adireshin gidan da zan baki,indai kikace nina turoki to za'a vaki aiki,kuma a biyaki mai tsoka"
DaÉ—i ne yakamani jin furucin innan,duk da zuciyata nasan yimata tambayoyi amma haka nayi shuru.
Tashi tayi ta nufi ƙarƙashin gadonta,da alama wani abun take nema..
Ban ankaraba naji mutum a jikina,ashe Deejah wacce take tsaye tana jin abinda muke faÉ—a.
"Nagode anty Sumaimah da karamcinki gareni,bazan taba manta yanda kowa ya gujeni amma keda yah Musbahu kuka taimakamin,gashi a yanzu kin kasa turani aikatau duk da halin matsi saboda karna halaka,kin zabi kije akaina"
Kallonta nake da mamakin yanda kalaman hankali suke fita daga bakinta,ashedai tana sane da abinda yake faruwa,katseni tayi da maganarta..
"Anty da Sayyid zaki tafi"
"Ahah ba dashi zata tafiba,idan ta tafi dashi bazatayi abinda taje yiba,sannan abin bazai tafi yanda ake so ba"
"Wannan abu kuma inna?"
Na tambaya ta mamaki,ganin yanda take magana kaman an turani wani muhimmin aiki.
"Ohh abu nace? Ina nufin aikin dazaki je yiɗin,anan zaki barshi shima zaifi masa sauƙi"
"Amma ......inna ban yayeshi ba fah"
"To jimin wani zance,É—an da tun bashida wayo kike guduwa makaranta ki barshi,ana mutuwa a bar yaro ma ya rayu ai?"
"Yawwa shikenan anty karki damu ki barmin shi,zan kula dashi tamkar kinanan"
Deejah ta faɗa cikeda farinciki,sauƙe ajiyar zuciya nayi tareda cewa.
"To shikenan khadija na barmiki shi har naje na dawo"
Daga haka ta fita tana murna,ni tausayima ta bani,ganin yanda muke ta faÉ—i tashi,idan na tafi zanyi kewarsu sosai.
Wata takarda naji inna ta miƙomin bayan na tafi duniyar nazari,karba nayi na bude,address na gida a abuja.
"Ga wannan gidan shi zaki nema idan kin isa,inkinje ki samu wata mai aiki inna ladiyo,kice mata nina aikoki,idan kika faÉ—i hakan zata baki aiki"
ÆŠaga mata kai nayi,na rasama mai zance,gabaÉ—aya a rayuwata bana kawo cewar wai zanje neman aikatau wani garin saboda mu samu abinyi.
"Toh inna Inshaallah zanyi hakan,batun kuÉ—in aikin kuma zan dunga turowa Tunga sai ya baku"
"Karma ki tayar da hankalinki,a nan ma zan samu wata sana'ar kota É—an tallene na lokaci kaÉ—an na dungayiwa Deejah,nasan kuma daman ba wai aikinne har a ranki ba,kinasone kiyi nesa da gida saboda abubuwan da suka faru"
Sunkuyar da kaina nayi,gaskiya hadda ma hakan,tunda na rasa mijina gabaÉ—aya zaman garin ma ya isheni,tun mutum yana toshe kunnuwansa da maganganu har suyi masa yawa.
Na haɗa kayana a ƙaramar jaka duk abinda nake buƙata,Deejah nake jira ta ƙiramin mai mashin ya kaini tasha.
Kallon Sayyid nayi wanda yake tsaye da minti a hannunsa,tun shekaranjiya da nasan ba dashi zan tafi ba na daina bashi nono,dama toh ba dogara yayi gabaÉ—aya a kai ba.
Amma duk da haka zuciyata saida tayi zafi da barinnasa na shiga duniya,wanda Allah ne kaÉ—ai yasan ranar dawowa ta.
Jiya naje gidanmu nayi musu sallama,muna zancen da ammi inna rammah tajiyo,dama halinta ne yin lab'e idan ana zance,kafi kaceme har zance ya gama ko'ina cewar talauci da baƙin ciki nima zai korani duniya. Wani lokacin abun ma har mamaki yake bani,shin metasa mutane basa ta kansu saita wani ne?
Ko ma dai menene nidai yau zan barmusu garin.
In cikin hakane naji Deejah ta dawo da gudu.."
"Anty ki fito gashinan na ƙiramiki mai mashin ɗin"
"Ohh har an samu mai mashin É—in?"
Inna tafaÉ—a wacce ta fito daga kewaye da buta a hannunta,tayi alwalar walaha..
"Ehh inna nasamo,saida ya É—anani muka taho tare"
Jakata na ɗauko zan fita daga ɗakin,da sauri Sayyid ya jefar da mintin hannunsa yana ɗagamin hannu alamar zai bini,wani kukane ya taho min ya tsaya a maƙogarona.
Inna tana ganin haka ta É—aukeshi tareda goyonsa,dan ma yau bayyi kukan yayeba da daddare.
Gaba na wuce suna bina a baya zuwa ƙofar gida,har raina banason barinsu,amma kuma nasan zuciyata tana buƙatar zuwa nesa,koba komai hakan zaisa na manta da wasu abubuwan.
Musamman yanzu dana gama karatu banida abinyi.
"Sumaimah Allah ya tsare hanya,ki kulada abubuwan dana faɗamiki jiya da daddare,karki shiga abinda babu ruwanki,amma idan yazamo abu nakine kiyi ƙoƙarin wajen ganin baki takura kanki kin hana kanki ba,ki zama jaruma ta yanda zaki iya tsayawa wanda yke naki. Labarin danace zan baki kiyimin uzuri akai,zakiga abinda zai gigitaki amma kibi komai a sannu. Sannan na miki alƙawarin duk wata tambaya da take ranki ki adana,da zar kin dawo nikuma zan amsa miki su. Idan na faɗamiki yanzu zai iya cutar dake,dan haka ki bi komai a sannu"
Kaina ne ya kulle da maganganun innan,nifa aikatau kawai zanje,shin mai ya haÉ—ani da waÉ—annan zantukan kuma?
"Inna shin meyasa kike min irin waÉ—annan zantukan?"
"Da sannu in kika inda zaki je to zaki gane,kije maza Allah ya tsare ya baki NASARA"
Ɗaga mata kai nayi tareda yiwa Deejah da Sayyid kallon ƙarshe kana na ɗale bayan mashin ɗin.
Ina kallon gaji ta fito daga gidan bayan mashin É—in ya tashi. Nasan ba komai bane banda gulma.
A raina nace kedai kika sani ni yanzu sai sanda kika ganni. Saida ba kama hanyar naji kaman na koma nace na fasa,dan ji nake kaman wani abun zai faru. Amma ya zanyi alƙalami ya riga ya bushe.
Chapter 7 · 0% Book details